27/07/2026
'NI DA KANNENA' CHAPTER TWELVE
GARGADI❗️❗️❗️
Labarin 'NI DA KANNENA' taska ce daga fasahar Khadija Aliyu Ibrahim. Kuma kyauta ne.
Satar rubutu ba nishadi ba ne, cin amana ne ga marubuciya da kuma kokarin toshe hasken hazakarta.
Idan ka ga wannan rubutu ba tare da sunana ko link ba, ka sani ba daga gare ni yake ba.
Sannan duk wanda muka k**a da wannan laifin zai fuskanci fushin hukuma.
Saboda haka a kiyaye.
"BISMILLAHIRRAHMÁNIRRAHEEM!"
"WASSALÁTU WASSALÁMU ALÁ RASULULLÀHI (SALALLÀHU ALAIHI WA SALLAM.)"
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
KU DIN GA YI MANA COMMENTS, LIKING IN DA HALI KUYI SHARING ZUWA WASU GROUP ƊIN SHINE ZAI BAMU ƘWARIN GWIWAR KAWO MUKU LABARAI KYAUTA.
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Rayuwa tayi min ƙunci, bana iya bacci, babu walwala, duk na rame na lalace, su Ameerah sun ɗauka iya damuwar kudin karatun Anuwar ce, amma basu sani ba gwara waccan damuwar sau dubu.
Nayi tunanin duk wata hanya da kuɗin nan s**a ɓata na rasa, na rasa yadda zanyi, nayi iya tunanin inda zan samu kuɗinnan amma na rasa.
Lokacin da aka ɗibarwa su Anuwar ya ƙarato, saura ƴan kwanaki, ganin babu wani motsi da nayi ya saka Anuwar ya kwantar da hankalin sa sannan nima ya shiga kwantar min da nawa musamman da Ameerah ta sanar dashi halin da na shiga.
Ina cikin wannan yanayin Daddy ya dawo daga tafiyar da yayi, hakan ya saka na yanke shawarar sanar dashi halin da nake ciki koma wanne hukunci ya k**a a yanke min saboda na gaji da fargaba.
Kwanan sa biyu da dawowa, wata lahadi da yamma ya kirani a waya yace yana son ganina, na tabbata zancen kuɗin da ya ɓata ne hakan ya saka na ɗebi duk wasu evidences da zan iya kare kai na na nufi guest house ɗin sa bayan ya turomin da address.
Isa ta ke da wuya da mamakina ban ga Al'ameen ba sai wani Babban mutum wanda zasu yi shekaru ɗaya da Daddy, abin ya bani mamaki saboda iya sani na duk wata harkar company akwai Al'ameen aciki.
Haka na ƙarasa na durƙusa na gaishe su, bayan sun amsa Daddy ya kalle ni cike da barkwanci yace:
"Nuratu sarkin aiki, to daga cewa kizo kuma sai ki ɗakko laptop da takardu haka?"
Murmushi yaƙe nayi saboda ban fahimci mai yake nufi ba.
Ya sake kallona fuskar sa babu alamar wasa yace:
"Yau ba ranar aiki bace, ba abinda ya shafi aiki zamu tattauna ba, abu ne da ya shafi rayuwar ki kuma wanda zai canja rayuwar ki har abada."
Wani irin faɗuwar gaba naji, zuciyata ta gaza fahimtar me yake shirin faɗa, haka nayi ta maza nace:
"Ranka ya dade ban fahimci me kake nufi ba?"
Yayi murmushi ƙasaita, sannan yace:
"Ai bazaki taɓa fahimta ba idan ba bayani nayi miki ba."
Ya miƙo min wata wayar Tab mai faɗi sosai, na saka hannu biyu na karɓa.
Hoton ASHRAF ne ya bayyana ajiki cikin shigar manyan kaya na cikakken Bahaushe, fuskar sa ɗauke da murmushi mai ƙayatarwa wanda ya fito da ainahin cikar sa da k**alar sa da kuma kwarjinin sa.
Ɗagowa nayi na kalli Daddy fuskata cike da tambayoyi, duk da ban furta ba amma duk wanda ya kalli yanayin fuskata yasan ina buƙatar ayi min bayani dalla dalla.
"Ki ƙare masa kallo sosai Nuratu, shine ɗa na guda tilo da na mallaka a duniya, bani da wani abu da nakeso kuma nake jin sa fiye da yadda nake jin kaina a duniya sama dashi, akan sa nake so muyi magana."
Sake ƙarewa hoton kallo nayi na tsanaki, zuciyata cike da miliyoyin tambayoyi wanda suke buƙatar amsa.
