Hasken Musulunci

Hasken Musulunci Wannan shafin an bude shi ne domin fadakarwar musulumci.

11/03/2026
’YAN UWANA MU KIYAYE SALLAR ASUBA A CIKIN JAM’I.Sabida tana da tarin falala sosai, kuma tana daga cikin manyan alamomin ...
08/02/2026

’YAN UWANA MU KIYAYE SALLAR ASUBA A CIKIN JAM’I.

Sabida tana da tarin falala sosai, kuma tana daga cikin manyan alamomin gaskiyar imani. Sallar Asuba a jam’i tana nuna tsoron Allah da cikakken biyayya gare Shi, domin a lokacin da mutane da dama suke barci, bawan Allah yana tashi ya bar jin daɗinsa domin bauta wa Ubangijinsa.

Manzon Allah ( S.A.W ) ya yi bushara da cikakken haske a ranar Alƙiyama ga masu tsayawa kan Sallar Asuba da Isha’i a cikin jam’i. Mala’iku suna halartar wannan salla, suna rubuta lada mai yawa, suna kuma yi wa mai sallar addu’a. Duk wanda ya kiyaye ta, Allah Zai tsare shi a cikin yini, Ya kuma sanya albarka da natsuwa a rayuwarsa.

Sallar Asuba a jam’i tana buɗe ƙofar alheri, tana gyara rayuwa, tana kuma sanya haske a zuciya. Wanda ya fara ranarsa da Allah, Allah Zai sa alheri ya biyo bayansa.

Allah Ya ba mu ikon kiyaye Sallar Asuba a cikin jam’i har ƙarshen rayuwarmu.

*02 Sha'aban, 1447 (Eqv. to January 21, 2026).**Assalamu Alaikum,**Have YOU Read the Glorious Qur'an today?*If No, then ...
21/01/2026

*02 Sha'aban, 1447 (Eqv. to January 21, 2026).*

*Assalamu Alaikum,*
*Have YOU Read the Glorious Qur'an today?*

If No, then spare 2 MINUTES from the 1,440 minutes you have in a day and *READ JUST ONE PAGE*. You will have multiple blessings In shaa Allah.

*Surah No. 007 Al - A'araf (The Elevators) 121 - 130*

DAREN FARKO A CIKIN KABARI... LOKACIN DA KOWA YA TAFI YA BAR KA 💔Dan uwa, ka taba zama kai kadai a cikin daki mai duhu, ...
18/01/2026

DAREN FARKO A CIKIN KABARI... LOKACIN DA KOWA YA TAFI YA BAR KA 💔

Dan uwa, ka taba zama kai kadai a cikin daki mai duhu, babu wuta, babu waya, babu kowa? Kana jin tsoro ko?

To ka yi tunanin Daren Farko a Barzahu.
Lokacin da 'Yan uwanka da Abokanka s**a gama zuba maka kasa.
S**a yi maka addu'a.
S**a juya s**a tafi.
Za ka dinga jin takun takalmansu suna raguwa... Tap... tap... tap... har sai shiru ya dauke.

A NAN NE ZA KA GANE AINIHIN MA'ANAR "KADAICI".

Gidan da babu 'AC' ko fanka.
Gidan da babu 'Network' ko 'Data'.
Gidan da babu aboki sai Aikin ka.

Idan aikinka nagari ne, zai zo maka a siffar aboki mai kyau ya debe maka kewa.
Amma idan aikinka na banza ne... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Zai zama abokin kuka da azaba har zuwa tashin Kiyama.

A wannan lokacin, za ka yi ihu: "Rabbir ji'un" (Ya Allah ka mayar da ni duniya in yi Sallah daya)... Amma amsar ita ce: A'A.

Dan uwa, yau kana saman kasa, gobe kana ciki.
Gadon da kake kai yau mai laushi, gobe kasa ce matashinka.

Ka gyara Sallarka. Ka gyara Zumuncinka. Ka daina Zalunci.

Domin Barzahu bata karbar "Transfer", sai dai abin da ka tura da kanka tun yanzu.

