Owner/managing Director I M BELLO medicals empire

Call Website Contact the business

Owner/managing Director I M BELLO medicals empire I. M. BELLO MEDICAL AND DISPENSARY SERVICES

MIYE CIWON HAMGUM,KUMA MI YAKE KAWO SHI ,KUMA TA YAYA ZA A KARE KAI Ciwon hangum (mumps) yana faruwa ne saboda kamuwa da...
11/08/2025

MIYE CIWON HAMGUM,
KUMA MI YAKE KAWO SHI ,
KUMA TA YAYA ZA A KARE KAI

Ciwon hangum (mumps) yana faruwa ne saboda kamuwa da wani nau'in ƙwayar cuta mai suna "paramyxovirus" wanda ke haddasa kumburin gland ɗin hangum (salivary glands) a wuyan mutum. Wannan cuta tana yaduwa ta hanyar tari, atishawa, ko ta hanyar saduwa da abin da ya shaɗe ko tsotsa wanda ƙwayar cutar ta ke ciki.

Ga wasu mahimman abubuwan da ke kawo ciwon hangum:

Kamuwa da ƙwayar cutar mumps ta hanyar iska ko abubuwan da s**a yi saduwa da majinyaci.

Rashin samun rigakafi ko kuma rashin cikakken rigakafin mumps.

Yananguwar dangi ko mutane masu kamuwa na kusa.

Ciwon hangum yana bayyana da kumburin gland ɗin hangum na gefe ko biyu, zafin wuyan ƙasa da kunne, zazzabi, ciwon kai, da rashin jin daɗi gaba ɗaya.

Don hana wannan cuta, ana bada shawarar yin rigakafi na MMR (measles, mumps, rubella) wanda yake da tasiri wajen kariya daga ciwon hangum.

Bayan haka, ciwon hangum ba ya k**a jiki gaba ɗaya k**ar wasu cututtuka na ciki ko na hannu, domin hangum na nufin gland din salivary ne ke kumbura saboda wannan ƙwayar cuta musamman.

Hanyoyin kariya daga ciwon hamgum (mumps) sun haɗa da:

Yin rigakafi na MMR (measles, mumps, rubella) wanda shi ne mafi tasiri wajen hana kamuwa da ciwon hamgum.

Gujewa kusantar da wanda ke da cutar hamgum, musamman gujewa musayar tari, atishawa, ko abubuwan sha da tsotsa tare da su.

Kulawa da tsaftar hannu da wuraren da ake taruwa don rage yaduwar ƙwayar cutar.

Ci gaba da kula da lafiyar jiki gaba ɗaya domin ƙara karfin garkuwar jiki.

Rigakafi na MMR yana bada kariya ta dindindin ko kusa da hakan daga ciwon hamgum, saboda haka yin wannan rigakafi ne hanya mafi muhimmanci da kuma inganci na kariya.

Bayan haka, idan akwai alamun ciwon hamgum k**ar kumburin gland a wuyan mutum, zafin wuyan, zazzabi, da sauransu, ya k**ata a nisanta wannan mutum daga wasu don hana yaduwa.

Kari akan haka, kiyaye tsafta da gujewa shan abubuwa daga mugun tsafta da tsaftar muhalli na taimakawa rage yaduwar cutar hamgum, wanda wataƙila ya haifar da cutar.

By I M BELLO MEDICALS MISAU.

02/04/2024

KYANDA KO SHARAFTUWA (MEASLES)

Kyanda ko sharaftuwa ciwo ne mai matukar saurin rabo da hatsari na gaske Wanda kwayan cutan virus yake janyota .

A kididdiga da hukumar lafiya ta duniya ta gudanar ya numa mutum dubu dari da arba'in ne s**a mutu a 2018 a duniya sak**akon kamuwa da Kyanda, kuma kamuwar da mutuwar yafi shafan kananan yara yan kasa da shekara biyar .

MANYA DA YARA SUNAYIN KYANDA

Hatsarin Sharaftuwa yafi tsanani ga yara yan kasa da shekara biyar (5) da manya yan sama da shekara talatin (30).

