Formula 9 formula 8

Formula 9 formula 8 Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Formula 9 formula 8, Shopping & retail, Jani house Funtua jihar katsina, Funtua.

Kammun baka,da hassada,da kishi,da yadda suke cutar da ɗan adam.👁️👀Sihirin idanuwa, da hasada – tasirinsu ga lafiyar ɗan...
21/08/2026

Kammun baka,da hassada,da kishi,da yadda suke cutar da ɗan adam.👁️👀

Sihirin idanuwa, da hasada – tasirinsu ga lafiyar ɗan Adam,da yadda suke kawo wasu matsalolin ga lafiyar ɗan Adam,da maganinsu bisa hanyar Alqur'ani)

🌿 1. Ma’anar “al-‘Ayn” (idon mai hasada)

Sheikh Usāmah ya fara da cewa “al-‘Ayn” ita ce idanun da ke kallon wani abu tare da sha’awa da kishi, sai a sami wannan abun,ko ɗan Adam,yasamu cuta ko tabarbarewar al'amuran sa ta hanyar aljani.

Annabi ﷺ ya ce:

> "العين حق، ولو كان شيء سابق القدر لسبقته العين."
(Muslim)

“Ido mai hasada gaskiya ne — da akwai abu da zai rigaya ƙaddara, da idone zai ya rigaya.”

Wato hasada tana da ƙarfi amma tana aiki ne da izinin Allah.

💠 2. Ma’anar “Hasad” (kishin kai da ƙiyayya)

Hasada ita ce so da fushi idan ka ga wani ɗan Adam,ko wani abu yana tare da ni’imar Allah, kuma kana fatan ta gushe daga gare shi.

Allah Ya ce:

> "ومن شر حاسدٍ إذا حسد"
(Suratul Falaq: 5)

Ma’ana: “Kuma daga sharrin mai kishi idan ya yi hasada.”

⚠️ 3. Bambanci tsakanin “kammun baka da “Hasada”

Ido kammun baka (Ain) Hasada (Hasad)

Yana iya zuwa daga mai sonka Yana kuma kasance wa yafito daga mai ƙiyayya agareka.👀👁️

Sau da yawa a wasu lokutan,ba da niyyar cutar dakai bane,ko Da niyyar lalata al'amuran ka ko gushewar wata ni’ima daga gareka.

Aiki ne na aljani ko tasirin ido(Kammun baka) Aiki ne na zuciya mai ɓacin raine.

Amma Ana ganin sak**akon nan da nan Sau da yawa irin wannan cutarwa din na kammun baka,da hasada yana zuwa a hankali,a hankali ne ga ɗan Adam idan yataru shine yake zama matsala ga ɗan Adam 👁️👀

🧠 4. Alamomin wanda aka samu mutum dasu,to yakamu da ciwan kammun baka, ko hasada

1. Jin kasala, ciwon kai, ko rashin kuzari.

2. Zazzabi ko jin zafi a jiki ba tare da dalili ba.

3. Rashin bacci ko mafarki mai rikitarwa.

4. Jin haushi ko tsoro daga mutane ba tare da dalili ba.

5. Rashin cigaba a aiki, ilimi, ko aure.

6. Wani lokaci kaya ko kasuwanci suna lalacewa ba tare da dalili ba.

🕋 5. Hanyoyin warkarwa da ruqyah

1️⃣ Tuba da komawa ga Allah

Domin Allah ne kawai mai warkarwa.
A yawaita istighfar, salati ga Annabi ﷺ, da tawakkali.

2️⃣ Ruqyah ta Qur’ani

A karanta:

Suratul Fātiḥa

Suratul Falaq

Suratun Nās

Ayatul Kursiy

Suratul Baqarah (cikakke ko sassan farko)

Suratul Qalam (51)

> “Wa-in yakādu alladhīna kafarū layuzliqūnaka bi-abṣārihim…”

3️⃣ Ruqyah da ruwan wanka

A karanta ayoyin ruqyah cikin ruwa, a sha kadan, sannan a yi wanka.
Ana yin hakan tsawon kwana 3–7.

