haitex_investment

haitex_investment Haitex Investment are dealers and retailers of the varieties of textiles, such as laces, materials,

01/10/2023

Ranar 'Yancin Kai

Rana ta 'Yancin Kanta yau ta zago
Murna suke yau har da ɗaura agogo

Ban ce a dena hakan ba, ko kwa a fasa
Ga tambayoyi nan a kawo amsa

Yau shekaru sittin ku ƙara ukun kai-
Mulkin, ina wani ci gaban da ake kai?

Fannin kwarafshin kun ga yai tsamari
Daga jami'ai, 'yan ƙwadago da samari

Matsalar tsaro ku fito ku ba ni bayani
Yaushe kuke sa ran ta sauya makani?

Ku taɓo ruwan shan nan abokin aiki
Kullun ana ta saye da 'ya'yan banki

Ba a batun NEPA, su gyara sun ƙi
Yau in akwai gobenmu ba lantarki

Har lafiyar nan wadda taz zama jari
Sai mai kuɗi ne ke ganin ta da sauri

Da uwa-uba ilimi, a wannan ƙarni
Duk ya fi ƙarfin 'yan ƙasa wayyo ni!

Babban misalin nan ku duba su ASUU
Duk malamanmu na Jami'a an kar su!

Har ɗaliban ma kar ka so kallonsu
An sa su duk a cikin halin ni-'yasu

Fanni na kimiyyarmu har da fasaha
Wani in ya hango sai ya yi mana "Haha"

Tsada ta kaya walla sai kai kuka
Kullun farashi sai ka ce hankaka

'Yan kasuwa an takure su ku duba
Da ma'aikata 'yan ƙanƙana har babba

Aiki na yi neman sa ya zama aibu
Har ma da kansu suke faɗa wai "babu!"

Yau dai abinci fa ya zamo ɗan Sarki
Yunwa tana tashe kuna kan mulki

Duk ci gaban da akai irin na su gayen
Nan ne da ke haƙa rijiya yen-yen-yen

Zan ɗan taƙaita kar na buɗe aiki
Amma ku yo nazarin salonsu na mulki

Ni ne Hassan ɗan Abdu nai muku waƙa
Ko Mai Bulawus, tsokacinmu na miƙa.

© Hassan Abdu Mai Blouse
[email protected]
08066303359
01 Oktoba, 2023

26/06/2023
Kampala New Arrival
28/09/2022

Kampala New Arrival

New arrival, available in colours
29/08/2022

New arrival, available in colours

28/08/2022

I've found it worth sharing. Copied

YADDA AKE TOSHE (BLOCKING) NA HARAMTATTUN WEBSITE NA BATSA A WAYA

Idan baku manta ba, na sanar muku cewa, zan Koya Muku Hanyar Magance Wannan Matsala Ta Yadda Wayar Ku Bazata Taɓa Bude Shafukan Batsa Ba Na Internet.

Lallai yana da kyau mu haɗu mu yaƙi kallace-kallacen Fina-Finan Batsa a tsakanin mu, domin Allah subhanahu wata'ala ya haramta, kuma yin hakan na jazawa ƙasa fitina da bala'i.

A addinance dai kowa yasan kallon video na batsa haramunne, haka kuma kallonsu yana cutar da lafiyar idanu da kuma gurɓata zuciya tare da saka raunin imani da tsoron Allah a zukatan al'umma.

Muna cikin wani zamani wanda yahudawa suke amfani da cigaban da aka samu na amfani da yanar gizo suna gurɓata mana tarbiyar ƙanne da yara dama mu kanmu ɗin baki ɗaya, ta hanyar buɗe website masu ɗauke da bidiyoyi na batsa wanda mu addininmu ya haramta mana kallansu, su kuma suna samun maƙudan ƙuɗaɗe ta haka.

Ba'a iya maza kallon bidiyoyin batsa ya tsaya ba, harda mata kuma hakan yana 'daya daga cikin abubuwan da suke bada gudunmuwa sosai wajen lalata mana tarbiya. Wa'iya-zubillah, Allah ka ƙara tsare mu, Amin.

