21/09/2024
1. Idan kana so ka gane mai iya taimakonka a lokacin da musiba ta faÉ—a maka, ka duba wanda ya tallafi abokin tafiyarka a lokacin da musiba ta faÉ—a masa.
2. Idan kana so ka fahimci yadda abokanka zasu iya tsayuwa akan matsalarka, ka fara bincikar kanka, mutum nawa ka tsayawa akan matsalarsa?
3. Yau da zaka kwanta mummunar rashin lafiya mai zafi, ina mai tabbatar maka zaka samu kula, irin kular da ka ke yiwa abonkan hulÉ—arka a lokacin da s**a samu kansu a cikin irin wannan yanayin.
4. Idan kana so kaga yadda iyalinka zasu kasance bayan mutuwarka, ka duba yadda iyalan abokananka s**a kasance bayan mutuwarsu.
5. Idan kana so ka fahimci irin jimamin da za a yi bayan rasuwarka, ka auna irin jimamin da aka yi bayan rasuwar abokan hulÉ—arka, wata kila bai wuce kwana biyu kacal ba!
6. Idan kana so ka fahimci makomar gobenka, ka duba ya makomar waÉ—anda s**a gabace ka take, musamman waÉ—anda kuke aikata aiki ko abebe iri É—aya.
7. Idan sana'a ka ke, ko aiki, yana da muhimmanci ka kalli ya ƙarshen masu irin wannan sana'ar ya ke ko ya ƙarshen masu irin wannan aikin ya ke. Domin idan ba wani iko na Ubangiji ba, kaima nan ne ƙarshenka.
8. Akwai yiyuwar yadda ka ke mu'amalantar budurwarka kamin ku yi aure, haka wanda ke neman Æ´arka zai mu'amalance ta. Yadda ka ke kula da matarka, haka za a kula da Æ´arka a wani gidan.
9. Yadda ka kula da taimakawa iyayenka a lokacin rayuwarsu, haka Æ´aÆ´anka zasu kula da kai a lokacin tsufanka!
10. Aikin da ka shuka a rayuwarka ta duniya, da shi za a tunaka bayan mutuwarka, kuma shi zaka riska a kabari haka kuma shi ne linzamin makomarka a gobe kiyama!
Barkanmu da Asuba
- Abubakar Umar