4️⃣ Ruqyah da ruwan wanda ya yi hasada (idan an sani)

Annabi ﷺ ya umarci wanda ya yi hasada da ya wanke jikinsa, sannan wanda matsalar tasama a zuba masa wannan ruwa — domin ya warke.

> “Wal-‘aynu haqqun, walau istaġsiltum faghisilu.”
(Bukhari)

“Idon mai hasada gaskiya ne, idan aka ce ku wanke jikin ku,don wanda aka shafa, to ku yi.”

5️⃣ Yin Addu’ar kariya

> “A‘ūdhu bi kalimātillāhi tāmāti min kulli shayṭānin wa hāmmatin wa min kulli ‘aynin lāmmatin.”

Ina neman tsari da cikakkun kalmomin Allah daga dukkan shaiɗanu da idon da ke cutarwa.

🌙 6. Hanyoyin kariya kafin a kamu da hasada

1. Yin Bismillah idan ana yaba wani abu.

> “Allahumma barik – Ya Allah Ka albarkace.”

2. Gujewa yawan bayyanar ni’imar kai ga mutane masu kishi.

3. Yin addu’ar safe da yamma akai-akai.

4. Karatun Suratul Ikhlās, Falaq da Nās a kowace rana.

5. Tsarkake zuciya daga ƙiyayya da kishi,ko hasada ga wasu.

💎 7. Kammalawa

Sheikh Usāmah ya kammala babin da cewa:

> “Idan mutum ya dogara da Allah, ya yawaita zikri, ya tsarkake zuciyarsa daga hasada, to babu ido da zai iya cutar da shi.”

> “وَإِن يَكَادُ الَّذِينَ كَفَرُوا لَيُزْلِقُونَكَ بِأَبْصَارِهِمْ… وَمَا هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَالَمِينَ.”
(Al-Qalam: 51–52)

Wato: Idan s**a yi kallo da ƙiyayya, ba za su iya cutar da kai ba, domin Qur’ani kariya ne ga kowa.

idan kana bukatar magana kai tsaye kayi amfani da wannan lambobin 08029665783/08152753609

Ko kaziyar ci shafiu na website akan https://algerianchemist.com.ng don saukaka muammala damu ko samun maganin zaku ga inda aka rubuta neman shawara ko Yi order zai kai ka kai tsaye wajen da zaka cike Form

Masu amfani dashi shafin TikTok akwai wasu muhimman shawarwarin namu a shafin https://tiktok.com/

Ko wannan shafi namu akan link blog.algerianchemist.comn.ng

17/08/2026

Daga cikin abubuwan da za mu koya a cikin wannan horo na mafarkai da ru'yoyi da kuma dangantakarsu da al'amuran gaibi (duniya ta daban).

Bambancewa tsakanin mafarkin Qarin (shaidanin da ke tare da mutum) da kuma mafarkin Aljanu na waje (Aljanin da ya shiga jikin mutum).

Ga cikakken bayani kan bambancin da ke tsakanin mafarkin Qarin (wanda ke ciki) da kuma mafarkin Aljanu na waje (shafawa, maita/sihiri, ko ciwon ido/hasada) domin inganta bincike da fahimtar yanayin kowace ru'ya:

Na Farko: Mafarkin Qarin (Shaitanin jiki na ciki)

Yanayin Ayyuka da Abinda ke ciki:
Mafi yawancin al'amuransa suna kewaye ne da rikice-rikice na nafsani (na zuciya), waswasi, sha'awoyi, tsoro na ciki, ko kuma shakku da ke taruwa a cikin kirjin mutum.

Dangantaka da Yanayin Imani:
Yana karuwa ko raguwa dangane da yanayin mai mafarkin; yana tsananta har ya hana nutsuwa idan mutum ya shagala daga da'a ko ya dukufa a laifuka, sannan yana saukawa ya saitu idan mutum ya gyara halayensa ya kuma kiyaye ambaton Allah (azkar).