Ya Allah Ka sa Kalmar Shahada ta zama abin fadinmu na karshe.
_________________
Karatun Sallah (PDF) 👇

https://haskenmusuluncii.blogspot.com/2025/11/sallah.html?m=1

Benefits of Ayatul Kursi:1. One who recites Ayatul Kursi every morning will be in the protection, safety of Allah until ...
17/01/2026

Benefits of Ayatul Kursi:

1. One who recites Ayatul Kursi every morning will be in the protection, safety of Allah until the night.

2. "Whoever recites Ayatul Kursi immediately after every prescribed prayer (Fardh Salah), there will be nothing standing between him and his entering paradise except death." [Sahih Al-Jami: 6464]

3. Recitation of Ayatul Kursi on behalf of those who have passed away gives light(noor) in their graves.

4. Learn Ayatul Kursi so that you can say it before leaving your home. Recite it once before leaving, the Almighty will send a group of angels to protect you. Reciting it two times, two groups of angels are sent down. Say it a total of 3 times, no angels will come down because Allah himself will take care of you.

5. Saying this Ayat to one's wealth or to his children, they will be protected from the Shaytan.

6. When one is alone in the house, recitation of Ayatul Kursi and asking Allah for help will make you remain calm and you will not fear.

7. If one recites Ayatul Kursi before going to sleep, Allah will send an Angel to come and look after youband protect.

•Recite while leaving your house, and 70,000 angels will protect you from all sides.

•Recite on entering your home, and poverty won't enter your home.

•Recite after wuzu, and it raises you 70 times in Allah's rank.

12/01/2026

Babban kuskure ne ka kira wani da sarkin sarakuna domin Allah ne kadai Sarkin Sarauta.

29/12/2025

Ga jerin Addu'o'i masu tasirin gaske

1. HasbunAllahu
wa ni'imal wakeel.

2. Astagfirullah wa atubu ilaih.

3. Laa'ilaha illallah.

4. Subhanallah.

5. Alhamdulillah
6. Allahu Akhbar.

7. Laailaha illa Anta subhanaka inni kuntu minazzalimin.

8. Allahumma inni As'aluka Jannah wa a'uzubika minnan nar

9. Allahumma Atiƙ riƙabana minan narr.

10. Subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil Azeem.

11. Rabbi inni Lima anzalta ilayya min Khairin faƙir.

12. Ya muƙallibal ƙuluub thabbit ƙalbee ala deenika.

13. Rabbi a'inni ala zikrika wa shukhrika wa husni ibadatik.

14. Rabbana atinaa fiddunya hasanatan wa fil akhirati hasanatan wa ƙinaa azabannar.

15. Rabbana hablana min azwajina wa zurriyatina ƙurrata a'ayunin wa ja'alna lil muttaƙiyna imaama.

16. Rabbi gifirliy, waliwalidayya, warhamhuma k**a rabbayani sagiyra.

17. Lahaula wala ƙuwwata illa billah.

18. Allahumma innaka afuwun tuhibbul afuwa fa'afu anniy.

19. Rabbi tawaffaniy musliman wa alhiƙniy bissalihiyn.

20. Rabbana taƙabbal minna innaka antas Samee'ul Aleem.

SHIN KO KASAN LOKACIN DA RAN MUTUM ZAI FITA AKWA WASU MALA'IKU BIYAR DA SUKE ZUWA MASAMala'ka na farko Yana zuwane lokac...
28/12/2025

SHIN KO KASAN LOKACIN DA RAN MUTUM ZAI FITA AKWA WASU MALA'IKU BIYAR DA SUKE ZUWA MASA

Mala'ka na farko Yana zuwane lokacin da ran Dan Adam zai fita sai yace Masa inane jikinka Mai daraja zai tafi Kuma meyasa kake tawali'u da zaran eai yarigada ya fita

Sai mala'ika na biyu yazo yace Ina dukiyarka da Abinda ka tara

Idan Aka kammala zana'idarsa Kuma mala'ika na uku zaizo yace yaune zakai wata doguwar tafiya wacce baka tabayin irinta ba A rayuwarka zaka sauka a wani gida Mai kankanta da kuntatawa wanda bakada wajen motsawa

A yayinda ake sanyashi A cikin kabari Kuma mala'ika na hudu zazo yace kafin yau ka zauna A duniya kayi dariya Amma yau Kai kadaine Anan

Idan Aka gama zuba kasa a kabarinsa Kuma mala'ika na biyar zaizo yace yau koka Sami Albishir da Aljanna ko kuma Azabar wuta,

Allah ya tsaremu daga Azabar wuta dana kabari.

