06/09/2025
Kungiyar Barcelona na ci gaba da nuna sha’awa ga ɗan wasan tsaron Sporting CP, Gonçalo Inácio.
Rahotanni sun nuna cewa Hansi Flick na neman ƙarfafa bangaren tsaro bayan rashin gamsuwa da wasu daga cikin ‘yan baya na yanzu.
Inácio, wanda ke taka rawar gani a Portugal, yana cikin jerin masu zafi da Barça ke bi, duk da cewa Manchester United da Liverpool suma suna zawarcinsa.
⚽️ Shin kuna ganin Barcelona za ta iya lashe wannan gasa wajen kawo shi Camp Nou?