Alamomin da s**a fi fice:
Ganin kai a cikin yanayi na rauni na 'dan adam, ko 'bata, ko gudun wasu mutane da ba a sani ba (wadanda ke wakiltar zuciya mai umarni da mummuna), ko shagaltuwa da tunani da waswasi masu rikitarwa.

*LTabbatar Ayyukansa a Filaye: Yana barin yanayi na damuwa ta gaba daya, ko waswasin tunani, ko kosawa da sakaci wajen gudanar da ibadu.

Hanyar Magancewa da Warwarewa: Mafi yawanci yana tafiya ne ta hanyar yi wa kai hisabi, yawaita neman gafara (istigfari) da ambaton Allah, da kuma kiyaye tsaurara addu'o'i da ibadu.

Na Biyu: Mafarkin Aljanu na Waje (Shafawa / Sihiri / Ciwon Ido)

Yanayin Ayyuka da Abinda ke ciki: Yana kewaye ne da hare-hare, biye-biye (bincike/kora), barazana a fili, yunkurin cutarwa ta jiki kai tsaye, ko ganin kalaman sirri (rokomi/laya), kullaye, da alamomin da ke nuni da cutarwa ta waje.

Yanayin Zuwan Mafarkin:
Mafi yawanci yana zuwa ne a matsayin hare-hare na ba-zata ko mafarkai masu ban tsoro masu biyo bayan juna, ba tare da la'akari da yanayin zuciyar mai mafarkin ba wani lokacin.

Alamomin da s**a fi fice:
Ganin wasu dabbobi na musamman suna yi masa fakoto da nufin cutarwa (k**ar macizai da karnuka 'dawa), ko ganin wurare masu duhu, kufai, kaburbura, ko kuma k**a shi da 'daure shi a mafarki.

Tabbatar Ayyukansa a Filaye: Yana tattare da tangarda ko tsaiko a fili a al'amuran rayuwa (k**ar samun arziqi, aure, ko lafiya), ciwon jiki a wurare daban-daban, da kuma gudun ambaton Allah, karanta Alqur'ani, ko sauraron Rukiyya.

Idan kuna bukatar ƙarin bayani shawara ko samun bayani akan wasu magungunan masu inganci da aka jarraba zaku iya ziyartar wannan shafi namu kai tsaye in sha Allah
👇
https://algerianchemist.com.ng

Addinin Aljanu da Nau'o'insu bisa ga Hakan dangane da Alqur'ani 📖✨Daga cikin aljanu akwai waɗanda wa'azi ke amfanar dasu...
18/01/2026

Addinin Aljanu da Nau'o'insu bisa ga Hakan dangane da Alqur'ani 📖✨

Daga cikin aljanu akwai waɗanda wa'azi ke amfanar dasu👺

Amma ba kiran addini ba. Kuma daga cikinsu akwai waɗanda Allah ke faɗaɗa kirjinsu ga addinin Musulunci 🕌,

kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke kafirta saboda jahilci ko yaudarar wasu gare su.

Kamar yadda ayoyin Suratul Jinn s**a ambata kuma, Allah Madaukakin Sarki ya ce: ﴿Kuma shi ne (shaidanmu) cewa wasu shashasu acikinmu ,kuma wawaye suna faɗin ƙarya mai nisa a kan Allah. وانه كان يقول سفيهنا علي الله شططا

Hakika Kuma munyi zato cewa mutane da aljanu ba za su faɗi ƙarya a kan Allah ba.﴾ (Suratul Jinn, Aya ta 4, 5).(وانا ظننا ان لن تقول الانس والجن على الله كذباً

**Imam Ash-Shawkani** ya ce: Aljanu suna musanta da karyata kalaman mushrikai daga cikin su da jahilansu na jingina ƙarya ga Allah game da ikirarin cewa Allah yana da mata ko ɗa da mak**antan haka.)(SUBHANALLAH)👻

Kuma 'Ash-Shaṭaṭ' na nufin wuce gona da iri a cikin kafirci, da nisantar manufa, da wuce iyaka,da wuce gona da iri.😈

Kuma ya kuma ce game da aya ta biyu: "Mun yi zaton cewa mutane da aljanu ba za su yi wa Allah ƙarya ba sa'ad da s**a ce Allah yana da abokin tarayya (shirka)ko mata, ko ɗa.

