Hausa books readers

Hausa books readers MUNA GABATAR MUKU DA=:

*labaran soyayya
*labaran nishadi
*labaran duniya
*neman shawara

03/12/2021

ABINDA AKE GUDU 🙆🏽 1

Batul Mamman💖

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Daki ne cike da 'yan mata sai hayaniya suke yi. Wasu suna saka kaya wanda ya kasance atampa ce ja mai adon baki, wasu kuwa kwalliya suke yi a gaban madubi. Wadanda basu sami wuri a gaban madubin ba da na jikin hodarsu suke amfani ana ta fentin fuska cikin nishadi.

Suna wannan hirar da shewa wata mace da bazata wuce shekaru talatin ba ta shigo da katon cikinta ita ma irin atampar jikinsu ta saka tayi kwalliya daidai gwargwado cike da damuwa ta soma magana.
" don Allah kuyi sauri ku fito ku ake ta jira. Umma sai fada take min babu amarya babu kawayenta. Kun dai san tayi ta kashedi akan African time".

Wata cikinsu wadda da alama ta gama nata shirin tace "kiyi hakuri Anti Shema'u yanzu zamu fito".

"Babu wani yanzu zaku fito. Ina Asma'un?" Ta fada tana dube dube.

Can gefen gado ta hango kanwar tata ana rangada mata kwalliya irin ta amare tayi kyau sosai. Kusa dasu Shemau ta koma ta sake nanatawa mai kwalliyar tayi sauri ta gama a fito da amarya. Ita dai Asma'u har yayarta ta gama magana bata ce komai ba saboda kada ta bata kwalliyarta. Wannan rana ce mai matukar mahimmanci a rayuwarta. Ranar kamunta da mutumin da take ganin tamkar babu irinsa a duniya.

Har Shema'u ta fara tafiya tayi saurin dawowa da sauri ta sake kai idonta gaban rigar jikin amarya. Daure fuska tayi " duk amaryar duniya idan ana bikinta rama takeyi saboda zulumin barin gida da sabuwar rayuwa banda ke Asmau. Dubi yadda rigar nan ta sake matse ki duk kirjinki ya fito ta sama".

Hannu Asmau tasa ta rufe jikinta saboda yadda 'yan uwa da kawayenta na dakin s**a maido da kallonsu gareta. Shemau ta cigaba da magana "ki tabbatar abinda zaki yafa ya rufe miki kirji don bani da amsar bawa Umma idan ta fara fada." Daga nan ta fice tana mamakin irin wannan jiki na kanwarta. Dama can ita mai jikin kiba ce....

******
Farfajiyar gidan ta gama cika da mata inda aka kawata wani bangare da ado irin na gargajiya domin zaman amarya. Ga kujeru da tebura wurin yayi kyau sosai harda turaren wuta na tsinke da na garwashi aka kunna sai kamshi ke tashi.

Mai gabatar da taron mace ce ta nemi kowa yayi shiru saboda amarya zata fito. Mai kida ya canza salon kidansa da wanda ya dace da amarya aka fara ita da kawayenta s**a fito suna taku daidai.

Sunyi matukar kyau da burge mutane da irin salon fitowarsu. Aka dauki tafi, masu hoto kuwa na camera da na waya s**a fara aikinsu. Haka s**a rinka tafiya har s**a karasa inda zata zauna. Autarsu ce Aina'u 'yar kimanin shekaru sha uku a tsaye da mafici irin na kaba yayarta na zama ta soma yi mata fifita a hankali. Hakan ma ya kayatar da mutane.

Hajiya Bara'atu dake zaune cikin 'yan uwanta da kawaye har 'yar kwalla sai da tayi. Gashi cikin ikon Allah karo na biyu kenan da zata aurar da daya daga cikin 'ya'yanta. A hankali tace " Allah Ka jikan Alhaji" bai rayu yaga auren 'ya'yansa ba bare yaga jikokin da s**a fara tarawa.

Daga nan fa aka soma shagalin biki inda aka bukaci dangin ango su fito domin kamun amarya. Suna tahowa Asma'u ta bawa Walida aminiyarta wayarta ta rada mata a kunne ta dauketa a hoto idan ana fesa mata turaren kamun. Walida tace "uhmm su Asmau an iya soyayya. Nasan sarai Abubakar zaki turawa".

