26/08/2026
ƁOYAYYIYAR DAMA CHAPTER 6
GARGAƊI❗️❗️❗️
ƁOYAYYIYAR DAMA Ƙirƙirarren labari ne daga taskar fasahar Khadija Aliyu Ibrahim (The Healer’s Pen), kuma kyauta ne.
Mun ƙirƙiri labarin ne da niyyar faɗakarwa, ilimantarwa, wa'azantarwa da kuma nishaɗantarwa. Ba da niyyar cin mutuncin wani mutum ba, gwamnati ko wata hukuma.
Kuma yana ƙarƙashin kariyar Dokar Haƙƙin Mallakar Fasaha ta Najeriya, ta shekarar 2022 (Copyright Act, 2022).
Duk wanda muka k**a da laifin siyarwa ko sarrafa labarin ta wani ɓangaren ba tare da izinin marubuciyar ba, to zai fuskanci fushin hukuma.
Daga Marubuciyar:
NI DA KANNENA
ƘWAI BIYU
LISSAFIN MATATTU
"BISMILLAHIRRAHMÁNIRRAHEEM!"
"ASSALÁTU WASSALÁMU ALÁ RASULULLÀHI (SALALLÀHU ALAIHI WA SALLAM)."
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Numfasawa tayi sannan ta duba agogon wayarta ta ci gaba da magana cikin ƙwarin gwiwa:
"Wahala ta rayuwa da jarrabawa kam na fuskance ta kala-kala, sai dai duk tsananin da na shiga ina samun ɗauki kuma bana mantawa da waɗanda s**a taimaka min a rayuwa.
Ina nan ina sane dasu duk lokacin da Allah ya nufa zan taimaka musu ko nayi wa ahalin su.
Bana mantawa da taimakon committee unguwa, da mutanen da suke ciki yadda s**a jajirce akan rayuwata. Duk da wasu daga cikinsu sun tsallaka wani mataki mai kyau na rayuwa, wasu kuma sun mutu, wasu suna raye amma inshaAllahu zan faranta musu, sannan zan ƙarfafawa wannan committe wanda shi ya zama ga ta na."
Miƙewa yayi daga kishingiɗar da yayi sannan ya kalle ta yace:
"Shin babu wanda yayi saura a dangin mahaifinki bayan Kawunki?"
Numfasawa tayi sannan tace:
"Ban san kowa daga dangin mahaifina ba bayan kawu na. Amma naji watarana Babana yana faɗawa Anty Maria cewar, ba wanda ya san daga in da mahaifinsu yazo. Saboda tsintar kansa kawai yayi a ƙauyen su Kakata a Wudil.
Wasu sunce kurciya aka yi masa.
Amma saboda ya kasance mutumin kirki ya saka Baban Kakata ya bashi auren ta. Shine ta haifi Kawuna da Babana. Bayan sun dawo cikin garin Kano yana kasuwancinsa bayan shekara ashirin da auren su ya rasu.
Babu wanda yasan asalinsa.
Su kuwa dangin Kakata ba wani sanin su muka yi ba, saboda daman ita kaɗai iyayen ta s**a haifa, kuma tun da ta rasu bamu sake ganin wani yazo daga garinsu ba.
Shiyasa bamu da wasu dangin mahaifi masu ƙarfi.
Numfasawa ya sake yi tare da jinjina kansa. Sannan yace:
"Yanzu menene babban burin ki na rayuwa?"
Ajiyar zuciya tayi sannan ta kalle shi ta kawar da kanta tace:
"Bani da burin da ya wuce na tsaya da ƙafa ta na gina rayuwa ta nayi ƙarfi sosai ta yadda zan taimaki marasa ƙarfi da yara marasa galihu iri na.
A da na so yin aure saboda ina ganin ita kaɗai ce hanyar da zan tsira. Amma da na sake hankali da wayo sai na fahimci cewar zamani ya sauya zaman aure a yanzu mace ba ta da wani ƙwaƙƙwaran abun yi shima wani ƙalubale ne mai zaman kansa.