Don haka muka gaskata su a cikin hakan, kuma bai taɓa zuwa zukatanmu ba cewa wani zai iya yin ƙarya ga Allah k**ar yadda masu kiran shirka da Allah da masu bautar gumaka na ƙarya s**a yi.👶

Har sai da muka ji Al-Ƙur'ani 👂, sai muka gane cewa kalaman nasu ba su da tushe, kuma abin da muka yi zaton gaskiya ne daga gare su ya zama ƙarya."

Saboda haka, daga cikin aljanu akwai waɗanda suke kafirta saboda bin wani, ko kuma wani ya ɓatar da su, k**ar yadda ayoyin s**a bayyana. Kuma daga cikinsu akwai waɗanda s**a kafirta da gangan kuma s**a yarda da kafirci k**ar Iblis da rundunarsa 😈, wa'azi baya masu amfani kuma kalma ɗaya ba ta masu amfani.

"Wallahi, na haɗu da wani mugun mutum daga cikinsu, wani maye la'ananne ya mallake shi a kan ɗaya daga cikin 'yan uwa 🧙‍♂️.

👶 Kuma wannan la'annanne yana gaya mana cewa shi ɗaya ne daga cikin kusoshin 'ya'yan Iblis.🫥

Kuma yana cewa ya sani cewa Allah gaskiya ne 🙏, kuma Muhammad gaskiya ne ﷺ, kuma ya san girman Allah da tsananin riƙonsa.

Duk da haka, yana cewa, "Duk da cewa na san game da Allah abin da ba ku sani ba, amma ni ba..."

Sai aka ce masa: "Wanene kai?" Sai ya ce da cikakken kafirine yana daga cikin ya'yan IBLIS nakusa dashi,kuma bazai taɓa yima Allah sujuda ba tunda babansu yakiyi shima:Yace "Ni ɗaya ne daga cikin waɗanda ba sa girmama Allah." 😤

Yana nuni zuwa ga faɗin Allah Madaukakin Sarki: ﴿Me ya sa ba ku girmama Allah ba?﴾ (Nuhu: 13)مالكم لاترجون لله وقارا Kuma ya kasance mai mugunta, mara kyau.🫥

👺 Kuma kaɗan ne daga cikinsu ke imani, amma mafi yawan waɗanda s**a yi imani suna daga zuriyar Āt. Kuma Allah ne mafi sani. 💡

Dukkan masu bukatar maganin akan Shafar jinnu daban-daban ko SIHIR ko jifa ko sammu ko wasu magungunan dabn zaku iya tuntubar a 08152753609/08029665783

Ilimin Dabi'ar ɗan Adam da kuma rayuwa🙂(Psychology)🛡️ Ka’idoji guda 10 Don Ɗaukaka Kima da Darajar Kai 🛡️1️⃣ Duk wanda y...
17/01/2026

Ilimin Dabi'ar ɗan Adam da kuma rayuwa🙂(Psychology)

🛡️ Ka’idoji guda 10 Don Ɗaukaka Kima da Darajar Kai 🛡️

1️⃣ Duk wanda ya daɗe baya nan, yana zama baƙo a zuciya.

2️⃣ Ka zauna kai kaɗai idan ya zama dole, domin babu abin da ya dace ka riƙa bibitar-mutane.

3️⃣ Nisanta wajibi ne idan kana tare da wanda yake ganin kansa ya fi ka daraja.

4️⃣ Duk wanda yake tunanin rasa ka, ka taimaka masa ya cimma hakan.

5️⃣ Ka kasance mai dogaro da kanka koyaushe; kada ka tambayi dalilin ɓacewa, kuma kada ka yi kuka kan jinkirin amsa. Kowa yana mu’amala da kai ne gwargwadon yadda yake jinka a zuciyarsa.

6️⃣ Yi nasiha sau biyu, amma a karo na uku—ka bar shi a hannun Allah.

7️⃣ Mutunci jan layi ne 🚫, a kansa ne abota dubu da soyayya ke ƙarewa.

