Harshe TV

Harshe TV HARSHE TV 📺 | Breaking News • Entertainment • Interviews • Community Updates | Muryar Jama’a, Tushen Sahihan Labarai.”

09/08/2026

Download the app → goliveindia.in/download

02/08/2026

Jamin horas da daliban soji ya bukaci su kasance masu da'a rikon amana da hidimtawa kasa.

01/08/2026

#

‎Hon. Sanusi Samaila Judugu, wanda aka fi sani da Hasken Giade, ya yi kira ga Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Senator Ba...
30/07/2026

‎Hon. Sanusi Samaila Judugu, wanda aka fi sani da Hasken Giade, ya yi kira ga Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Senator Bala Abdulkadir Mohammed (Kauran Daular Usmaniyya), da ya sanya aikin titin Giade Jugudu Kurba har zuwa ɓullo ta yankin Darazo cikin jerin sabbin ayyukan hanyoyi da gadoji guda 24 da za a aiwatar da su da tallafin Bankin ECOWAS na Zuba Jari da Raya Ƙasa (EBID).

‎Kiran na Hasken Giade ya biyo bayan sanarwar da Gwamna Bala Mohammed ya fitar, inda ya bayyana cewa Jihar Bauchi ta samu tallafin kuɗi na dalar Amurka miliyan 91.6 daga EBID domin aiwatar da manyan ayyukan hanyoyi da gadoji guda 24 a sassan jihar.

‎A cewar gwamnan, ayyukan za su inganta hanyoyin sufuri, sauƙaƙa zirga-zirgar jama'a da kayan amfanin gona, faɗaɗa hanyoyin kai kayayyaki kasuwanni, tare da ƙarfafa bunƙasar tattalin arzikin Jihar Bauchi.

‎Hon. Sanusi ya bayyana cewa saka titin Giade–Jugudu–Kurba zuwa ɓullo ta yankin Darazo cikin waɗannan ayyuka zai kawo gagarumin ci gaba ga al'ummomin yankin, musamman wajen bunƙasa kasuwanci, noma da kuma sauƙaƙa zirga-zirga.

‎Ya kuma nuna fatan gwamnatin jihar za ta yi la'akari da wannan buƙata domin tabbatar da cewa al'ummomin yankin Giade da Darazo sun amfana da wannan muhimmin shiri na ci gaban ababen more rayuwa.

29/07/2026
24/07/2026

Tsira Aminci Daraja Martaba Matsayi Girmamawar Allah su kara tabbata gareka ya farkon tashi da shiga Aljanna
MUHAMMAD RASULULLAH

Tsohuwar jarumar fina-finan batsa ta zama Sanata a ColombiaAn rantsar da tsohuwar jarumar fina-finan batsa, Deyci Alejan...
24/07/2026

Tsohuwar jarumar fina-finan batsa ta zama Sanata a Colombia

An rantsar da tsohuwar jarumar fina-finan batsa, Deyci Alejandra Omaña Ortiz, wadda aka fi sani da Amaranta Hank, a matsayin sanata a ƙasar Colombia bayan ta lashe zaɓen da aka gudanar a watan Maris.

Ortiz za ta wakilci yankin Norte de Santander a majalisar dattawan ƙasar a ƙarƙashin jam'iyyar Historic Pact na wa'adin 2026 zuwa 2030.

Ta ce tarihin rayuwarta bai kamata ya hana ta yin hidima ga al'umma ba, tana mai jaddada cewa ma'aikatan masana'antar nishaɗin manya suna da gudunmawa ga tattalin arzikin ƙasa kuma sun cancanci kariya da amincewa a ƙarƙashin doka.

Sabuwar sanatan ta kuma bayyana cewa za ta mayar da hankali kan batutuwan lafiyar ƙwaƙwalwa da yaƙi da cin zarafi ta hanyar jima'i, duk da s**a da ce-ce-ku-cen da naɗinta ya haifar a fagen siyasar Colombia.