Gashi mutanen da nake zaune dasu basu da matsala suna ƙauna ta Nima ina kula dasu haka mutanen unguwa kowa yana girmama ni yana tausayi na bani da matsala da kowa tsakani na da mutane sai san barka.
Gwara a yanzu duk ƙoƙarin da zanyi zan tsira da mutuncina, amma idan na haihu dole nauyi ya ƙaru, saboda yawancin mazan yanzu ba iya riƙe aure suke yi ba.
Muna ganin cases da yawa da suke faruwa.
Ƙawayen mu da a da suke ganin k**ar sun kere mu saboda sun yi aure, a yanzu ni nake basu sha'awa. Gani suke yi ina cikin kwanciyar hankali. Masu hassadar cikin su ne kawai zasu jefe ni da kalmar na ƙi kayi aure.
Saboda suna shan wahala a gidan mazajensu, suna baƙin cikin gani na cikin kwanciyar hankali ba su san wahalar da nasha ba, shine suke son nina nayi auren na ɗanɗana.
Ba ina yaƙi da aure bane, a'a ina son na inganta rayuwa ta ne kafin nayi saboda kar ahali na su sha irin wahalar da na sha.
Shiyasa na tsaya tsayin daka da neman kuɗi babu ruwa na da saka tension ɗin namiji a raina, idan mutum yazo da soyayya ba ni na kawo shi ba zan saka shi a bakin zuciya, idan ya tafi Allah raka taki gona Daman bashi bane.
Nayi inani in dai da rai da lafiya dole mijina yana hanya kuma zai zo ya same ni komai daren daɗewa.
Hakan ya saka na fara neman kudi ka'in da na'in, duk da albashi na amma na fara sana'a daban-daban, na fara aikin abincin biki lokaci zuwa lokaci ina samu.
Sannan daga baya na fara free order abinci.
Tun da na fara bana rasa kuɗin kashewa a rana ina iya samun order biyar zuwa goma. Idan ka ɗauke na biki da shi ba yaushe ake samu ba.
Ranar da muka haɗu da kai ranar na samu order mafi yawa wanda ta zo min bagatatan Allah yayi zamu haɗu.
Ban ji tsoron taimakon ka ba saboda nayi yaƙini duk mutumin da ya tsarkake zuciyarsa ba zai taɓa shan wahala ba.
Na taimake ka ne saboda nasan zafin wahala da haɗarin rayuwa. Sannan kuma ina da halin da zan taimake ka. Kuma a yanzu bani da tsoro, zuciyata ta dake ta sare, da a da ne tabbas ko me zan samu bazan je hotel ba.
Kuma ina jin daɗin yadda muka saba da kai ina jin ka k**ar wani jini na ko mahaifi na, ina kwatanta kyautata maka ne saboda ina ji a raina k**ar iyaye na na ke yi wa.
Saboda wanda yayi shekaru a ɗaure shi ya san zafin igiya.
Duk da ko sunan ka ban sani ba. Ban san daga in da kake ba, amma na yi yaƙini kai alkhairi ne a rayuwa ba sharri ba.
Saboda tun da na haɗu da kai mafarkai na s**a sauya, haka zan dinga ganin haske, ko ina tafiya a hanya mai kyau, ko mafarkin mukulli, ko na abinci mai kyau ko korayen bishiyu ko mafarkin turare, ko aure, mafarkin taron mutane ina can saman su.
Da na bibiyi fassarar mafarkin Ibn Sirin sai na ga duk alkhairi ne.
Hakan ya saka na kwantar da hankali na
Wannan shine ainahin labari na. A hakan ma ba komai na faɗa maka ba sai iya wanda Allah ya nufa zaka ji."
Ajiyar zuciya s**a yi gabaɗayansu, ɗakin yayi tsit kowa yana nazari a cikin ƙwaƙwalwarsa. Can Zarah ta sake ɗagowa ta kalle shi tace:
"Amma don Allah Baba wanene kai, daga ina kazo? Meyasa ake bibiyar ka? Menene sunan ka?"