Ɗago kai na nayi daga kallon hoton tare da ɗora Tab din akan table ɗin da yake gabana naɗan turata kaɗan da gefen yatsuna, na ɗora hannun a ƙasan haɓata ina faɗaɗa tunanina.
Murmushi Daddy yayi sannan ya kalle ni yace:
"Nuratu!"
Cikin sanyayyiyar murya ya ambata, hakan ya saka na ɗago muka haɗa ido dashi fuskata sam babu alamar wasa sannan na amsa da"Na'am." Acikin murya mara amon sauti.
"Ina so ki buɗe kunnuwan ki da kyau ki saurari maganar da zan faɗa miki, deal nakeso mu shirya da ke na kasuwanci, kin sani cewa ni ɗan kasuwa ne bana tsoron kowanne irin kasuwanci matuƙar bai saɓa ka'ida ba, shi kuma wannan business ɗin da zamuyi ina mai tabbatar miki da zai sauya goben ki, zaki kafa kanki har da ma ƴaƴan ki, sannan zaki tsaya da kafar ki, amma sai kin amince, sannan idan kika ga bazaki iya ba bazanyi miki dole ba amma bana bukatar ki fitar da sirri na waje, dafatan kin fahimce ni?"
Jinjina kai na nayi ba tare da na kalli inda yake ba saboda na ƙagu naji wacce irin hulɗa zamu ƙulla.
Ya sake gyara zamansa sannan ya kalleni ya fara bayani:
"Kamar yadda na faɗa miki Ashraf shi kadai ne ɗa na a duniya, na raine shi na bashi cikakkiyar tarbiyya daidai gwargwado sannan na bashi ilimi na addini da na boko, na bashi gata da soyayya, babbar matsalata dashi shine mahaifiyar sa tana nuna masa so na cutarwa hakan ya saka yake yin duk abin da ya ga dama, tana fakewa da larurar ciwon zuciyar da yake dashi tun yana yaro shiyasa sam batayi masa faɗa batason ayi masa."
Ya sake numfasawa sannan yaci gaba da magana:
"Nayi iya bakin ƙoƙari na akan sa domin ya zama mutumin kwarai amma abun yaƙi, ko ba don komai ba ko don ya kula da wannan tarin dukiyar da na tara masa amma abu yaci tura, in taƙaita miki zance Ashraf babu wani nau'in kayan maye da baya ta'ammali dashi, ina faɗa miki wannan ne saboda ki fahimci abin da zan faɗa kuma kiji da kunnen basira."
"Ta sanadiyyar shaye shayen da yakeyi da mu'amala da abokan banza ya saka yau kusan wata shida daya gabata s**a samu matsala akan mace s**a taru s**a yi poisoning ɗin sa acikin lemo wanda yanzu haka zancen da nake miki yana London unconscious acikin 'Comma'."
"Innalillahi wa'inna ilahi raji'un" na furta a zahiri saboda ya tunamin da halin da Alhaji ya shiga lokacin da yaci guba, sannan ga tsananin tausayin da Daddy ya jefa ni aciki saboda yanayin yadda yake magana zai bawa duk wani mai imani tausayi.
Haka Daddy ya daure yacigaba da bayanin sa:
"Babbar matsalar da tafi damuna itace; duk da likitoci sun bani tabbaci akan farfaɗowar sa zuwa nan da kowanne lokaci, amma fa abinda bincike ya nuna shine sanadiyyar wannan gubar da yasha a hankali tana lalata masa ƙwaiƙwayen haihuwar sa, idan ba'a ɗauki matakin ba Ashraf ba zai taɓa haihuwa ba har abada..."
Ɗagowa nayi cike da razani na kalli Daddy da kuka ya ƙwace masa, take naji hawaye ya fara gangaromin, tabbas dukiya aikin banza ce, gashi yana kuka akan abinda kuɗi bazasu yi masa ba, kuma ace mutum k**ar wannan yana kuka ai akwai tashin hankali da tausayawa.
Wannan abokin nasa da suke tare ne ya hau rarrashin sa, sannan Daddy ya kalle shi yace:
"Kaci gaba da yi mata bayani Doctor."