Ni Salisu Magaji Fandalla'fih, Zan faɗa muku hanyar da za ku bi domin ku toshe hanyar da dan uwan ka, ko yar uwar ka, da wayar ka, shiga shafukan finafinan da basu dace ba ta kafar Internet.

Shin Kana da ƙani ko ƙanwa da ke hawa kafafen Sada Zumunta, ?

Kuma kana tsoron kada su rinƙa zuwa shafukan Batsa na kafar Internet suna kallon Fina-Finan Banza ba tare da kai ka sani ba, ga hanyar da zaka hana su ko hana wayar ka shiga waɗancan lalatattun shafukan.

Hanyar da zaka iya bi domin haramta ma wayarka ko wayar ƙaninka kota ƙanwarka, kota yaranka samun damar kamo wa'dannan website ɗin shine.

1. Da farko zaka shiga cikin (Settings) na wayar ka.

2. A cikin settings ɗin akwai wajan Searching (Bincike) a sama saika shiga.

3. Idan ka shiga saika rubuta wannan kalma (Private DNS) Zaka ga ya fito a ƙasa saika shiga.

4. Idan ka shiga zai nuna maka wasu rubutu guda uku a jere
Na farko an rubuta

✅ Off

🔘 Automatic

🔘 Private DNS provider hostname

Idan kaga haka saika cire waccan alamar ✅ dake kan Off saika kamayar dashi kan, ma'ana ka danna kan wannan kalma 👇

✅ Private DNS provider hostname

Saika duba ƙasa waje mai alamar wajan rubutu, a wajan zaka ga an rubuta, enter hostname of DNS provider

4. Saika shiga wajan ka rubuta wannan kalamar kamar haka 👉 adult-filter-dns.cleanbrowsing.org👈

Idan ka rubuta haka a ciki, saika duba ƙasa zaka ga an rubuta
👇
SAVE

Ka danna wajan kana dannawa insha Allahu ka rigada ka gama rufe, duk wani website dake sanya Videon Batsa a internet, insha Ko kaje kayi searching ka shiga zaka ga bazai buɗe ba.

Kuma koda a Facebook ka rubuta kalmar da take nufi da batsa a harshen turanci, to saidai kaga Facebook ɗin ka sunce ka koma baya.

Sannan ina bamu shawara wannan saitin mu saita shi a wayar duk wanda muka san wayar sa zata iya zuwa hannun mu, hakan ba laifi bane illa ma ka taimaki wanda kaiwa hakan.

Dan Allah ku tayamu da sharing, domin duk wanda ya sanar da wani shima yana da lada.

Zamu kulle wayoyin mu daga buɗe Fina-Finan Batsa a kafar Internet, kuma zamu kulle wa ƙannen mu, da duk wanda wayar sa tazo hannun mu, ba tare da ya sani ba, domin tsira daga azabar uban giji.

Allah ya ƙara tsaremu damu da ƴan uwan mu, tare da dukkanin musulmi daga faɗawa tarkon sheɗan da she'danun mutane, Allah ka tsare mana imaninmu aduk inda muke, ka nesanta mu daga aikata dukkan wani aiki wanda baka so. Amin.

Daga Salisu Magaji Fandalla'fih
27-08-2022

New Arrival Laces
28/08/2022

New Arrival Laces

New Arrival  contact 09040964323
16/08/2022

New Arrival contact 09040964323

New swiss cotton materials 2+2=4yrds Double Length XLAvailable at 3500 Naira
15/08/2022

New swiss cotton materials
2+2=4yrds Double Length XL
Available at 3500 Naira

Luxury Lapaya Available
23/06/2022

Luxury Lapaya Available

Cotton Voile Materials. Available!
23/06/2022

Cotton Voile Materials. Available!

Address

No. 30 Makwarari House, Upstair, Kwari Market Kano
Kano
700213

Telephone

+2348066303359

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when haitex_investment posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to haitex_investment:

Shortcuts

Share