Murmushi yayi, sannan ya kalle ta yace:
"Ki kwantar da hankalinki Mamana in dai labarina ne da kanki zaki taka ki je in da zaki same shi."
Fuskarta cike da tambaya tace masa:
"Ban fahimce ka ba?"
"Ai yanzu ba zaki taɓa fahimta ta ba, sai nan gaba."
Haka ya miƙe ya nufi tsakar gida domin yayi alwala ya barta a zaune a cikin ruɗani...
****************************
Yau tsawon kwana biyu da kammala bashi labarin ta. Amma yaƙi ya ce mata komai game da waye shi. Hakan yayi matuƙar saka ta a damuwa da ruɗani.
Gashi sam ya daina bata fuska k**ar da, ya rage zama ma a gidan sai dai kawai ta ganshi a ƙofar gida yana nazari.
Yau ma k**ar kullum haka ta sakko ta g*ishe shi, sai dai da mamakinta ta ga ya haɗa kayansa tsaf a akwatinsa. Saboda daman Zarah bata barin sa da wanki.
Cikin kiɗima da tashin hankali ta ƙarasa in da yake ta durƙushe a gabansa tace:
"Baba nayi maka laifi ne? Na ga k**ar tafiya zaka yi?"
"Ko kusa Zarah ai sai dai ni na tambaye ki. Wa'adin zamana ya ƙare dole zan tafi na sauke nauyi."
Take ta ji zuciyarta ta karaya hawaye sun fara zubowa daga idon ta. Ta miƙe tsaye tace:
"Ka tsaya ka karya sai na raka ka ka hau mota."
"A'a Mamana ana jira na. Ki kwantar da hankalinki bana jin yunwa."
Ta sani sarai wannan ba al'adarsa bace, mutum ne da baya wasa da cikinsa, sannan ta hango damuwa ƙarara a fuskarsa.
Saboda haka tayi ta roƙonsa amma fafur ya ƙi amincewa dole ta haƙura ta shirya domin ta raka shi.
A sanyaye ta sanar da Maman Sadiq itama haka ta dinga ƙorafi akan zai tafi babu sanarwa. Dole s**a haƙura s**a ƙyale shi. Ta ɗauki kayansa s**a fita t**i.
Maimakon su nufi tasha sai yace su tafi wata unguwar daban. Haka mai napep ya nufi ɗaya daga cikin manyan ungunnin GRA da suke birnin Kano, suna isa wani ƙaton fili ta hango da wasu jibga-jibgan motoci Landcruiser guda biyu sunyi parking da wasu bodyguard guda biyu suna tsaye a jikin motar.
Sai da s**a ƙarasa dab, sannan s**a sakko daga napep ɗin s**a ƙarasa, suna dab da bakin motar ɗaya daga cikin bodyguard ɗin ya taho da sauri ya karɓi akwatin hannun Zarah da ƙaramar jakar.
Anan ne Baba ya tsaya cak! ya juyo ya kalli Zarah da take ta kuka yace mata:
"Kiyi hakuri Mamana. Na gode sosai da yadda kika kula dani kuma kika ceci rayuwa ta Allah ya saka miki da alkhairi Allah ya sake tsare rayuwarki.
Sannan ina miki nasiha duk in da kika tsinci kan ki a rayuwa to ki kiyaye mutuncin ki, sannan kar ki zamo mai saɓa alkawari, sannan ki zamo mai riƙo da amana.
Sannan ki kiyaye kimarki da darajarki, saboda nan ba da daɗewa ba mutane zasu tsaya a gabanki suna neman wata alfarma. Kar ki sare da rayuwa, karki tsorata da matsayin da Allah zai baki. Sannan ina da ɗa jaddada miki cewar: KARKI SAƁA ALƘAWARI."
Har yayi gaba ya juyo ya sake kallon ta yace:
"Akwai wani lissafi da nayi, idan har ya tafi daidai to zan fi kowa farinciki."