Gyaran murya shima yayi sannan ya kalleni yace:
"Sunana Dr Sabo Lawan, ni ƙwararren likitane a ɓangaren sassa daban daban na jikin ɗan Adam, to babban abinda yake faruwa da Ashraf shine; Daman yana da gado na matsalar 'Low S***m Count' ma'ana ƙarancin ƙwaiƙwayen haihuwa daya gada a wajen mahaifinsa, sannan kuma ga wannan muguwar guba nau'in 'Organochlorine Compound' da yasha acikin lemo mai ɗauke da kwayoyin maye aciki ita ta taimaka wajen fara kashe ƙwaiƙwayen haihuwar sa, wadda daman aikin ta kisa ne direct, idan kuma Allah ya ceci mutum ya rayu, to zata illata masa ƙwaiƙwayen haihuwar sa, sannan ga bugawa da zuciyar sa tayi saboda tsorata da yayi, to a wannan yanayin Ashraf yake kai a yanzu wanda ko da ya samu mu'amala da mace bazata iya samun ciki ba sai ta hanya guda ɗaya itama idan bamu gaggauta ba to zamu iya rasa ta saboda a kullum Ashraf yana rasa miliyoyin ƙwaiƙwayen haihuwar sa ta sanadiyar wannan guba."
Dr Sabo ya numfasa sannan ya kalleni yace:
"Hanyar guda ɗaya itace; IUI (Intrauterine Insemination), da Hausa shine; DASHEN CIKI.
Za'a ciri abinda ya rage na ƙwan haihuwar sa a dasa acikin mahaifar mace, idan ciki ya bayyana, zata zama ƙarƙashin kulawar likitoci har zuwa lokacin haihuwa yayi ta haife shi lafiya da izinin Ubangiji, wannan shine kaɗai ne solution na matsalar Ashraf."
"Nuratu muna so ki ɗaukar mana cikin ɗan Ashraf ki haife shi acikin sirri ba tare da kowa ya sani ba, mu kuma zamu baki dukkan abinda k**e buƙata a duniya wanda zai sauya rayuwar ki gabaɗaya".
Ya ƙarasa maganar acikin wani salo na ƙoƙarin jan hankalina.
Wani mugun kallo nabi su dashi, haba jama'a sai kace a Film haka kawai ina zaman lafiya ta ban taɓa mu'amala da namiji ba haka kawai a ɗauki ɗan mutum a dasa min aciki na na haife shi su karɓi abin su saboda ni nafi kowa son kuɗi, duk talauci na bazan yi wannan abun ba ba daji ba.
Daddy ne ya kalle ni, yanayin da ya ga fuskata yasan tabbas bazan taɓa amincewa ba, sannan yayi murmushin ƙarfinhali yace:
"Nuratu zan baki Naira miliyan ɗari biyar akan wannan abun, zan baki gida zan baki mota zan baki wasu daga cikin kadarori na idan kin amince a yanzu zamu baki rabin kuɗin cash in dollars, fatana kawai ki amince ayi wannan aikin dake, saboda kema inaso ki ƙaru ki fita daga talauci na har abada."
Juyowa nayi na ƙare masa kallo, take naji wani tausayin sa ya k**a ni, amma babban abinda nasani shine bazan iya wannan kasadar ba sam na haihu babu aure ai bazan taɓa ɓata record ɗi na ba akan kuɗi duk yawan su na gwammace nayi prison wallahi.
Shurun da nayi yayi matuƙar ɗagawa Daddy da Dr. hankali, sai dana numfasa sannan nace:
"Kayi haƙuri ranka ya daɗe bazan iya ba, bana son abinda zai taɓa mutunci na, bazai taɓa yiwuwa na haihu babu aure ba..."
"Nima bance zaki haifa min jika babu aure ba Nuratu..."
Ɗagowa nayi na kalleshi cike da mamakin yadda yayi magana cikin ɓacin rai, hakan ya saka na sunkuyar da kaina naci gaba da sauraron sa.
"Bazanyi alfahari da jikan da aka haifamin babu aure bah, Nuratu idan kin amince sai an fara ɗaura auren ki da Ashraf sannan za'a yi wannan aikin, sai dana tuntuɓi malamai s**a bani fatawa sannan na fara yunkurin aiwatarwa, idan kinga zaki iya Bismillah, idan kuma bazaki iya ba zan nemi wata, na baki nan da kwana uku kiyi shawara."
Ya ƙarasa maganar tare da miƙewa yabar wajen cike da ɓacin rai.
Dr. Sabo shima miƙewa yayi sannan ya kalleni yace:
"Karki bari wannan damar ta ƙwace miki Nuratu na tabbata ba zaki taɓa samun k**ar ta ba anan gaba."
Shima ya wuce ya bar ni a zaune k**ar an dasa bishiya.
Haka na ɗebi jikina babu ƙwari na nufi gida, ban zame ko'ina ba sai bedroom ɗin mu na kifa kaina akan pillow na fara rabzar kuka mai tsuma zuciya.
Na rasa kukan me nake yi, tun da al'amuran nan suke faruwa banyi kuka ba sai yau, haka nayi tayi har nayi mai isata sannan na miƙe nayi alwala nayi sallar la'asar na kai kuka na gurin mai duka.
