18/06/2023
WANENE SARKIN SIYASAR KANO ?
Daga Malam Bello Muhammad Sharada
A ganina shekara 24 sun isa a bayar da kambu na sarautar siyasa a Kano, a wannan jamhuriyya ta hudu. An yi masu mulki samfuri guda uku. Wanda Allah ya nufa da ransu da lafiyarsu da shekarunsu, sun ga yadda Injiniya Rabiu Kwankwaso ya mulki Kano a 1999-2003 da kuma 2011-2015. Sun ga yadda Mallam Ibrahim Shekarau ya yi nasa mulkin a jere 2003-2011. Haka kuma kwana 20 da s**a gabata aka ga karshen mulkin Dr Abdullah Ganduje.
Za a iya baiwa Sanata Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano matsayin sarautar Sarkin Siyasar Kano saboda tsarin siyasar sa hade yake da salon tarihi da addini da siyasa da sarauta da kasuwanci da ya baiwa Kano shuhura a duka fadin duniya. Duk dan siyasar da ya yi daidai a dabi'a da tafarki da tunani da koyarwar magabatan Kano shi ne sarkin siyasar Kano. Sarkin siyasa ba shi ne wanda ya fi cin takara ko shiga zabe ba, A'a, Sarkin Siyasar Kano shi NE; wanda yake siyasa tare da la'akari da yadda na baya s**a yi da kuma yadda ake lala siyasa a sauran sassan duniya, sannan kuma sakamakon siyasarsa yake komawa kan akasarin jama'ar da ya fito daga cikinsu kuma s**a amfana matukar gaske da tsarinsa, ba biyan bukatarsa ko 'yan tsiraru da ke kewaye da shi. Babu mai wannan siffar sai Shekarau, Sardaunan Kano..
Ina da dalilai guda tara:
Na farko, Shekarau ne mutane s**a zabe shi tsabarsa da karfin kuri'ar ra'ayoyi na jama'a masu son sauyi ba a jam'iyyar gwamnati ta jiha, ba kuma ta karfin mulkin tarayya
Na biyu, Shekarau shi ne dan siyasar da ya yi mulkin jama'a basa tsangwamarsa, ya maimaita a jere kuma ya bar mulki ya ci gaba da mu'amala a cikin kowa babu hantara, ana kewarsa.
Na uku shi ne kadai dan siyasar da ya shigo siyasa da manufar sananniya, ta ra'ayoyi na addini, sannan kuma bai sauya daga inda aka san shi. Shi din nan dai shi ne.
Na hudu shi ne kawai dan siyasar Kano da babu wani jinsin jama'ar Kano da bai tafi da shi ba, kuma har zuwa yau ake buga misali da shi. Ya tafi Sarki da malami da talaka da attajiri da mata da matasa da 'yan boko da 'yan gargajiya.
Na biyar shi ne dan siyasar Kano mai tsananin bin tsarin dimokuradiyya da ka'idojin jam'iyya a kan mulki da wajen mulki.
Na shida shi ne dan siyasar Kano kacal mai bin tsarin aikin gwamnati a mulki da mu'amala kuma mai mutunta umarnin kotu uwar kowa.
Na bakwai shi ne dan siyasar da ya baiwa jama'a dama da jawo su kusa da gwamnati da basu 'yancin fadar albarkacin bakinsu da walwala ba tauye hakki. Bai zama dodo ba a gurin jama'a.
Na takwas shi ne dan siyasar jihar Kano Mai koyi da Sardaunan Sakkwato a tausayi da kyauta. Mai dabi'a ta kishin na kasa kamar Aminu Kano. Mai yafiya da rangwame ba ramuwar gayya kamar Abubakar Rimi, mai tsabtar zancen siyasa kamar Musan Musawa.
Na tara shi ne dan siyasar jihar Kano da bai tara dukiya ba a Kanon da wajenta, kuma bai yi amfani da gwamnati don gina tuwonsa da miyarsa. Sannan a siyasarsa babu yaudara da farfaganda da jamhuru da bita da kulli. Siyasarsa ta tawaliu ce da maida komai gurin Allah da jama'a.
IDAN DA MAI JAYAYYA
GA FILI, GA MAI DOKI