Sannan ya shige cikin ɗaya daga cikin motar aka mayar da ƙofar aka rufe. Take shima ya ji wasu hawaye sun zubo masa saboda yadda ya ga ta durƙushe a ƙasa tana kuka.
Basu jira ba wannan motocin s**a fara tafiya cikin ƙanƙanin lokaci s**a gushe daga wajen k**ar ma ba'a taba yin su ba.
Haka ta kasance a durƙushe tana kuka mai tsuma zuciya har sai da ta gaji ta tashi ta hau napep ta nufi gida.
*************************************
Tun daga wannan ranar Zarah ba ta da walwala, ba farin ciki, ko order abinci ta samu ba ta yi, sai dai ta kwanta a ɗaki tayi ta kuka. Ta rasa me yake damunta da wannan tsohon lokaci guda ta ji ya shiga ranta.
Kullum cikin kewa take a sannu hankali kuma da aka koma makaranta ta koma baki aiki, sai ta fara rage damuwarta, amma ba zata taɓa iya daina kewarsa saboda ya shiga cikin jerin mutanen da ba zata mantawa da su ba.
Tsawon sati biyu da tafiyarsa, tana girkin wani biki da ta samu, kwatsam sai yaro ya shigo yace ana sallama da ita.
Tana fita ta iske wasu mutane guda biyu a tsaye.
Bayan sun g*isa s**a tambaye ta cewar ita ce Zarah Sulaiman Tela? tace itace sai s**a bata wata brown ɗin envelope s**a tafi.
Da ta dawo gida ta buɗe ta iske wasu takardu guda biyu dukkan su form ne amma da number waya a jiki.
Da sauri ta kira number aka ce mata wata gidauniya ce da take son tallafawa mutane s**a zaɓeta ta cike form ɗin zasu ɗauke ta aiki gobe ta zo headquarters da takardunta.
Cikin murna kuwa ta cike har tana nunawa Maman Sadiq tana taya ta murna.
Washegari haka ta shirya da kwatance ta je office ɗin su. Anan s**a yi mata albishir da sun ɗauke ta aiki s**a nuna mata office ɗin ta.
Nan fa ta fara murna amma ta sanar dasu cewar tana aikin gwamnati yau ma excuse ta ɗauka. S**a ce mata babu komai duk su ma suna aiki amma sun fi zuwa nan weekend saboda haka itama weekend zata zo.
Haka ta dinga murna ta dawo gida ta sanar wa da Maman Sadiq itama ta taya ta murna.
To da Asabar tayi haka ta shirya ta tafi aiki. Ranar meeting s**a yi akan matsalolin da s**a addabi unguwannin cikin gari. Nan fa s**a fara tambayar Zarah. Nan fa ta fara zayyano musu musamman matsalolin rashin ruwa.
Aikuwa aka ɗauki shawararta nan da nan aka fara yin tsarin yadda za'a kawar da matsalar rashin ruwa a wannan unguwannin.
Nan fa aka kafa team aka bata shugaba s**a fara shiga lungu da saƙon na unguwannin suna yin survey da analysis akan yadda za a kawar da matsalar.
Haka ta zauna ta dinga bada shawarwari suna ɗauka, aka kirawo masana take aka ƙaddamar da aikin gina rijiyar borehole mai amfani da hasken rana guda dubu a unguwannin tsakiyar birnin Kano.
Wannan mataki ba ƙaramin faranta mata rai yayi ba. Ranar kasa bacci tayi. Haka sauran ƴan unguwa s**a dinga murna suna saka mata albarka.
Haka aka fara aikin cikin nasara da tsarin kowacce unguwa aka tsara yadda za'a yi da inda za yi. Aka samar da masu kula da wannan boreholes ɗin aka ɗauki ma'aikata a unguwannjn da zasu din ga bawa cibiyar kowacce unguwa tsaro.
Kafin kace me, ruwa ya fara wadata, al'umma sai san barka suke yi suna maraba da Zarah foundation.