Haka nayi wunin ranar babu daɗi, daƙyar na iya cin abinci, na nemi makwanci da wuri na kwanta saboda nasan gobe akwai aiki, amma ina ranar bacci sai ɓarawo.
Washegari haka na tashi jikina babu ƙwari, a daddafe na shirya na fita office, a hanya ina tafe naji gabana yana ta faɗuwa, naji k**ar na koma gida amma haka na daure na ƙarasa baki na cike da ambaton Ubangiji.
Bayan na isa office na iske saƙon Managing Director akan yana son gani na, ko zama banyi ba na nufi office ɗin sa.
Duk yadda na kai da ɓoye kuɗaɗen da s**a ɓata sai da asirina ya tonu, nayi iya bakin ƙokarina akan na kare kaina amma abun yaci tura saboda Cyber Security Company abinda ta nuna shine an fitar da kuɗin babu izini.
Hankali na yayi matuƙar tashi, take naji jiri yana ɗiba na, ƙarshen maganata da Manager itace:
"Ki daure ki nemo kuɗin Company saboda nan da ƴan kwanaki zasu iya zama alerted zasu fahimci komai kuma hukuncin kora ce tun da kudin suna da yawa, bazai yiwu adinga cira a albashin ki ba, idan kuma baki fito dasu ba magana ta gaskiya sai dai ku ƙare dasu a kotu."
"inshaAllahu zanyi iya ƙokarina."
Na furta tare da ficewa daga office ɗin.
Haka na dawo office ɗina a daddafe na nemi kan carpet na kwanta tare da kulle ƙofar office ɗin, tunanin duniya ne ya ishe ni naji gaba ɗaya, na gaji da rayuwar nan, na fara tambayar kaina "shin yaushe al'amurrana zasu daidaita?"
Haka na yini a ranar babu abin da na aikata na da lokacin tashi yayi na nufi gida na nemi kan gado na kwanta take naji zazzaɓi mai zafi ya rufe ni.
Can cikin bacci na mafarkin Baffana nayi, yanayin da na ganshi naji dadi acikin ni'ima amma fa fuskar sa a ɗaure babu alamar dariya yana ta karatun Alkur'ani k**ar yadda ya saba, na matsa kusa dashi ina yi masa magana bai saurareni ba, a ƙarshe dai ya miƙe yaci gaba da tafiya hannunsa riƙe da wani yaro ƙarami da ban ga fuskar sa ba.
Firgit! Na farka tare da yin salati, na jiƙe sharkaf da gumi alamar zazzaɓin ya sauka, na zauna nayi jugum ina nazarin mafarkin da nayi, zuciyata tana raya min wani abu daban.
Ameerah ce ta katse min tunanina ta shigo hannun ta riƙe da kwanukan abinci ta ajiye min tayi min sannu sannan ta fita saboda ta shigo ta ganni ina rawar zazzaɓi.
Haka na lallaba naci abincin nayi wanka na fara shirin kwanciya saboda period yazo min babu damar yin sallah.
Har na fara bacci tunanin Anuwar ya faɗo min, nayi sauri na ɗakko wayata na hau WhatsApp na iske saƙon sa k**ar haka:
"Ukhty na fara haɗa kaya na jibi zan taho inshaAllahu."
Wata mummunar faɗuwar gaba naji, banaso Anuwar ya dawo Allah ya sani ina so ya samu ingantaccen ilimi ko za'a samu ya nutsu, yanzu idan ya dawo ya zanyi da ɗawainiyar su da Allah ya ɗoramin, nan fa tunanin dukiyar da muka binne da Baffana ta faɗomin, nayi zumbur na miƙe na fara tunanin ko na koma garinmu ayi duk wadda za'a yi mu ɗauki hakkin mu na turawa da Anuwar yaci gaba da karatun sa.
Wata zuciyar tace min: "Shin kina da tabbas akan dukiyar tana nan? halakar zaki koma? Nuratu har yanzu bakiyi ƙarfin da zaki tunkari garin ku ba, to ma dame k**e taƙama?"
Komawa nayi na zauna a gefen gado jagwaf jikina babu ƙwari, na fara maimaitawa a raina "Har yanzu banyi ƙarfin da zan tunkari garin mu ba?"
To sai yaushe zanyi ƙarfi?
Na furta a zahiri.
Tunanina Naira miliyan ɗari biyar ne ya fara karakaina a cikin ƙwaƙwalwata, na tabbatar da zasu yanke min talauci na har abada, zan fita daga duk wata chakwakiya sannan zan tsaya da ƙafata kuma zanyi ƙarfin da zan iya karawa da koma waye.
