07/04/2026
Sansanin Hausawa 2 : A Kalamaina Ba Kunya
Gaskiya mutum ya rinka nuna abun da yake so a waje, kar abun ya zame mishi matsala. Kamar dai ni din nan, idan ina son abu to ba ni shakkar bayyanar da shi a gaban ko ma wane ne. Na tuna da wasu tambayoyi da yan jarida s**a yi min game da karatu da rubutun Hausa da nike yi. Kamar yanzu a ce an tambaye ni mi ya sa nike fadar wasu kalaman a cikin litattafan da nike rubutawa. Misalin wasu littattafai da na rubuta irin Rikincin Rayuwa, Boyayyar Manufa da kuma Matar Maigidana. Saboda na rubuta su a kan yadda wasu suke rayuwa tare da kawaye ko kuma yan uwa, rigimar sai cikin gida. Kamar yanzu a littafin Rikincin Rayuwa, labarin wata budurwa ne na rubuta wadda ta samu ciki kuma aka rasa na wane ne tsakanin babanta, yayanta da kuma saurayinta. Sannan a cikin littafin Boyayyar Manufa, na rubuta rayuwar wani mutum mai biya ma matan alhazzai bukata kasancewar wasu daga alhazzan ba su da karfi ko kuma gamsarwa kamar yadda ake bukata. Sai kuma littafin Matar Maigidana, shi kuma na rubuta shi ne a kan rayuwar wata mai aikin gida wadda take yin le***an. A cikin haka ne wasu suke tambaya ta mi ya sa ba ni sanya kunya a cikin litattafan da nike rubutawa. Sai nike cewa ba rashin kunya ba ne ai kowa yana da wasu kalamai da yake jin nauyin fadarsu to ni ban ga hakan ba a kalaman da nike rubutawa ba. Kuma abun da ma ya sa nike bayyana irin kalaman kaya haka saboda na taba jin wani ciwo a cikin gabana to kuma ina son in bayyana ma mahaifiyata amma ina nuku-nuku irin ba zan iya fada ba. To ana haka dai har abun ya kai ya kawo na ji idan ban fada ba fa zan wahala sai na bayyana cikin ikon Allah aka yi min maganin abun. Zan iya fadar kowace kalama da turanci ko da ta batsa ce amma kuma sai in ji kunyar fadarta a yaren Hausa, na ce kai malaman nan fa ba ni na kirkire su ta ya zan yi dar-dar wajen amfani da su. Tunda ga tambaya mai sauki, ya ne mutum zai bambanta bura, nonuwa, da kuma duri tunda duk gaba ake ce musu?