22/05/2022
A yau 22/05/2022 wannan kungiya mai albarka ta gudanarda taro na jaha da shugabanni da kuma membobin kungiyar karkashin jagorancin shugaban kungiyar na jihar Gombe Comr kabiru sale abban ansar.
Yayinda aka sanarda wasu dokoki guda uku da majalisar zartaswar kungiyar ta cimma wadanda s**a hada da
1. Sanarda committee na duban tsafta da zai ke zagawa rumfunan masu shayi Don tabbatarda cewa kowane mai shayi yana samarda ingataccen shayi wa jama'a
2. an samarda committee da zai ke zagawa rumfunan masu shayi Don karban haraji duk Sati naira 100 domin aiwatarda ayyukan kungiya k**ar yadda muka sani babu wata kungiya da zata tafi ba tare da kudin shiga ba.
3. an samarda jamai'an tsaron kungiya wadanda zasu kula da harkokin tsaro na masu shayi a fadin jihar Gombe
Daga karshe an mika takardun k**a aiki ga sababbin shuwagabanni na kungiyar