Miƙewa tsaye nayi na fara zarya a ɗakin zuciya ta tana hasasomi yadda waɗan nan kuɗin zasu sauya gobena, sannan ba fa haramci zan aikata ba, abune za'a yishi a sirrince, idan abun nan ya tabbata zan samu Anuwar yayi karatunsa k**ar kowa, na cigaba da daukar ɗawainiyar ƴan uwana da Allah ya doramin sannan na biya bashin Company saboda idan aka kore ni a wannan yanayin bansan ya zanyi da raina ba.
Haka ya saka nayi gaggawar ɗakko wayata na turawa da Daddy text message k**ar haka:
"Na amince, amma ina bukatar kudin gobe da sassafe."
Banyi tunanin ƙalubalen da yin hakan yake ƙunshe dashi ba na tura masa da wannan text ɗin.
Cikin kankanin lokaci Daddy yayi min reply:
"Kinyi dabara, maganar kuɗi kuma sai kinyi signing saboda akwai sharuɗɗa da ka'idoji, zan turo miki da address ɗin inda zaki same ni zuwa da safe idan Allah ya kaimu."
Banyi tunanin komai ba na kwanta zuciyata a cunkushe na gaza fahimtar murna zanyi kokuma baƙin ciki.
Washegari ina farkawa naga address ɗin ya shigo wayata, cikin sauri na shirya a gaggauce na fita.
A hankali na isa wani guest house ɗin Daddy na daban, bayan na karewa wajen kallo nace a raina "masu kudin sun huta."
Haka na shiga na iske Daddy da Dr Sabo sai wasu manyan mutane guda uku, biyu daga ciki da alama malamai ne, haka na durƙusa na gaishe su cikin girmamawa sannan na nemi waje na zauna.
Daddy ne ya kalle ni fuskar sa babu yabo babu fallasa yace:
"Nuratu ai lokacin da aka ɗiba kiyi shawara bai cika ba, shin kina ganin hakan babu matsala?"
"Babu matsala inshaAllahu, uzuri ne ya saka nayi hakan."
Na faɗa a takaice.
"Babu laifi ma hakan yayi."
Daddy ya furta yana ƙare min kallo.
Sannan ya umarce ni da na shiga wani palour da yake gefen wanda muke ciki, jikina sanyaye na shiga na zauna ina daɗa ƙarewa wajen kallo a zuciya ta ina raya cewa "zamuyi rayuwa NI DA KANNENA a irin wannan daular inshaAllahu zan basu ingantacciyar rayuwa."
Shigowar su Daddy da Dr Sabo ne ya katse min tunani na, na ɗago na kalle su a daidai lokacin da s**a zauna a kujerun da suke fuskanta ta.
Sannan Daddy ya ɗakko wata doguwar takarda ya miƙo min yace na karanta idan na amince da sharuddan jiki nayi signing za'a bani kudi na gasu na tafi dasu.
Ya saka hannun sa ya buɗe wani brief case take na ga daloli sababbi miraran, tun da nake a rayuwa ta ban taɓa ganin kuɗi masu yawan waɗannan a zahiri ba sai yau.
Mahimman abinda takardar ta kunsa shine; in dai na amince za'a daura auren a yanzu ba sai anjima ba, zan fara shirin tafiya zuwa nan da sati ɗaya zamu tashi zuwa London, ba'a yarda na fita ko'ina ba, ba'a yarda na faɗawa kowa ba, idan aiki ya kammala zan zauna acan har na haihu, sannan zan shayar da yaro na kula dashi na tsawon shekara biyu, sannan duk sanda suke bukata zasu iya karbar ɗan su daga wajena, sauran sharuddan kuma abubuwan ne da s**a shafi likitanci k**ar su; karbar magani da allurai akan lokaci, kula da cin abincin da aka keɓance da sauransu.
Bayan na gama nazarin wannan takarda kafin nayi signing na ɗago nace:
"Zan iya neman alfarma?"
Daddy ya kalleni yace:
"Zaki iya, amma babu abinda zamu iya sauya wa acikin waɗannan ka'idojin."
Nayi murmushin takaici sannan nace:
"Na sani ai ba'a canja doka, ni budurwa ce ban taba yin aure ba ballantana na haihu hasali ma ban taba yin soyayya da wani namiji ba, alfarmar da nake nema itace; ina so a bawa ƴan uwana a rubuce cewar company zai turani na ƙaro karatu ƙasar waje sannan idan naje ni kuma zan nuna nayi aure na samu ciki, saboda ya fidda kaina daga zargi."
