12/02/2024
Ƙasurgumin ɗanta'adda
Wannan wani ƙasurgumin ɗanta'adda ne da rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta kame, a lokacin da yake ƙoƙarin samun mafaka domin ya ci gaba da zaluntar jama'a.
Kamar yadda kakakin 'yan sandar jihar Kano, Malam Kiyawa ya bayyana a shafinsa, ya ce; "Isah Lawal, Dan Shekaru 33, Dan Ta'adda ne dake zaune a kauyen Kaya, Karamar Hukumar Giwa, Jihar Kaduna. An kamashi da shanu 55 da tumaki 6 a Garin Karaye, bayan ya baro Dajin Birnin Gwari da yunkurin kafa sansanin garkuwa da mutane a daji tsakanin Gwarzo da Karaye da ke Jihar Kano."
Allah ya ci gaba da kare al'umma daga sharrin jemammun miyagu, amin.