07/08/2022
IN ZAKA FADI FADI GASKIYA KO TAKA JAMA KA TA BIYA:-
Ni a fahinta ta, fadin gaskiya daban cin-zarafi daban.
Dan na fadi(rubuta) gaskiya akan cewa wane ya aikata wani abu ko bai aikata wani abu ba nikam ban taba daukar wannan cin-zarafin shi ba.
Saboda sau da yawa za ka ga mutum yasan tabbas abin da aka rubuta ko aka fadi gaskiya ne amma saboda kawai akan shi abin ya fada sai kaji shi ko magoya bayan shi su famar yada cewa an ci zarafin shi saboda rashin son gaskiya.
To nikam!! ka sani indai fadin gaskiya shine cin zarafi to da yaddar Allah ba zamu bari ba.
zamu cigaba da fadin gaskiya koda kuwa akan wa zata fada.
In kaji zafi ka gyara halin ka, ka gani zamu yabe ka ko kuma a'a.
MUSA YUSUF TUNGA JEGA