Jinjina kai s**a yi alamar sun gamsu, sannan s**a nuna amincewar su akan hakan sannan daga bisani na rattba hannu akan takardar Ƙaddarata.
Bayan nayi signing Daddy ya dube ni yace:
"Iya mu ukun nan ne kawai muka san da wannan al'amarin, waɗancan gabaɗayansu babu wanda ya san ainahin abinda yake faruwa ba, na gayyata su ne daga nesa saboda su shaida wannan auren, saboda haka ina daɗa jaddada miki cewar kiyi shiru da bakinki."
Jinjina kaina kawai nayi ba tare da nace komai ba, sannan daga bisani muka miƙe muka koma palour da muka baro.
Ina zaune k**ar a Film aka kafa Camera aka ɗaura min aure da wanda ban sani ba, wallahi ni abun ma dariya ya bani, Dr. Sabo ne waliyyi na, aka ɗaura akan sadaki Naira dubu ɗari biyar cash aka miƙo min su a hannuna nasa hannu na karɓa acikin zuciya ta wallahi dariya kawai abun yake bani saboda gaba ɗaya ina daukar lamarin da wasa.
Ban daɗa gasgata al'amarin ba sai da naga an dauki wadannan makudan kudin an bani na taho dasu, zuciya ta sai mamakin irin wannan gangancin da Daddy yayi da waɗannan maƙudan kuɗi.
Direct banki na nufa, da mamakina cikin sauri aka yi converting ɗin kuɗin zuwa Naira, yana yin yadda ma'aikatan bankin s**a karɓe ni k**ar daman sun san da zuwan. Gabaɗaya kuɗin aka saka min su acikin account dina, bayan na ware wadanda za'a turawa da Anuwar da kuma bashin Company wanda yafi komai ɗaga min hankali.
Tambayar duniyar nan Anuwar yayi min akan inda na samu kuɗi, abinda nace masa kawai loan naci a Company, yayi ta yimin faɗa akan meyasa shi fa ya hakura amma nace kar ya damu na riga naci, sannan nayi masa albashir da na samu admission an tura ni karo karatu a London, yayi murna sosai sannan daga bisani na nufi gida da sabon aure a kaina.
Bayanin da nayiwa Anuwar shi nayiwa Ameera, hakan ya saka ta shiga damuwa nayi ta rarrashin ta ni da Baba Rabi sannan daga bisani ta hakura ta fawwalawa Ubangiji.
Bayan na nutsu ni kaɗai nayi sallar nafila nayi kuka mai isa ta nayiwa Allah kirari saboda fitar dani daga ƙuncin wannan ibtila'in kuɗin Company da yayi, ji nayi jikina yayi sakayau zuciyata ta rage raɗaɗi babu faɗuwar gaba da tunanin inda zan samu na biya kuɗin company da na karatun Anuwar, amma kuma lokacin da na tuna da haɗarin da na jefa rayuwa ta da kasadar da nayi don samun wannan kuɗi sai naji wani sabon tashin hankalin ya sake ɗarsuwa acikin zuciyata. "Ya ilahi!"
Sannan babban abinda yafi bani mamaki da tsoro shi ne idan na duba account balance ɗin bankina naga lambobin kuɗin birjik aciki, hakan yana matuƙar shayar dani ruwan mamaki saboda bantaɓa tunanin zan samu kuɗi mak**ancin irin su a rayuwa ta ba, komai dare haka nake farkawa na duba na gani, sai dai kuma sam bantaɓa farin ciki ko jin daɗin ganin su ba musamman idan na tuna ta hanyar da na same su, amma kuma daga baya nayiwa zuciyata faɗa da daɗa tabbatar mata da cewar wannan kuɗi fa halal ɗina ne ba haram ba.
Washegari driver daddy yazo ya ɗauke ni sai immagration office, akayi min International Passport, da yake abun na masu kuɗi ne dandanan aka wuce wajen.
Haka na fara shirin tafiya, gaba ɗaya shirin baya yimin daɗi saboda babu fita, sai ATM Card ɗina na bawa Ameerah ita da Baba Rabi s**a tafi kasuwa s**a yi duk wata siyayyar abubuwan da zasu bukata na tsawon shekara guda, nima naso nayi tawa siyayyar tafiyar duk da ban san me dame zan siya ba amma sai daga baya na tuna cewar acikin takardar yarjejeniyar mu an rubuta bazan tafi da komai ba ko da wayar hannuna, hakan ya saka na hakura nake ta sauraron wannan iko na Ubangiji gagara misali.
A ranar na kira Manager zan yi masa bayani ya nuna min ai takardar da na turo ta isa, ni kuma nasan babu wata takarda dana aika, haka na wayance nayi shiru sannan ya tayani murna bisa samun damar dawowa da Company hakkin sa.