Har zuwa wannan lokacin Zarah bata san wanda ya assasa wannan gidauniya ba, in takaice muku zance bata san cewa saboda ita aka ƙirƙiri wannan gidauniya ba. Ba Ta san cewar dabara akai mata domin a samar da ruwa wadatacce a waɗannan unguwanni ba.
Abubuwan da Zarah bata sani ba suna da yawa mai karatu.
Babban abinda ya bata mamaki shine yawan albashin ta. A ƙalla kusan naira dubu ɗari shida a wata, banda allowance. Abun yayi matuƙar ba ta mamaki.
Hakan ya saka ta shiga yin alkhairi da kuɗin, duk wanda take da burin taimaka masa sai da tayi masa alkhairi musamman Anty Maria da su Abban Sadiq.
Haka ta yi musu borehole acikin gidan, sannan ta saka musu standard solar 24hours, ta yi musu fenti, sannan ta inganta kayan sana'ar ta.
To haka ta ci gaba da aiki na tsawon lokaci. Tana samun albashin ta. Bata ajiye aikinta na gwamnati ba, aikin abinci kuwa wani lokacin Maman Sadiq ce take yi domin itama ta samu nata, musamman na order.
Haka Zarah ta dinga tara kuɗin ta tsawon watanni. A yanzu kam bata da matsala sam sai ta rashin aure itama tana roƙon Allah ya kawo mata lokacin, saboda a yanzu tunaninta ya fara karkata kan itama ta yi aure ta haihu ta ga yaran ta.
Da ta samu hutu ta je har Nijar gurin Anty Maria ta kai mata kayan arziƙi. Nan fa ta dinga murna ta rasa in sa zata saka kanta.
A can ma haka samari s**a yi mata caaaa...amma taƙi tace ita ba za ta iya zaman Nijar ba. Kuma a yanzu kam ba kowanne namiji zata iya aure ba. Saboda ta san kanta tana duba goben ta da ta ƴaƴanta.
Haka ta lallaɓo ta dawo da niyyar idan ta sake samun lokaci zata je Maiduguri dangin mahaifiyar ta. Ko ba komai ta gansu su gana.
Haka ta koma bakin aikin ta.
A hankali s**a fara ƙaddamar da ayyuka kala-kala a cikin birni. Kamar koyawa matasa sana'a da basu injina da jari. Sannan da ɗaukar ɗawainiyar marayu da marasa galihu.
Wannan ya jawowa Zarah farin jini sosai a cikin mutane, musamman manyan mutane saboda Allah yayi mata kyau da diri gashi yanzu hankalinta ya kwanta ta ƙara yin kyau matuƙa.
Haka gidajen jaridu na kafofin sada Zumunta s**a dinga hira da ita saboda yadda ta dinga yaɗa manufofin wannan ƙungiyar ta su da ayyukan alkhairin da suke yi.
Da haka kafafen sada zumunta s**a san Zarah Sulaiman Tela.
************************
To kwanci tashi asarar mai rai yau kusan wata biyar kenan da tafiyar Baba. Amma har yau ta kasa mantawa dashi.
Kullum cikin kewar sa take da tsammanin kiransa, amma shuru.
Wata rana tana scrolling a Facebook kawai ta iske shafin BBC HAUSA sun yi posting din wani hoto mai matuƙar ɗaure kai sun rubuta:
"ALLAH YAYIWA SHARARREN ATTAJIRIN NAN ALHAJI AL-HASAN IBRAHIM ƊANBATTA RASUWA A GIDANSA DA YAKE A BIRNIN LONDON."
Take ta jefar da wayar da take hannunta, saboda k**ar hoton Baba ta gani. Babanta da ya tafi ya barta yau tsawon wata takwas.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un."
Abinda ta dinga maimaitawa kenan a lokacin da idanuwanta s**a tabbatar mata da cewar tabbas shine babu kokwanto.
Zubewa tayi a ƙasa ta fara zaro idonta cike da tsoro, sannan ta sake kallon fuskarsa tayi zooming sosai ta tabbatar da cewar shine babu kuskure.