8️⃣ Kulawarka ga wanda bai damu da kai ba, raini ne ga kanka.

9️⃣ Wanda ya nisance ka da son ransa, ka nisance shi da cikakken nufinka; kada ka taɓa nuna masa kana son ya zauna—even idan zuciyarka tana yagewa saboda kaunarsa.

🔟 🤲 Ya Allah, duk wanda ya karanta wannan, Ka wadatar da duk mai damuwa daga abin da yake damunsa, kuma kada Ka tilasta masa neman taimakon wani halitta—cikin gaggawa. Amin. ✨

🧿 ADDINAN ALJANU DA IRE-IREN SU 📘 BABI NA HUƊU  LIILAJI   WALMASI SHAIDAN.🧿 Addinan Aljanu da Ire-irensu🕌 Ka sani, ya ka...
17/01/2026

🧿 ADDINAN ALJANU DA IRE-IREN SU

📘 BABI NA HUƊU

LIILAJI WALMASI SHAIDAN.

🧿 Addinan Aljanu da Ire-irensu

🕌 Ka sani, ya kai ɗan’uwa Musulmi, cewa aljanu suna da addinai mabanbanta, k**ar yadda mutane ma suke da addinai daban-daban.

👉 A cikinsu akwai:

❌ Kafirai gaba ɗaya

✡️ Yahudawa

✝️ Kiristoci (Nasara)

☪️ Musulmi, daga cikinsu:

😔 Musulmi masu fasikanci

🌟 Musulmi masu tsoron Allah (muttaqiun)

🤝 Akwai Sahabbai daga cikin Aljanu

📜 A cikin aljanu, akwai sahabbai, k**ar yadda aka samu sahabbai daga cikin mutane.

Wannan abu sananne ne ga malamai, kuma akwai ijma’i (yarjejeniya) a kansa.

📚 Imam Ibn Hajar (رحمه الله) ya ambaci haka a cikin littafinsa Al-Isābah fī Tamyīz aṣ-Ṣaḥābah cewa akwai wani babi da ya keɓe sahabban aljanu daga cikin sahabban Annabi ﷺ.

📖 Hujja daga Al-Kur’ani

Allah Maɗaukakin Sarki Ya faɗa mana a Suratul Jinn cewa aljanu suna cewa:

“Bayan haka Kuma a cikinmu akwai masu adalci, kuma a cikinmu akwai waɗanda ba haka ba; mun kasance da hanyoyi mabanbanta.”
📍 (Suratul Jinn: 11)

🌍 Aljanu Ƙungiyoyi ne Masu Bambanci

🧠 Malamai sun ce:
Aljanu ƙungiyoyi ne daban-daban, kuma suna da addinai mabanbanta.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya fadi haka kuma a cikin surar nan:

“Hakika Kuma lalle mu, lokacin da muka ji shiriya, mun yi imani da ita.

Duk wanda ya yi imani da Ubangijinsa, ba zai ji tsoron cutarwa ko zalunci ba.”

“Kuma a cikinmu akwai Musulmi, kuma a cikinmu akwai azzalumai.

To, wandanda s**a musulunta, su ne masu neman shiriyar Allah.

“Amma azzalumai kuwa, daga cikin mu sun zama itacen wutar Jahannama.”
📍 (Suratul Jinn: 13–15)

Domin bukatar ƙarin bayani ko shawara ko maganin akan dukkan nau'i shafar aljanu ko sihir ko kammun baka ko akan wasu matsalolin daban daban zaku Iya tuntubar mu 08152753609/08029665783

🟢 Ciwon Ciki Mai Taƙurawa wanda yaki Warkewa?koko bayajin maganin Ko Ciwon Ciki Bayan Haihuwa?Ga hanyar da zata taimaka ...
15/01/2026

🟢 Ciwon Ciki Mai Taƙurawa wanda yaki Warkewa?

koko bayajin maganin

Ko Ciwon Ciki Bayan Haihuwa?

Ga hanyar da zata taimaka — in shaa Allah za’a samu sauƙi.