Ina duba wayata naga saƙo ya shigo ta Email ɗina, takardu ne guda biyu; ɗaya tana ɗauke da albishir na cewa Company ya ɗauki nauyin Master Degree na a 'London Business School (LBS)', ɗayar kuma Admission Letter ce da take nuna alamar cewa na samu Admission a wannan jam'i a.
Da farko abun ya bani mamaki sosai amma daga bisani da na tuna duk shiri ne kuma na tabbata in dai mutum yana da kuɗi da faɗa aji babu abinda ba zai iya aikatawa ba ya saka na kauda tunanin tare da turawa da Anuwar shina ya gani, murna kam k**ar ta kashe shi don har kuka sai da yayi.
Ita kuwa Ameerah kukan rabuwa dani take yi, ni kuwa haƙuri kawai nake bata ina rarrashin ta, duk da ni kaina na sha nawa kukan kasancewar yadda muka shaƙu da juna muka taso a tare muka sha gwagwarmaya a tare bamu taɓa rabuwa da juna na tsawon lokaci ba, sai gashi yanzu dukka mu ukun zamuyi rayuwa a ƙasashe mabambanta.
Wannan ya saka ya rage kwana uku tafiyar mu na tashi da wani matsanancin zazzaɓi da ciwon kai, abun yayi tsamari sosai, nasha magani amma shiru, hakan ya saka na lalubo wayata nayi wa Daddy text message domin neman izinin zuwa asibiti.
Cikin gaggawa yayi min reply da cewar driver zai zo ya kaini asibiti, haka na kimtsa tare da taimakon Ameerah bayan ya ƙaraso muka nufi wani katafaren asibiti na masu hannu da shuni.
Bayan mun isa aka yi min gwaje-gwaje aka tabbatar da jinjina ne ya hau sak**akon rashin samun isasshen bacci da kuma yawan damuwa.
Wani kuka ne mai ƙarfi ya ƙwacemin a zuciyata kuma fargabace fal tare da tunanin tunda ƙuruciyata na gamu da larurar hawan jini.
Rarrashina likitan yayi tare da kwantar min da hankali sannan daga bisani yayi min wasu allurai waɗanda s**a sakani bacci, bayan na farka ya bani magungunna, cikin ikon Allah naji kaina sayau sannan daga bisani ya sallama ni na miƙe na shiga motar muka tafi.
Maimakon driver ya mayar dani gida sai na ga ya ɗauke hanya, cike da mamaki na kalleshi nace:
"Ina zaka kai ni kuma?"
"Alhaji ne yace na kai ki guest house ɗin sa na bayan gari."
Ya faɗa cike da girmamawa.
Bani da zaɓi haka na haƙura na zubawa sarautar Allah ido.
Guest house ɗin da aka ɗaura min aure muka nufa, ban san meyasa ba naji gaba na yana ta faɗuwa, take na fara ambaton Ubangiji "Azza wajallah!"
A harabar gidan muka iske Daddy shi kaɗai yana zubawa wasu kyawawan tattabaru hatsi, isar mu ke da wuya ya nemi waje ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun da aka ƙawata farfajiyar gidan dasu sannan nima yayi min umarnin da na zauna.
Nasiha Daddy ya shiga yi min tare da kwantar min da hankali saboda yace tuni likita ya sanar dashi dalilin rashin lafiya ta, kasancewar Daddy mutum ne mai Balaga ta magana yayi tasiri sosai a zuciya ta, hakan ya saka na samu nutsuwa sosai musamman da yace min indai naci gaba da damuwa jinina ya kai wani mataki to aikin fa da za'a yi min ba zai yiwu ba.
Hakan ya saka na kwantar da hankali na sosai, musamman da na fara tunanin "shin idan naci gaba da damuwa aiki bai yiwu ba ina zan samo kuɗin su dana taɓa na biya basu?"
Haka na haƙura na barwa Allah komai, bayan mun dawo gida na samu naci abinci sosai nasha magunguna sannan daga bisani nayi wanka na kwanta bacci.
Lamarin sai tafiya yake k**ar shirin film, haka nake zama a gaban mudubi na ƙarewa kaina kallo wai inada aure, na zauna nayi ta sheƙa dariya k**ar wata shashasha, sannan na ɗakko pillow na saka a cikina ina gwada tafiyar masu ciki ina dariya, ashe bansani ba 'wasa farin girki'.
