Sadeeq Abdullahi Boda

Sadeeq Abdullahi Boda Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sadeeq Abdullahi Boda, Shopping & retail, No 4 Layin Yan Bokolo Jabiri Funtua, Funtua.

02/11/2025
Ƙarƙashin Jagoranchin Jagoran Haɗin kai Maulana Imam Prof. Ibrahim Maqari
13/05/2025

Ƙarƙashin Jagoranchin Jagoran Haɗin kai Maulana Imam Prof. Ibrahim Maqari

16/01/2024

Alhamdulillahi for the gift of life

Koyi da Maulana Prof. Ibrahim Maqary 001Wata rana wata mata wacce mukayi sanadin haɗuwa da ita anan facebook ɗin.Mun sab...
26/01/2023

Koyi da Maulana Prof. Ibrahim Maqary 001

Wata rana wata mata wacce mukayi sanadin haɗuwa da ita anan facebook ɗin.

Mun saba da juna sosai amma babba ce dan ta kusa haihuwata.

Sai take bani labarin cewa tana da ƙawa amma ƙawar tana buƙatar taimako domin da ƙawar taɗin ba musulma bace, sai ta haɗu da wani soja musulmi ya aure ta ya kuma musuluntar da ita, bayan sun kai shekaru 20 da aure, sai Allah yayi ma sojan rasuwa a Maiduguri sanadin yaƙi bayan ya rasu to dama ƙawar tata ɗin ita kaɗai ce musulma a gidan kuma sanadin mijin nata ne ta musulunta ta watsar da danginta gaba ɗaya ta zaɓi musulunci da mijin nata.

Bayan tsawon lokacin da s**a ƙwashe a tare gashi kuma ta saba da musulunci ta haifi ƴaƴa kusan biyar a cikin musulunci kuma duk musulmai ga kuma miji ya rasu sai ta dawo gida inda danginta suke s**aƙi amsarta s**a watsar da ita to da yake aƙwai wani abu da ake bayarwa na kuɗin makarantar yara sai take amfani dashi har ya ƙare amma ko wata uku bayayi mata a cikin watanni sha biyu kuma duk shekara ake badawa, sai baiwar Allahn nan ta kasa haƙuri ta koma gurin ƴan uwanta sai s**a amsheta amma da sharaɗin zata koma Kiristancinta, sai kuwa ta amince saboda tsananin wahalar da take sha kota fara sana'a bata ɗorewa ga kuɗin makarantar yara ga abinci ga haya da sauran matsalolin rayuwa.

Bayan ta shafe lokaci a cikin Kiristancin sai taji gaskiya bazata iya zama ba, sai ta zaɓi ta fita kiristancin to amma babu mai taimakonta kota koma musulunci domin ta nemi ƙungiyoyi da dama an haɗata da limamai da sauran ƙungiyoyi na addini shuru sun ƙyaleta shi yasa ma ta koma kiristancin da musulmai sun kawo mata ɗauki da bazata koma kiristancin ba.

Sai wannan matar dana haɗu da ita anan facebook ta nemi na haɗata da Prof. Ibrahim Maqary, ya musuluntar da ita kuma ya taimaketa, bayan mun gama magana sai na samu wani bawan Allah ya bata dubu goma ta hau mota daga Sokoto zuwa Abuja bayan ta sauka kuɗi ya ƙare muka samu wasu kuɗi na zirga zirga da abinci muka ƙara tura mata taje gurin Prof. sai a zuwa na biyu s**a haɗu bayan sun haɗu dashi sai ta karanta mishi matsalarta dama nima nayi masa bayani.

Matsalolinta uku ne

1. Tanason ta koma Musulunci.
2. Tana neman taimakon kuɗin da zata biya ma babban ɗanta registration na Poly a Sokoto ya samu admission
3. Kuɗin da zata riƙe a hannu ta riƙa kashewa da abinci da biyan kuɗin makarantar sauran yara da sauran abubuwa.
4. A aurar da ita.

Bayan Maulana yaji matsalolinta, sai yace ta kawo takardun yaron ya sanya shi a Private University, Abuja. Ba kuɗin registration ɗin Poly zai bata ba University ta kuɗi zai sanya shi fa yace.

Ya kuma ce zai musuluntar da ita zai mata aure kuma zai bata abinda zata riƙe a hannunta.

Kaɗan daga cikin abubuwan da Maulana yakeyi kenan fa dan ni kaina na kai mutane sunfi biyar da kusan irin wannan matsalolin

Dalilin wannan dogon rubutun shine:

Yanzu da ace munada irin wannan gidauniyar da muke ƙoƙarin assasawa a yanzu da bazamu tura irin wannan matar gurin Maulana ɗin ba, da sauran makamantan irinsu dama ƴan ƙananun abubuwa waɗanda bazamu iya ba sai a ƙungiyance sannan kuma tunatawar ne akan duk mai cewa yanason Maulana to ba a baki zai bar abin ba a aikace zaiyi domin shima idan ya faɗa yana aikatawa ne ba yana jiran sai ya samu ba, ni nasan lokacin da Maulana sai dai yayi alƙawari ya jira sai kuɗi sunzo sannan yayi wallahi sau da yawa zaiyi ma mutanen dake neman taimako alƙawari kuma bashi da kuɗi a lokacin da kuɗi sun shiga kuma zai cika alƙawarin abubuwa sunyi masa yawa ne matuƙa.