Asmau ta juya ido tana fari "ke kuwa an hana bawan Allah ganin iyalinsa dole na taimaka masa da hoto". Dariya duk s**a yi sannan aka cigaba da biki.

******
Ana soma kiran sallar magriba aka gama taron shiyasa dama Haj Bara'atu ta rinka nanata musu banda African time. Sallah aka tafi a gabatar harda amarya wadda ta gaji sosai. Dakinta s**a nufa ita da kawayenta s**a yi tasu sallar. Tana idarwa aka fara yi mata tayin abinci, kafin a kawo ta dauki wayarta ta turawa Abubakar hotunan kamu.

A lokacin yana tare da abokinsa Qasim. Shi dai Qasim gani yayi Abubukar ya dan matsa ya fara waya. Murmushi yayi don yasan da wa ake wayar. Hira suke yi sosai yana fada mata yadda tayi kyau da kuma rashin jindadinsa da aka hana shi zuwa wurin kamun.

Karshen gado ta koma ta rungume waya suna ta hira. Tun ana cewa ta sauko ga abinci har s**a gaji s**a dena. Ba su s**a gama wayar ba sai da ya fara jin kiran sallar isha daga masallacin gidansu wanda suma su Asma'u shi din suke ji. Sallama s**a yi tare da alkawarin zai kirata anjima.

Tana saukowa daga kan gadon ta dafe cikinta "yunwa nake ji k**ar na kwana ban ci abinci ba"

Walida ta dan harareta "abincin ai ba jiranki zaiyi Juliet. Ni nayi tsammanin a irin soyayyarki da Romeo din naki baku san yunwa ko kishiruwa ba idan kuna tare".

"Nasan ba wani abu ke damunki ba sai tafiyar da rabin ranki Babangida yayi gashi ba kya samunsa a waya sosai" Asmau ta fada cikin tsokana ai kuwa Walida ta jefeta da pillow tana fada. Babangida yaron gidansu Walida ne irin almajiran nan marasa kunya gashi ya kware wurin kaiwa matar babansu gulmar duk abinda take yi shiyasa ta tsane shi. Har kusan daya na dare 'yan matan s**a kai suna hira sannan bacci ya dauke su. Wasu akan gado wasu a katifun da aka shinfida a kasa.

Cikin bacci Asma'u taji wayarta na kara ta dauka cikin magagi. Tana ganin sunan mai kiran ta wartsake.

Cikin taushin murya yace " Asmy na tasheki daga bacci ko?"

Sai a lokacin ta kula karfe hudu da kwata na dare sunfi wata daya yana tashinta a irin wannan lokacin dama.

Ta dan shafa idanu "babu komai Yayana yau mun so mu makara ma".

"To a tashi ayi a nemi kusanci da Allah. I love you Asmy."

Murmushin da yake so a gareta tayi sannan tace "me too Yayana".

Bayan ta ajiye wayar tashi tayi ta fita ta tafi bandaki ta dauro alwala. Nafila tazo ta fara yi sannan ta dukufa istigfari k**ar yadda s**a sabarwa kansu ita da Abubakar har aka kira assalatu. Sake kira yayi ya tabbatar idonta biyu sannan ya tafi masallaci ita kuma ta tashi 'yan matan dakin ta tayar da tata sallar.

*****
Yau ta k**a alhamis babu wani taro da za'ayi a gidan sai karfe bakwai da rabi da za'ayi dinner da daddare.

Qasim yazo har gida ya sami Abubakar tare da takardar da aka bashi ta canjin wurin aiki da karin matsayi. Abin takaici ana bukatar lallai yaje ya gabatar da kansa a sabon ofishin da aka tura shi a Zamfara kafin litinin mai zuwa. Abubakar ya taya shi murna sai dai sunyi bakincikin bazai sami dinner da daurin auren abokin nasa ba. Abubakar duk ya shiga damuwa Qasim ya rinka kwantar masa da hankali.

Abubakar yace "yanzu tunda ka zama ACP Qasim to sai ka nemo mana mata musha biki."

Dariya Qasim yayi "wace mata zan nemo bayan kasan albashin dansanda har yanzu bai taka kara ya karya ba."

"A dai rinka godewa Allah" Abubakar ya fada yana saka takalmi. Har bakin mota ya raka Qasim. Dukkaninsu basu ji dadin zuwan canjin aikin a wannan lokacin ba.
******

Kwalliyar Asma'u ta yau har tafi ta jiya. Kawaye da 'yan uwanta kowa yayi irin nasa adon. Anti Shema'u, 'yarta Mimi da Aina'u kayansu iri daya. Mazan gidan su biyu suma shadda s**a saka iri daya.