A daren ranar da zamu tafi kasa bacci nayi hankalina ya tashi matuƙa, sai sannan tunanin wautar da nayi ya faɗo min, nayi kuka iya kuka nayi sallah nayi addu'a akan idan akwai cutarwa ko babu alkhairi ubangiji ya wargaza wannan tafiya.
Haka Ameerah itama ta kwanta jikina tayi ta nata kukan nima ina yi, idan kuka gan mu abun tausayi mun rasa yadda zamuyi, har zuwa asuba na lallaɓata muka tashi muka yi salla kasancewar na samu tsarki sannan na shirya na zauna ina jiran lokacin da driver zai zo.
Daƙyar Baba Rabi ta ɓanɓare Ameerah daga jikina na shiga mota nima ina nawa kukan, ina hangota ta Window mota tana ta birgima da tumami amma ba yadda zanyi, haka na kifa kaina nayi ta gurza kuka mai tsuma zuciya ina ambaton "yau dai na gaza saboda abun duniya na tafi na bar tsagin jikina."
Duk da bani da fargaba akan Baba Rabi nasan ko a wanne irin yanayi zata iya kula da Ameerah bana shakka ko kokwanto akan hakan, sannan ga isassun kayan da zasu buƙata daidai gwargwado na tanadar musu da duk abinda Ameerah zata buƙata na makaranta, sannan ga isasshen kuɗi dana tura acikin ɗaya account ɗina na banki na bar musu ATM Card ɗin ko da wata buƙatar zata taso amma duk da haka ji nake yi k**ar ban aikata daidai ba.
Haka nayi ta kuka babu mai rarrashina zuciya ta k**ar ta tsage, wallahi tun daga lokacin na fara danasani da nadamar wannan ɗanyen hukunci dana aikata da na san inda zan samu kuɗin nan sai na koma, sai daga baya zuciya ta ta kawo min wani tunani da tun farko na gaza kawo shi cikin ƙwaƙwalwata ballanta na tambayi mafitarsa domin samun mak**ar da zan dogara da ita;
"SHIN WANNAN AUREN DA YAKE KAINA TA YAYA ZA'A WARWARE SHI?"
Haka muka ƙarasa Aminu Kano International Airport, Daddy ya ƙaraso tare da Dr Sabo da tawagar bodyguards ɗin sa, ɗaya daga cikin securities ɗin Daddy ya miƙo min akwati trolley da hand bag sannan ya karɓe wayar hannuna, ji nayi k**ar an rabani da komai nawa na duniya amma ba yadda zanyi haka na haƙura Hausawa sunce 'Ƙaddara Ta Riga Fata', muka nufi wajen tantance matafiya, sannan daga bisani jirgin mu ya tashi zuwa Lagos.
Har zuwa lokacin da muka isa Lagos ina sharar ƙwallah, ina kallon yadda Daddy yake satar kallona da alamar tausayawar sa gareni hakan ya saka na haƙura na barwa Allah na maida hankalina na ƙarewa cikin jirgin kallo.
Duk da wannan shi ne karo na biyu na hawa jirgi amma sai da ƙauyancina ya bayyana, saboda a VIP seat muke haɗuwar cikin wajen ba sai na faɗa ba, tun da nake a rayuwa ta ko da wasa ban taɓa tunanin zan shiga mak**ancin waje irin wannan ba sai gani yau a ciki, iya wannan ma kaɗai ya isa na godewa Ubangiji da ni'imar da yayi min kasancewata ƴar ƙauye marainiya mara gata Ubangiji ya fiddoni daga cikin ƙunci da damuwa ya ɗaukakani akan maƙiya na.
Duk da na tabbatar da wani ƙalubalen zan sake riska a nan gaba, amma hakan bazai hanani godewa Ubangiji ba bisa ga ni'imar da yayi min, kuma a shirye nake da tunkarar duk wani ƙalubalen da zai sake riskata, tun da ina ji a raina zuciya ta ta fara ƙwari, tunda har na iya yarda na bar ƙasa ta na nufi inda bani da tabbas, to kuwa duk abinda zan tarar zan iya jurewa saboda na saka Ubangijina a farko al'amurana na tabbata bazan taɓa taɓewa ba.
Da wannan tunanin nawa dandanan naga mun iso 'Muratala Muhammad International Airport' da ke garin Lagos. Bayan munyi sallar Azhar munci abinci muka sake hawa wani jirgin muka lula zuwa birnin London.
Written by:
Khadija Aliyu Ibrahim
(The Healer's Pen)
[email protected]
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
KU DIN GA YI MANA COMMENTS, LIKING IN DA HALI KUYI SHARING ZUWA WASU GROUP ƊIN SHINE ZAI BAMU ƘWARIN GWIWAR KAWO MUKU LABARAI KYAUTA.