Take ta ji kanta ya sara. Ƙirjinta ya fara dukan uku-uku bata ankare ba ta ga wani duhu ya gifta mata.
Ita dai kawai farkawa tayi ta ganta a gadon asibiti.
Gefe ga Maman Sadiq tana yi mata sannu.
Zumbur ta yi ta miƙe zaune ta fara tuna abinda ya faru. Take ta ɗora hannunta a ka ta rusa wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Ta rasa ta ina zata fara.
Ta rasa ta in da zata yi wa mutane bayani.
Shin daman wannan Dattijon shine Alhaji Al-Hassan Danbatta dai da ta sani a duniya?
Shi ta ajiye a ɗakin ta na tsawon wata guda?
Shi ta ceta a hotel?
Shi ta ciyar da hannun ta?
Da shi ta zauna tsawon wannan lokacin su yi hira, su yi dariya ya kira ta da Mamansa?
Babban abun tashin hankali ma, wai shine ya rasu?"
Haka ta dinga kuka babu yadda Maman Sadiq bata yi ba a akan ta faɗa mata ko meye, amma ta ƙi sai zumbur da tayi ta miƙe ta fita.
Dolan su s**a rubuta mata sallama.
Tana isa gida ta sake ɗakko wayar ta dinga bin shafukan sada zumunta, haka ta dinga cin karo da Labaran mutuwarsa, tarihin rayuwarsa, da gwagwarmayar da yayi. Ciki har videos ɗin sa kala-kala na lokacin da yake da ƙuruciya da lokacin da yake a yanzu.
Adadin ƴaƴansa, ayyukan alkhairin sa, da tarin dukiyar da ya mutu ya bari.
"Tabbas Baba ya rasu, Allah ya jiƙanka da rahama."
Haka ta shiga uwar ɗaki kan katifar da yake kwana ta kwanta ta din ga kuka cikin dare tana tuna hirar su tana tuna yadda yake santin abincin ta da ranar da s**a haɗu, da ranar da ya tafi ya barta da maganganunsa na ƙarshe.
"Baba kai ma ka tafi ka bar ni...daman kace ni zanje in da labarin ka yake da kaina...ba kai zaka faɗa min ba..."
Haka ta dinga maimaitawa tana kuka yadda ta ga rana haka ta ga dare.
Washegari tun kafin kowa ya tashi ta shirya ta fice, saboda ta samu labarin za'ayi jana'izar sa a babban masallacin juma'a na garin Ɗanbatta. Haka ta tafi tasha ta hau mota, ta nufi garin.
Tun da s**a doshi garin suke cin karo da cincirindon mutane ana ƙoƙarin shiga. Duk da sai an idar da sallar juma'a za'a yi masa sallah, amma tun safe garin ya cika maƙil da manyan mutane ta ko ina daga ciki da faɗin Arewacin Najeriya.
Da ƙyar ta samu hanya ta shiga masallacin ta hau sama ɓangaren mata. Daga nesa tana hango komai. Ta saka face mask banda kuka babu abinda take yi.
Haka ta dinga yi masa addu'ar neman rahamar Ubangiji gashi babu hali, ballantana ta je kansa ta yi masa addu'a.
Wa ma ya santa?
Waye zai yarda da ita?
Ta ina zata fara yi wa mutane bayani?
Amma da son samu ne da tayi bankwana da gawarsa.
Haka ta ci gaba zama, tana daga zaune ta hango motar asibiti ta shigo wajen da jami'an tsaro an shigo da gawar.
Nan fa hankalinta ya sake tashi, ta miƙe tsaye. Take numfashinta ya fara ɗaukewa sai zaunar da ita mata tayi ta fara yi mata firfita.
Sai da aka idar da Sallar juma'a sannan tarin al'umma s**a sallace shi ciki har da Zarah.
Sannan daga bisani aka ɗauki gawar aka nufi gidan gonarsa in da za'a binne shi.
Haka ta dinga bin zugar mutane a ƙafa k**ar mahaukaciya tana tafe tana kuka har sai da s**a iso.