Suna gama shiryawa motar ango tazo daukar amarya. Shima kayansa ya dace da nata. Tun a gida ake daukarsu hotuna haka a wurin dinner din. Abin ya kayatar saboda komai anyi shi cikin nutsuwa irin na 'yan boko. Duk motsin Asma'u idon Abubakar yana kanta suna hada ido sai suyi murmushi. Soyayya ce da ta samo asali tun farkon tarewarsu Asma'u a unguwar su Abubakar shekaru tara da s**a wuce.

Sai wurin shadaya da rabi aka tashi daga taro kowa ya tafi gida. Wani abokin Abubakar ke tuka motar s**a ajiyeta a gida sannan s**a wuce.

******
Washegari Juma'a gidan commissioner k**ar yadda duk 'yan unguwa s**a sakawa gidansu Abubakar sun tashi a makare saboda gajiyar da s**a kwaso a wurin dinner da kuma sanyin da aka tashi dashi.

Mahaifinsu Alh Adamu Matawalle tsohon dan sanda ne har commissioner ya taba yi. Da taimakonsa Qasim ya sami aiki ma. Matarsa daya Yalwa wadda suke kira Mama. Su shida ta haifa. Babban danta sunansa Abdulhalim yana da mata daya da 'ya'ya biyu sai mai binsa Nasiba itama tana gidan nata mijin. Abubakar ne na uku amma kannensa mata biyu Sadiya da Suwaiba duk sunyi aure. Su biyu s**a rage shi da autansu Umar.

A gaggauce s**a tashi domin baifi awa daya da rabi ya rage musu ba lokacin daurin auren ya yi. Mata s**a tashi aka shiga kitchen saboda abokan Baba k**ar yadda suke kiran mahaifinsu a gidan zasu ci abinci idan an taso daga wurin daurin auren. Ga samari 'yan uwa da s**a kwana a gidan su ma shiyasa aka yi ta layin shiga wanka a bandakuna biyun dake bangaren maza. Da gangan s**a ki barin Abubakar ya fara shiga a cewarsu shi ango dole a jira shi.

Baifi minti talatin ya rage ba Umar ya fito daga bandaki kumfar jikinsa bata gama fita ba Abubakar ya shiga ya rufe kofar da mukulli.

Sauran samarin babu wanda ya tsaya cin abincu s**a fita dama wurin daurin auren babu nisa daga gidan ko a kafa zasu iya karasawa kofar gidan kakan Asma'u tunda bayan layi ne.

Duk an gama taruwa iyaye suna daga cikin katon soron gidan sauran mutane suna daga waje duk an cike layin. Alh Adamu ya kira Abdulhalim yana tambayarsa ina Abubakar. Abdulhalim yace "inajin yana waje kasan halinsa da kunya karshenta ya ki shigowa."

A waje kuma abokansa ke tambayar juna ko ya shige ciki ne domin basu ganshi ba.

Babu wanda ya saka damuwa a ransa har aka gama daurin auren kowa yana tunanin yana wani wurin.

A can gidansu kuma Haj Yalwa ce ta kira wata yarinya cikin 'yan uwansu tace ta duba mata kowane bandaki na gidan ta dauko bota a cika su da ruwa a ajiye a waje saboda abokan Baba. Idan sunci abinci zasu yi shirin sallar Juma'a.

Yarinyar tayi ta zagaye tana dauko buta. Kofar bandakin dake cikin dakin Umar ce ta kasa budewa sai ta koma ciki ta fadawa Nasiba. Tare s**a dawo s**a yi ta kokarin budewa s**a kasa ga ruwa kuma ya fara fitowa ta karkashin kofar bandakin. Nasiba ta saka kunne jikin kofar taji alamun famfo yana zubar da ruwa. Mama s**a sanarwa tace a samo wani ya b***e kofar saboda kada ruwan bangaren ya kare tunda tanki ne. Abu ya hada da mata s**a kasa budewa ga ruwan yana yawa.