Mu daure mu assasa wata gidauniya da sunan koyan sunnarsa domin faranta ma mabuƙata kamar yadda yanzu haka muka fara kuma da izininsa.

Muna da kuɗi Naira 6000 a account ɗinmu kuma zamu buɗe account na gidauniyar tamu da zarar komai ya lafa na sha'anin canjin kuɗin nan da akeyi.

Zaka iya saka naka tallafin a 👇

3101004274
First Bank
Anas Usman

Allah yasa mu dace ya ƙarama Maulana lafiya ya kuma bamu ikon yin koyi dashi da ƙyaƙƙyawar niyyah

Haƙiƙa dukkan mu ɗin nan muna sane da irin ƙoƙarin da Prof. Ibrahim Maqary yakeyi akan Marayu da mabuƙata waɗanda wasuns...
25/01/2023

Haƙiƙa dukkan mu ɗin nan muna sane da irin ƙoƙarin da Prof. Ibrahim Maqary yakeyi akan Marayu da mabuƙata waɗanda wasunsu sun bayyana a garemu, wasu kuma basu bayyana ba, dan abubuwan da basu bayyana a gare muba waɗanda yakeyi sunfi yawa.

Bayan dogon nazari tare da nazari akan haka munason mu sanar da ƴan uwa burin mu na assasa wani abu koya yake na musamman wanda muma zamu motsa koda kaɗan ne ba a baki ba, idan har mukace sai mun samu dama zamuyi to bazamu iyaba domin Maulana Prof. yana yawan cewa

" Mutum zai riƙa cewa ina Allah ya yarda gobe zan fara, in Allah ya yarda jibi zan fara, in Allah ya yarda sati mai zuwa zan fara to kaga gobe da jibi ɗin nan baka da maƙiya kamarsu, kawai kayi ƙoƙari rayuwarka ta zama yanzu, wajibi ne abu kaza to sai ka fara kawai BismilLah".

Bayan haka munayi muku wannan bayanin da zuciya ɗaya da kuma amincewar su Maulana akan mu assasa duk wani abu wanda zamu faranta ma ƴan uwa mabuƙata rai koda a cikinmu suke, domin kuwa ko mun haɗa zamu iya duba duk wanda ya cancanta ya miƙo ƙoƙon bararsa zamu tantance mu tabbatar domin zamu naɗa wakilai suje har inda yake ya tabbatar mana da matsalar tashi sai musan abinda zamu iyayi akanta amma bazamu jira ba sai an samu matsalar sannan mu haɗa a'a ƙofa buɗe take akoda yaushe zaka iya saka duk abinda kake da niyyar badawa komai ƙanƙantarsa ko nawa ne domin babu wani abu kaɗan matuƙar kaɗan ɗin ya haɗu zai zama mai yawa wata rana.

Muna sanar da ƴan uwa dan girman Allah a ɗauki wannan abun da muhimmanci tabbas zai faranta ran Maulana Prof. Ibrahim Maqary matuƙa da gaske.
Kuma duk abinda mukayi za'a sanar dashi nan take kuma zai riƙa bibiyarmu kuma zai ƙara mana ƙarfi koda bamu kai inda mukeso ba.

Kusan kullum zamu riƙa posting ɗin abubuwan da Maulana ɗin yayi kuma yake kanyi badan komai ba sai dan ƙarama kanmu ƙaimi muma akan wannan muhimmin al'amarin.

Dan girman Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam a ɗauki wannan abin da muhimmanci indai mun tabbata munason Maulana to wannan itace aƙidarsa a aikace kuma muyi sharing ya shiga lungu da saƙo dako ina na wannan sahar zamuyi amfani da groups ɗinmu na Darut Tazkiya na Whataspp dama sauran guraren da muke tunanin isarsa kuma muna maraba da shawara ko wani ƙarin bayani kuma duk wanda yake da wani mutum mai wata matsalar tun yanzu ƙofa buɗe take ya sanar damu kuma mutumin ba dole sai musulmi ba ko Ɗan Tijjaniyya ko waye kuma ko meye aƙidarsa muna maraba zamu taimaka masa.

Bamu bawa kowa ikon canza wannan rubutun ba ko details ɗin da muka bada idan mukaga haka zamu ɗauki mataki na musamman.

Sannan wannan account number ɗin za'a cire shi daga baya saboda zamuje banki mu buɗe na musamman yanzu ma abinda ya hanamu saboda hadadar canjin kuɗin nan amma da an kammala zamu buɗe In sha'a Allah.

3101004274
First Bank
Anas Usman

Za kuma a iya tuntuɓar waɗannan bayin Allahn

Mujtaba Muhammad Sani
Mai kula da makarantar Maulana ta Marajal Bahrain Zaria.
08087232812
Muhammad Usman Gashua
0806 991 7239
Othman Muhammad
0806 042 6647
Imam Anas
08060755821

Allah yasa mu dace, ya tsarkake mana niyyar mu ya bamu ikon yi dominsa.

Address

No 4 Layin Yan Bokolo Jabiri Funtua
Funtua

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sadeeq Abdullahi Boda posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sadeeq Abdullahi Boda:

Share