FOCUSpride.NG

FOCUSpride.NG Shop for your pride.

07/02/2026

Good Morning

mā kāna muḥammadun aba aḥadim mir rijālikum wa lākir rasụlallāhi wa khātaman-nabiyyīn, wa kānallāhu bikulli syai`in 'alī...
13/09/2024

mā kāna muḥammadun aba aḥadim mir rijālikum wa lākir rasụlallāhi wa khātaman-nabiyyīn, wa kānallāhu bikulli syai`in 'alīmā
jumma'at kareem

28/08/2024

Idan aka baka naira TRILLION DAYA zaka cigaba da aiki ko denawa zaka yi?

MU HADU A COMMENTS SECTION.

26/08/2024

Wanda bai sha kashi ba,ba ya jin bari.

06/12/2023

Ina ya tuni, wai shin ya za’ayi masu tsare rayukan Al’umma ace sunyi kuskure. Ni a tuna ni na wannan rashin kwarewa ne.

Menene Ra’ayin ku game da wannan lamari ?

15/12/2022

Wata Babbar Kotun Shari'ar Muslunci ta yankewa Sheikh Abduljabbar Kabara hukuncin kisa a Kano.

Aliyu Samba

Babbar kotun shari'ar Muslunci dake zaman ta a Kofar Kudu ƙarƙashin Mai Shari'a Alkali Ibrahim Sarki Yola ta yankewa Sheikh Abduljabbar Kabara hukuncin hukuncin kisa ta hanyar rataya dogaro da sashe na 392(b) na Kano state Shari'a Penal Code.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan bayyana ra'ayin ta game da shari'ar da aka ɗauki tsawon shekara da watanni ana gudanarwa a babbar kotun shari'ar.

An gabatar da Malamin Sheikh Abduljabbar Kabara a gaban kotun a ranar 16 ga watan July, 2021 bisa zargin kalaman ɓatanci da rubuta al'umma wanda s**a saɓa da sashe ba 392 (b) na ACJL, zargin da Malamin ya sha musantawa.

Mai Shari'a Ibrahim Sarki Yola ya yanke hukuncin a yau Alhamis 15 ga watan Disamba, 2022 ya kuma yi umarnin a kwace masallatai biyu da malamin yake da su, Masallacin Ashabul Kahfi dake Gwale sani mai Nagge, da kuma Jami'urrasuli dake tukuntawa gidan maza a jihar Kano.

Kotun ta kuma yi umarnin haramta wallafawa ko sanya hotunan sa da sunan yada manufar sa, ta kuma haramta tallata aƙidar sa da sanya karatukan sa a gidajen Radio, talabijin da kuma kafafen sada zumunta, ta kuma yi umarnin ga gwamnatin jihar Kano da ta da yan sanda su k**a duk wanda ya saba wannan umarnin.

Farfesa Mamman Lawan Yusufari SAN wanda yayi magana a madadin lawyoyi masu gabatar da ƙara ya sheda cewa sun gamsu da wannan hukuncin da Kotun ta yankewa Sheikh Abduljabbar.

Saidai a nashi bangaren, Sheikh Abduljabbar Kabara ya hakurkurtar da mabiyansa inda yace zai yi mutuwa ta girma, kuma baya rokon sassauci daga mai Shari'a.

''Ni bana neman sassauci akan wannan laifi da ban yi ba, ina bawa masoyana hakuri, kar su samu damuwa kan tafiya ta lahira, zanyi mutuwa ta girma, kuma bana neman kai Ibrahim Sarki kayi mun sassauci, kuma a gaggauta yi mun hukuncin nan. Kalami na na karshe kenan. '' inji Sheikh Abduljabbar.

Saidai bamu samu jin ta bakin Barista Aminu Ado wanda ya rikewa Barista Dalhatu Shehu Usman a matsayin lawyan wanda ake ƙara sak**akon ficewar sa da wuri bayan kammala shari'ar, kuma bamu same shi a waya ba har zuwa kammala wannan rahoto.

Jarida Radio
15/12/22

New brand design. For N5000
11/05/2022

New brand design. For N5000

10/05/2022

Affordable training suit

Address

No. 16 Karkasara Behind Akth. Kano
Kano
930222

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when FOCUSpride.NG posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to FOCUSpride.NG:

Share