14/07/2025
*KADA KA ZAGI MAMACI*
-
Domin shi haƙiƙa ya haɗu da abinda ya aikata a duniya.
-
"Wato yana daga cikin irin kuskuren da mutane suke aikatawa shine su dinga zagin mamaci, (wanda ya mutu), ta iya yuwuwa ko ya zalunce su ne kafin ya mutu, ko kuma dai yayi musu wani abinda ransu baiso ba, to lallai kuwa kusani cewa ba'a zagin wanda ya mutu, addua kawai yake buƙata daga gareku, shi musulmi hatta gawarsa ma saida musulunci ya bata kariya"
-
"Manzon Allah ﷺ, kada ku zagi matattu domin su haƙiƙa sun haɗu da abinda s**a aikata"
Sahih Al-Bukhari
-
"Idan sharri ya aikata to yanzu ya haɗu dashi, idan kuma alkhairi ya aikata to haƙiƙa yanzu ya haɗu abinsa"