Can wani bene ta sake hawa daga nesa ta hau tana hangowa aka saka shi acikin makwancinsa. Mutane suna ta kuka ba maza ba mata kowa yana faɗar alkhairinsa musamman mutanen garin Ɗanbatta.
Haka tayi jigib a ƙasa har la'asar da mutane s**a fara watsewa, sannan ta hango mutane suna ƙoƙarin zuwa in da kabarin yake domin su yi masa addu'a.
Haka itama ta miƙe da ƙyar ta iya ƙarasawa.
Amma daga can nesa take iya hangowa, saboda jami'an tsaro da suke a tsaye sun katange wajen babu wanda yake iya ƙarasawa.
Saboda an ce ɗansa ne a tsaye a wajen, babu yadda ba'a yi dashi ba, amma ya ƙi barin wajen, yana tsaye kyam ko motsi ba yayi.
Haka ta dinga zagaye a wajen ko da zata iya hango kabarin daga nesa, amma inaaaa...babu hali, dole ta haƙura ta bar wajen ta na yi masa addu'o'in samun rahamar Ubangiji Mahalicci.
Haka kowa na wajen ya watse babu kowa a wajen har kusan sallar la'asar.
Sai wannan kyakkyawan saurayin dogo a tsaye k**ar gunki.
Sanye yake da wandon jeans (dark blue slim-fit), da baƙar riga mai hula (charcoal hoodie), da wata farar riga a ciki (crew net T-shirt), a kansa akwai wata baƙar hula (baseball cap) tare da wani baƙin glass (sunglasses).
Hannunsa na hagu ɗaure yake da wani tsadadden agogo (Patek Philippe Aquanaut), sannan ƙafarsa ɗauke take da wani baƙin takalmin fata (leather Chelsea boots), ƙugunsa ɗaure yake da wani tsadadden belt sai sheƙi ya ke yi.
Ya zira hannayensa duka biyun a cikin aljihun wandon, fuskarsa ta ɓuya a cikin duhun hular rigar, da kuma ɓakin glass ɗin da yake fuskarsa.
Baka iya fahimtar ainahin halin da yake ciki, ballantana ka fassara yanayinsa, ko k**anninsa.
Sai dai abinda na sani shine, ya tsaya ne kyam tsayuwa irin ta jarumai. Tsananin lokacin da ya ɗauka a tsaye da kuma ruwan sama mai nauyi da aka fara tafkawa bai saka ya girgiza ba, ko ya nuna alamar gajiyawa....
***********************************
Tun da Zarah ta rasa Baba ta sauya matuƙa, ta shiga ruɗani gashi ta kasa faɗa wa kowa komai. Sai ƙarya ta yi wa Maman Sadiq ta ce mata wani saurayinta ne ya mutu.
Haka ta shiga damuwa tana mamaki da almara akan yadda akayi ya ɓoye mata asalin ko shi waye, da yadda aka yi ya iya rayuwa da ita a haka. Har yake iya cin abincinta, yake kuma kwana a wannan gidan duk da hakan haɗari ne ga rayuwarsa.
Shin meyasa ka ake neman sa?
Me ya saka ya ɓuya a hotel?
Me yasa ɓoye mata asalin sa?
Me ya saka ya jaddada mata kalmar ta riƙe alƙawari?
Shin wanne alƙawarin yake nufi?
Waɗanne mutane ne zasu tsaya a gaban ta suna neman alfarma?
Shin wanne irin lissafi ya yi da yake fatan ya tabbata?
Shin ma menene musabbabin mutuwarsa?
Idan muna son mu samu amsoshin waɗannan tambayoyin, dole sai mun yi haƙuri mun sake waiwayawa baya domin bin diddigin ainahin labarin Alhaji Al-Hassan Ibrahim Ɗanbatta.
Anan ne zamu samu amsoshin waɗannan tambayoyin, da ma waɗanda babu sani ba.
Sannan daga bisani mu ɗora...
The Healer's Pen ✍️
[email protected]