04/03/2025
Gaskiya tayi karanci. Babu tsoron mutuwa a zuciyar Al,uma. Kuma kowa sai ya mutu. A yau Ina tare da wani bawan Allah sai wani matashi ya kirawo wayar sa yace nine wane.,sai s**a gaisa saboda sun san juna .. matashin nan sai yace da mutumin akwai sakon ka an bani in baka akwai shinkafa rabin buhu 25kg da taliya katan daya da s**ari 20kg da Kuma man girki 10kg.Alhaji wane Kuma Saraki ne yace a baka dama duk shekara yana bayar wa a kawo maka,tun yana turo maka da babban buhu da babbar jarkar Mai.. yace ayi hakuri da wannan. Mutumin da muke tare yayi godiya yace zai tura a dauko... ya tura aka dauko. Ashe wakilin da ake baiwa shekara da shekaru bai taba baiwa mutumin sakon ba.. "Mutuwa ta riske shi" an chanja wanda ke da alhakin rarrabawar,shi ne Allah yasa yasan da haka.Shin mai karatu kana cikin irin wadannan mutane wadanda idan an baka sako ka Kai kake ragewa ko kuma ka hana ka cinye? Matasa ayi hattara Allah baya yafe hakkin wanda aka zalunta..Kuma komai dadewa asiri sai ya tonu. Rike Gaskiya ka Sha mamaki..
MUSHA RUWA LAFIYA. ALLAH YA KARBI IBADA. AMIN
Sako daga.
Hamisu Lamido Iyantama.