📜 LOKACIN DA JIBRILU YA TOSHE BAKIN FIR'AUNA A ƘARSHEN RAYUWARSA 🪨 Labarin Fir’auna da Annabi Musa (AS) koyaushe yana ɗa...
04/12/2025

📜 LOKACIN DA JIBRILU YA TOSHE BAKIN FIR'AUNA A ƘARSHEN RAYUWARSA 🪨


Labarin Fir’auna da Annabi Musa (AS) koyaushe yana ɗaya daga cikin labarai mafi girma a tarihin Annabawa. An san Fir’auna a matsayin azzalumin mai mulki, wanda ya yi iƙirarin cewa shi Ubangiji ne, kuma ya ci gaba da ƙin koyarwar Annabi Musa (AS).

Amma shin kun san… a ƙarshen rayuwarsa, Fir’auna ya amince cewa Allah ne kaɗai Ubangiji? To, me ya sa Mala’ika Jibrilu ya toshe bakinsa da laka?

Lokacin da Fir’auna da sojojinsa s**a biyo Annabi Musa (AS) da Bani Isra’ila, Allah (SWT) Ya raba teku kuma Ya yi musu hanya.

Da farko Fir’auna ya yi jinkirin shiga, amma Mala’ika Jibrilu, wanda ya canza k**a, ya tursasa dokin Fir’auna ya ci gaba da shiga.

Bayan dukkan sojojin sun shiga tsakiyar teku, ruwan ya sake rufewa… kuma a nan ne Fir’auna ya fara nutsewa.

A wannan lokacin na mutuwa, a ƙarshe Fir’auna ya ce:

“Na yi imani cewa babu wani abin bautawa sai Ubangijin da Bani Isra’ila s**a yi imani da shi.” (Surah Yunus: 90)

Lokacin da mutum ya riga ya kai ga bakin mutuwa kuma ya ga azaba a gabansa, ƙofar tuba ta riga ta rufe. Wannan shi ne abin da ya faru da Fir’auna—nadama ce da ta zo a makare.

A Wata Ruwaya Mai Ban Sha’awa
A cikin wani Hadisi da Tirmizi ya ruwaito, Mala’ika Jibrilu ya ce ya ɗauki laka (ko yumɓu) daga teku ya saka shi a bakin Fir’auna.

Me ya sa?

Domin Jibrilu yana jin tsoron kar Fir’auna ya faɗi kalmar shahada (kalmar Tauhidi) kuma ya nemi rahamar Allah—alhali a tsawon rayuwarsa, ya:

Zalunci Bani Isra’ila,

Ƙin karɓar Ayoyin Allah,

Yin iƙirarin cewa shi Ubangiji ne,

Kuma ya yaƙi da’awar Annabi Musa (AS).

Girman kansa ya rufe zuciyarsa har zuwa ƙarshe.

Mai Muhimmanci:

Labarin Fir’auna yana tunatar da mu cewa:

– Kada ka taɓa jinkirta tuba.

– Kada ka bar zuciyarka ta taurare da girman kai.

– Kada ka jira azaba ta zo sannan ka amince da gaskiya.

Muna fatan Allah Ya kiyaye zukatunmu su kasance masu taushin hali don karɓar gaskiya.

Allahumma salli ’ala Sayyidina Muhammad wa ’ala aalihi wa sahbihi ajma’in.

---

Allah shi ne mafi sani akan komai da kowa!.

Ya Allah, ka yafe mana zunubanmu, ka karɓi ayyukamu na alheri🤲

.✍️

Address

Fufore

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hasken Musulunci posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share