19/09/2022
*RAYUWA A TSAKANIN MUTANEN BIRNI DANA KAR'KARA*
Tsakanin mutanen birni dana kar'kara akwai rayuwa mai matukar kyau da cikakkiyar
tarbiya.
Mutanen birni suna rayuwa daban da mutanen dake zaune a kar'kara, sai dai mafi yawan mutane muna mantawa da cewa asali na kar'kara , tarbiya na can,zaman lfy na can, amana na can, jarumta na can.
Al hali kuma mutanen kar'kara basu damu da wasu Abubuwa da mutanen birni s**a damu dasu ba, misali kamar haka:-
(1) wutar lantarki
(2) wurin shakatawa
(3) na'urar kallo(television)
(4) motar hawa da dai sauransu.
Amma kuma duk da haka suke rayuwa cikin aminci da yarda.
Mutanen birni sun yi sabo da Abubuwa masu yawa waΙan da babusu/ko basu yawaita a
Kar'kara ba kamar:-
(1) wayar hannu iri daban daban
(2) motocin hawa iri iri
(3) gidaje na alfarma
(4) makarantu na boko iri iri
(5) manyan asibitoci
(6) wuraren shakatawa
(7) wuraren kwanan baki(hotel)
(8) hanyoyin sadarwa (Network)
Amma duk da haka zakuga mutanen kar'kara sunfi mazauna birni lafiya,tarbiya,biyayya,iya neman halat, jarumta da dai sauransu.
Mafi yawan cin abubuwa da mutanen birni ke amfani dasu s**an yi sanadiyar lalacewar tarbiyar wasu, s**an yi sanadiyar cin haram ga wasu,kuma s**an yi sanadiyar mutuwar zuciyar wasu da kuma girman kai da kyamatar wasu yan'uwa ta hanyar amfani dasu ba yanda ya kamata ba.
Amma kuma mafi yawan mu mun kasan ce duk mun guji
Kar'kara domin zuwa birane mu zauna, idan har komawa birni ya zama dole to mu Ιauki wannan tarbiyya da kuma al'adunmu na kar'kara mu tafi dasu sannan mu haΙa da tarbiyyar da muka isko a birni mai kyau muyi amfani dasu.
Tsaya ka fahimci rayuwa dan uwa hakan ba faduwa bane domin na Bayanka suyi alfahari da asalinsu
ποΈποΈποΈποΈποΈποΈποΈποΈποΈποΈποΈποΈποΈποΈ
*COMRD Auwal isah