26/04/2026
HANYOYI 6 YADDA ZAKA GYARA ALAƘARKA DA ALLAH.
Kafin ka yi tunanin cewa addu'arka bata karɓuwa, baka ganin wani cigaba a rayuwarka, ko ƙunci ya yi maka yawa wanda ka rasa menene dalilin... Ina son ka fara gyara tsakaninka da Mahaliccinka gabanin ka zargi asiri ko mayun unguwa.
Duk lokacin da layin sadarwa ya katse tsakaninka da Asalin Mai raba arziƙi, to tabbas abin da ake bayarwar zai tsaya cak a gare ka. Ga hanyoyi 6 na Sirri da zasu sake haɗa wannan igiyar, su dawo maka da natsuwa a yau:
1. Gyara Sallah A Kan Lokacinta:
Babu wata alaƙa tsakanin bawa da Ubangijinsa da ta wuce Sallah. Idan kana wasa da Sallah, ko kana haɗa su a lokaci guda saboda fafutukar neman kudi, to tabbas kana fafutukar rusa rayuwarka ne.
2. Tsaftace Hanyar Samun Kuɗinka:
Annabi (S.A.W) ya faɗa mana cewa mutum zai yi tafiya mai nisa, ya ɗaga hannu yana roƙon Allah, amma ba za a amsa masa ba saboda abincinsa haramun ne, tufafinsa haramun ne. Idan jarin da kake juya wa akwai cuta, damfara, ko cin haƙƙin wani a ciki, koda kayi kuka jini addu'arka gagara zata yi.
3. Yawaita Neman Gafara:
Mafi yawan lokuta, zunubanmu da laifukan da muke aikatawa a ɓoye sune suke zama kamar baƙin gajimare su toshe mana ƙofar arziki. Samun lokaci a cikin dare ka zauna kai kaɗai kana yawaita "Astaghfirullah".
4. Kyautata Alaƙa Da Iyaye Da Ƴan Uwa:
Igiyar da take haɗa ka da Allah tana da alaƙa kai tsaye da igiyar dake tsakaninka da Iyayenka. Idan iyayenka suna fushi da kai, ko kana tauye haƙƙinsu domin ka burge mutanen waje, ko ka yanke zumunci saboda ɗan abin duniya, to kofofin samunka a rufe suke.
5. Ciyar Da Na Ƙasa wato Sadaqa A Ɓoye:
Idan kaga abubuwa sun kulle, ka matse a asusu, to a lokacin ne ya kamata ka fitar da ɗan abin da ya rage maka ka bawa wanda yafi ka buƙata. Sadaka tana kashe fushin Ubangiji, tana kariya daga masifa, kuma tana tilasta wa ƙofar arziki ta buɗe.
6. Kyakkyawan Zato Da Miƙa Wuya:
Ka Daina zargin cewa Allah ya manta da kai ne ko baya jin addu'arka. Allah yana amsa addu'ar duk wan