Dole s**a hakura har Allah Yasa aka fara dawowa daga wurin daurin auren. Lokacin duk sun tsince kayan dake kasan dakin saboda ruwa. Umar na shigowa Mama ta hau shi da fada shi bai ma san laifin da yayi ba sai da tace yaje ya bude kofar bandakin shi. Yayi mamakin jin kofar a rufe ya saka iya karfinsa ya soma dukanta. Babu kowa a dakin sai shi kadai don Mama tace babu mai taya shi gyarawa. A bugu na hudu kofar ta bude yayi tozali da abinda yayi matukar razana shi.

Abubakar ne kwance cikin ruwan da ya hade da jini daga kasan kansa ga sabulu can a gefen kafarsa ta hagu alamun zamewa yayi.

30/11/2021

:💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞

🌹 *_KHALEESAT_*🌹
🙎🏼🙎🏼🙎🏼


```Maman Abd shakur```

_PAGE_
0⃣1⃣

Saukowan jirginsu kenan maisuna
ARIK
AIRLINE a national airport abuja.
wanda
daga Indonesia yake, aikam na
gyara
zama dan naga masu fitowa daga
jirgin.
Wasu mata da maza nagani wanda
ga
dukkan alamu yan makarantane
suna
sanye cikin uniform dinsu dogon
wanda
da red riga saidan hijab akansu
dukansu
irin kayanne a jikinsu.
Kutsawa nayu cikin students din
chan
nahango wasu yan mata su 3 wanda
ga
dukkan alamu bazasu wuce 17
years ba.
Biyu farare daya kuma chocolate ce.
Mai suna fateema amma suna
cemata
TEEMA COOL tace ma mai suna
CHUCHU
da KHALEESAT wlh wanan
compition
din da school dinmu s**a turamu
yayi,
yakuka kawatar ashe haka Indonesia
keda kyau? atleast mudan bude ido,
chuchu tace abii my sis. Teema tace
wai
maisa khaleesat yau bata magana?
tun
muna cikin jirgi bata cewa komi, ko
abinci da akabamu bata ciba cofee
kadai
tasha, chuchu tace wlh nima
nadamu,
khaleesat tai musu murmushi batare
datace komiba duk maganan nan
dasukeyi tafiya suke.
Suna fitowa s**aga motar
makarantan
su tazo daukansu mai suna
TURKISH
INTERNATIONAL SCHOOL.
Suna shiga motan khaleesat taji
gabanta
yacigaba da faduwa rike kirjinta tayi
saikuma tafashe da kuka sosai.
Teema da chuchu s**a daddafata,
chuchu tace khalee kidena kuka plz
kifadamana meke damunki, teema
tace
ko bakida lpy ne?ko ciwon cikinki
yatashine? Khaleesat ta girgizakai
tana
matsar hawaye.
Chuchu tace khalee kinfasan dad
nawa
yace zaisai ma dukanmu gift inhar
mukai wining kuma munci soo cheer
up.
Khaleesat ta share hawayen
muryanta
mai k**a da tayara kuma karama
tace
chuchu, teema wlh bansan mesaba
jinake
k**an wani abu zaifaru dani yau, i
can
feel it, dama tun tuni nake bad
mafarki,
takara fashewa da kuka tace i can
feel it
wlh my destiny is going to change
today
tacigaba da kuka.
Chuchu da hawaye yacika mata ido
dan
su ukun suna bala’in son junansu,
idan
antaba daya to antaba dukansu,
iy

30/06/2021

Kukara hakuri

30/06/2021

Aslm kukara hakuti

27/05/2021

Ku qara hakuri zamu fara posting inshaAllah

07/05/2021

Assalamu alaikoum inshaAllah zamu fara posting kwananan InshaAllah

A big thanks from a good friend of mine who introduced me to this platform which I trust to invest 20k and my account wa...
25/08/2020

A big thanks from a good friend of mine who introduced me to this platform which I trust to invest 20k and my account was credited with 60k.... actually I thought it was a scam before but I invested in my time. two and I received my reimbursement ... this is why I am introducing all my friends to benefit from it and the platform name is OLYMPIC INVESTMENT PLATFORM .... and of course it is legitimate and the platform is such a valuable resource in today. If you are interested in private conversations I registration is continuing in the platform now click below to register with them follow this path and get started directly. You can call MD at 08105313274 or click this link to chat with MD of the platform 👇