MUNANAN HATSARIN SUNE;

***Tana makantar da mutum

***Tana kowa ciwon kumburin Kwakwalwa

*** Tana kurmantar da mutum

*** Tanasa matsanancin gudawa mai tsotse ruwan jiki cikin gaggawa

*** Tana haddasa ciwon kofofin iska,tare dasa ciwon sanyi k**ar irinsu pneumonia
*** Uwa uba tana kisa idan ba a yi maganinta da gaggawa ba .

ALAMOMIN KYANDA

** Zazzabi: bayan cutan ta shiga jikin mutum da kwana 10 ko 12 zai fara zazzabi

Zai yi fama da zazzabin har na tsawon kwana 4 zuwa 7

*** Daga bisani sai Hanci ya fara yoyo, sai tari ,idanu zasuyi ja suna zub da ruwa

*** Kuraje kanana farare s**an feso a cikin baki, kurajen daga bisani sai su feso a Fiska da Haba

*** Daga nan bayan kwana 3 sai kurajen su baiyana a ko ina a jikin mutum

*** Kurajen bazasu fara warkewa ba sai sunyi kwana 5 zuwa 6

A KULA: Duk Wanda kurajen s**a feso masa to yayi kwana 7 ko 14 zuwa 18 da Haduwa da kwayar cutan KYANDA (Virus).
HANYOYIN KAMUWA DA KYANDA

Kyanda yana daya daga cikin mayan cututtuka a Duniya da ake kamuwa dashi ta ISKA ( AIRBORNE DISEASE), komar Corona

Ga hanyoyin kamuwar;

* Idan mai shi yayi tari ko atishawa iska yana rabawa mutane cutan

* Mannuwa da jikin mai Kyanda ko taba wani abun da jikin mai kyanda ya taba ,yanasa a kamu da shi.

* Yin karo ko taba YAWU, MAJINA , KAKI, AMAI ,ko RUWAN da yake fitowa a idanun mai kyanda yana sa a kamu da kyanda .

* Rashin wanke hanu kafin cin abinci ka iya kawo ciwon kyanda .

Jumma'a Mubarak
01/12/2023

Jumma'a Mubarak

27/11/2023

Sanarwa mai muhimmanci..

Bawai zanyi wannan bayanin bane domin na ragewa masu kasuwancin Zoɓo da kunin aya customers bane sai dai kawai saboda yak**ata musani sai mu ɗauki matakan kariya gabaɗayan mu..

Jama'a kuguji shan duk wani abin sha da za'a zubashi a cikin Empty robar ruwan da yaƙare ko lemon da yaƙare.

Misali: Robar faro ko Fanta ko Pepsi ko CocaCola ko maltina daidai sauransu, Akasarin robobin ana samosu ne daga asibitoci, wasu kuma an zubar a shara, wasu me ciwon Hanta yasa bakinsa, wasu kuma mai tarin T.B yasa baki, haka zalika robobin mararsa lafiya kanyi amai ko tara yawun bakinsu aciki, a haka kuma masu shara zasu tsinta s**ai su sayarwa da jama'a.

A bincike da akayi shan zobo da kunun aya da ake zubawa a "Disposed Bottles" yaƙara yawan jama'ar dake fama da ciwon Hanta a wannan nahiya tamu..

Shawara: duk wasu masuyin wannan kasuwanci na Zobo da kunun aya, dan Allah ku daure idan ankawo maku waɗannan robobin ko daga ina aka kawosu, nasan kuna wankesu amma da ruwan sanyi, to bahaka yak**ata kuyi ba, ruwan zafi yak**ata kudinga wankesu dashi, koda basu zafi sosai ba, idan har zasu iya kashe cutar dake ciki hakan ya wadatar.. Domin ruwan zafi yana taimakawa wajen kashe cututtuka..

Allah yataimaka.. 🙏

29/08/2023

.

Address

Bauchi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Owner/managing Director I M BELLO medicals empire posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Owner/managing Director I M BELLO medicals empire:

Shortcuts

Share