31/03/2026
TSOKACI: Rikicin Plateau da neman k**a Dan4Ne (Maha): Ya zama wajibi hukumomi su yi dalci kan daukar mataki ba tare da wariya ba -Zagazola
Daga: Ayau News || Zagazola Mak**a
Ana ci gaba da tattaunawa da cece-kuce a Jihar Plateau kan batun adalci da daukar mataki iri daya ga kowa, bayan wasu kungiyoyi sun bukaci a k**a wani dan barkwanci mai suna “Maha” ko saboda kalaman da ya yi bayan rikicin da ya faru a Barkin Ladi.
Rahotanni sun ce rikicin ya biyo bayan wani harin ramuwar gayya da ya yi sanadin mutuwar matasa biyar Hausawa, lamarin da ya kara tayar da hankali a yankin.
Bayan faruwar lamarin, matasa daga bangarori daban-daban sun bayyana fushinsu ta hanyoyi daban-daban, inda wasu daga cikin kalaman da aka yi s**a kasance masu tayar da hankali.
Daga cikin wadanda s**a yi irin wadannan kalamai akwai Maha/ , wanda bidiyonsa ya yadu a kafafen sada zumunta, lamarin da ya jawo s**a da kuma kira a k**a shi.
Sai dai wasu na ganin cewa ana nuna son kai, domin su matasan Jos (Birom) din ne ma s**a fara kalamai masu tsauri a bidiyoyi kowa ya gani wanda shi ya jawo wannan hari wanda idan da adalci su ma ya k**ata a fara k**awa a hukunta.
Rahotanni sun nuna cewa wasu shugabannin matasa na kabilar Birom sun yi kalamai masu tsauri, ciki har da gargadin daukar fansa da kuma cewa zaman lafiya ya kare, kiri-kiri a bidiyo,
Haka kuma, an ji wasu ma har cewa s**a yi za su dauki mataki kan duk wanda aka gani daga wata kabila, kalamai da masana ke ganin na iya kara rura wutar rikici, su ma ya k**ata a kamo su.
Akwai kuma zarge-zargen cewa wasu manyan mutane masu daa'war Fasto ci ne sun yi kalamai da ake ganin sun kara dagula lamarin, maimakon kwantar da hankali, su ma ya fi k**ata a kamo.
Mak**a Zagazola na ganin irin wannan yanayi na rikici, kalamai na da matukar tasiri, kuma duk wani furuci da ya kunshi barazana na iya haddasa karin tashin hankali.
Ya jaddada cewa dole ne a rika daukar mataki bisa adalci, ba tare da wariya ba, domin tabbatar da adalci ga jama’a.
Gwamnati ta bukaci kowa da kowa da ya kwantar da hankali, tare da kira ga shugabanni da matasa da su guji kalaman da ka iya haddasa rikici.
Haka kuma, an bukaci jami’an tsaro su mayar da hankali wajen gano wadanda ke da hannu kai tsaye a hare-haren tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Me zaku ce?
LIKE // SHARE & FOLLOW ~ Ayau News