https://api.whatsapp.com/send?phone=+2348105313274&text=Hello%20sir

23/08/2019

'NI da 'YAR TALLA' (1)

Daga Na Ƴar Talla

Kasancewar ni mutum ne me yawan karance-karance, musamman ma abin da ya shafi tarbiyyantar ƳAƳA MATA, wannan tasanya na shiga bincike dangane da rayuwar matasan Ƴan mata masu TALLA.

Mafi yawan karance-karancena nakan karanto cewar TALLA masifa ne, kuma mataki ne na farko a wajen lalata tarbiyyar Yara, musamman Ƴan Mata, daga ƙananan har manyan, zuwa kan ZAWARAWA da ma kuma wasu masu auren da suke sana'ar sayar da abinci, ko dai a cikin kasuwanni ko bakin tituna, ko kuma manyan makarantu, dama duk wani gurbi da ake iya samun mai tallan abinci ko wani abin siyarwa da ya danganci Ci da Sha.

Na fara da wannan matashiyar ne dan na haskowa mai karatu suffofi da kuma rukunan masu mak**anciyar irin wannan sana'ar ta TALLA. Duk da cewar a kowane irin rukunin al'umma sai ka samu na Allah, wanda yake tafiyar da lamuransa da tsarkakakkiyar zuciya.

Wasu da farko s**an shiga sana'ar da niyyar samun kuɗin shiga dan su rufawa kansu asiri, wanda daman wannan tunanin shi ne tunani mafi kusa da gaskiya akan ko ma wace irin sana'a mutum yayi nufin aiwatarwa. Sai dai daga baya manufar kan iya juyewa ta canza launi da k**anni ta rikiɗe ta koma kan son abin duniya, da kuma mafarkin mallakar sa ta ko ma wani irin hali ko yanayi, wanda kuma babu makawa sai an kaucewa layi.

Daman kuma yana daga cikin sunnar rayuwa, muddin ka sauka daga kan tubalin farko da ka ginu a kansa, to LA budda sai ka fuskanci gararambar rayuwa. Da wannan mafi yawan masu TALLA s**an canza manufar su ta farko da tasanya s**a fara sana'ar da suke, wanda a ƙarshe danasani ne ke maye gurbin arziƙin da aka samu.

Bibiyar da nayi akan wannan matsalar ba ƙaramar bibiya bace, dan na ɗauki tsawon lokaci ina bin sawun bincike na kafin na yanke tunanin watsawa duniya abin da ke akwai dangane da hakan. Sai dai kuma, dan na gujewa s**ar ra'ayin mabiya da kuma makaranta labarin, akwai buƙatar na sanar da cewar duk abin da zan zayyano ya ta'allaqa ne kawai ga fahimtar da nayiwa binciken nawa, dan haka akwai buƙatar a ƙare ni da sa ni, ko kuma a nusashsheni inda na kuskure dan na daidaita akan SIRAƊAL-MUSTAQIM.

Allah ya tallafa mini wajen kaucewa s**ar ra'ayi ko fahimtar wani.

31/07/2019

YOUR NAME IN JAPANESE. Please write your name
in Japanese language, let's see how it will sound.
A= ka, B= tu, C= mi, D= te, E= ku, F= lu, G= ji, H=
ri, I= ki,| J= zu, K= me, L= ta, M= rin, N= to, O=
mo, P= no, Q= ke, R= shi, S= ari, T= chi, U= do, V=
ru, W= mei, X= na Y= fu, Z= zi.

07/07/2019

```BUDURWAR AREWA```

*BAHAUSHIYA*

1.Ka Nuna Mata So Taja Maka Aji.
2.Kayi Mata Kyauta Ba Godiya.
3.Kaje hira Ta Shanya Ka A Waje.
4.Ka Yabeta Agun Abokai Ta Zageka Agun Kawaye.
5.Ka Amince Da Ita Ta Yaudareka.
6.Ka Bata Waya Ta Sayar Tace Ta Fadi.
7.Kai Mata Anko Tace Dan Wahala.
8.Ka Tura Mata Kati Ta Kira Wani.
9.Ka Mutunta Ta Ta Wulakanta Ka.
10.kaki zuwa inda take tace dama baka son ta.
11.Ki Karanta Ki Wuce Kinji Tsoro Na.
12.Ki Zage Ni *Keda Allah.*
13.Ki Bar Maganar Acikinki Bazatayi Miki Maganin Yunwa Ba.
14.Ki ji Haushina din *domin adoke bazan doku ba*
😄😄😄

Address

Kano
KANOSTATE

Telephone

+2348142068355

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa books readers posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausa books readers:

Share

Category