DA DUMI-DUMI: Trump ya yabawa Tinubu kan jagorancinsa a yaƙi da ta'addanciShugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yabawa...
22/07/2026

DA DUMI-DUMI: Trump ya yabawa Tinubu kan jagorancinsa a yaƙi da ta'addanci

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan abin da ya kira jagoranci mai ƙarfi wajen yaƙi da ta'addanci da matsalolin tsaro a Najeriya.

A wata wasiƙa da ya aike wa Tinubu mai kwanan wata 6 ga Yuli, 2026, Trump ya ce yana goyon bayan ƙudirin gwamnatin Najeriya na magance hare-haren 'yan ta'adda, musamman waɗanda ke shafar al'ummomin Kiristoci.

Ya kuma ce haɗin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya na ci gaba da ƙarfafa, inda ƙasashen biyu s**a kafa Kwamitin Haɗin Gwiwa kan Tsaro domin musayar bayanan sirri, horas da jami'an tsaro da gudanar da ayyukan haɗin gwiwa.

A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, haɗin gwiwar ya taimaka wajen kai farmaki kan maɓoyar ISIS a yankin Tafkin Chadi a watan Mayu, inda aka kashe babban jagoran ƙungiyar, Abubakar Al-Minoki, da wasu manyan kwamandojinta.

Trump ya kuma tabbatar da aniyar Amurka na ci gaba da haɗa kai da Najeriya wajen yaƙi da ta'addanci da inganta tsaron ƙasar.

GIDAN GWAMNATIN JIHAR BAUCHISANARWAR MANEMA LABARAIGWAMNA BALA MOHAMMED YA AMINCE DA ƘANANAN SAUYE-SAUKYE A MAJALISAR ZA...
17/07/2026

GIDAN GWAMNATIN JIHAR BAUCHI
SANARWAR MANEMA LABARAI

GWAMNA BALA MOHAMMED YA AMINCE DA ƘANANAN SAUYE-SAUKYE A MAJALISAR ZARTASWA TA JIHAR

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, CON, FNIPR (Kauran Daular Usmaniyya), ya amince da yin wasu ƙananan sauye-sauye a cikin Majalisar Zartaswa ta Jihar a matsayin wani ɓangare na ci gaba da ƙoƙarin gwamnatinsa na ƙarfafa shugabanci da inganta ayyukan yi wa al'umma hidima a faɗin jihar.

A cikin sauye-sauyen, Kwamishinan Kasuwanci, Masana'antu da Zuba Jari, Alhaji Mohammed Salis Gamawa, da tsohon Kwamishinan Ilimi wanda daga bisani aka mayar da shi Ma'aikatar Wutar Lantarki, Kimiyya da Fasaha, Dr. Mohammed Lawal Rimin Zayam, sun fita daga Majalisar Zartaswar Jihar nan take. Haka kuma, Gwamnan ya amince da murabus ɗin tsohon Kwamishinan Raya Karkara da Harkoki na Musamman, Hon. Faruk Mustapha.

Domin tabbatar da ci gaba da ingantaccen gudanar da mulki ba tare da tangarɗa ba, an miƙa sunayen waɗanda aka zaɓa domin maye gurbinsu, tare da sauran waɗanda aka tsayar domin cike guraben da s**a samu sakamakon ficewar wasu kwamishinoni a baya, zuwa Majalisar Dokokin Jihar Bauchi domin tantancewa da amincewa.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana matuƙar godiya ga kwamishinonin da s**a bar muƙamansu bisa sadaukarwa, jajircewa, da gudunmawar da s**a bayar wajen ci gaban Jihar Bauchi a lokacin da s**a yi aiki. Ya yi musu fatan alheri da nasara a rayuwarsu ta gaba, tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da gina gwamnati mai inganci, mai sauraron jama'a, kuma mai samar da kyakkyawan sakamako domin amfanin al'ummar Jihar Bauchi.

Mai Sa Hannu:
Mukhtar Gidado, MNIPR
Mai Bai Wa Gwamna Shawara Na Musamman kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a
17 ga Yuli, 2026.

17/07/2026

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka zata sayarwa Saudiya makamai na makudan kudade.

Address

Giade
Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Harshe TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share