Yawanci akan ga mutum ya yi ta fama da ciwon ciki amma ba’a sami magani ba, ko ma bayan haihuwa ciwon yaƙi sauka. Idan ka shiga asibiti a duba ka ba’a gano matsalar ba — ka gwada wannan maganin, in shaa Allah zaka ga sauƙi.

🟩 Magani:

✔ A samo duman rafi ko duman kada
✔ A dafa shi ko a yi shayin sa
✔ A sha tare da madara ko kuma a murza ganyan a sha kai tsaye da madara

📌 Ana iya amfani da shi ɗanye ko busasshe, duka suna aiki in shaa Allah.

Fa’ida:

🔹 Ana samun sauƙin ciwon ciki mai tsawon lokaci
🔹 Yana taimakawa ciwon ciki bayan haihuwa
🔹 An jarraba shi a lokuta da dama, kuma ya yi tasiri sosai bi iznillah

(Hoton ganyan yana ƙasa domin sauƙin gane shi)

🕌 Don Allah a taimaka da share domin sauran ’yan uwa su amfana.
Jazakumullahu khayran.

📞 Mai buƙatar karin bayani ko shawarwari
08152753609
✍ Muhammad Jameel Ja'afar

🦠 Helicobacter pylori (H. pylori) –A Ilimin LafiyaHelicobacter pylori (H. pylori) wata ƙwayar cuta ce (bacterium) da ke ...
15/01/2026

🦠 Helicobacter pylori (H. pylori) –A Ilimin Lafiya

Helicobacter pylori (H. pylori) wata ƙwayar cuta ce (bacterium) da ke rayuwa a cikin ciki (stomach), kuma tana iya haifar da matsaloli ga tsarin narkar da abinci,

musamman ciwon gastritis da ulcer. A wasu lokuta masu tsanani, tana iya ƙara haɗarin kamuwa da kansar ciki, wata (Colon Cancer)

📌 Yadda Cutar Ke Faruwa

H. pylori na shiga jiki ta hanyoyi k**ar haka:

Cin Abinci ko ruwa mai ɗauke da ƙwayoyin cuta

Rashin tsaftar hannu a lokacin cin abinci

Hulɗar baki-da-baki a wasu lokuta da mai dauke da kwayoyin cutar.

Da zarar ta shiga ciki, tana iya lalata kariyar bangon ciki, hakan na sa acid ya cutar da bangon ciki, wanda ke haifar da ulcer

⚠️ Daga cikin Alamomin ta

A mafi yawan lokuta, mutum na iya kasance wa ɗauke da H. pylori ba tare da alamomi ba ko kaɗan.

Idan alamomi sun bayyana, suna iya haɗawa da:

Jin zafi ko kona a cikin ciki

Kumburin ciki da jin cunkoso

Tashin zuciya ko amai

Jin koshi da wuri bayan cin abinci kaɗan

Raguwar sha’awar abinci

Raguwar nauyi ba tare da wani dalili ba

Warin baki

Yawan gajiya da kasala

Jin sautuka a ciki

Canjin launin bayan gida (a wasu lokuta)

Lura: Idan an ga jini a amai ko bayan gida, wannan abune da za'a dauki matakin na gaggawa domin dorewar lafiya.

🧪 Hanyoyin daake Ganowa

Ana tabbatar da H. pylori ta hanyoyin gwaji k**ar:

Gwajin numfashi (Urea breath test)

Gwajin bayan gida

Gwajin jini

Endoscopy (a lokuta na musamman)

Likita ne ke zaɓar gwajin da ya fi dacewa.

💊 Magani (Hanyar Likitanci)

Maganin H. pylori yawanci yana haɗa:

Antibiotics (fiye da ɗaya) don kashe ƙwayar cuta

Magungunan rage acid (k**ar proton pump inhibitors)

Ana shan magani tsawon kwanaki 10–14, kuma dole a kammala shi yadda likita ya tsara domin guje wa resistance (ƙin karɓar magani).

🌿 Abubuwan da zasu taimaka wajen Tallafi akan ta (Ba Madadin Magani Ba)

Wasu abubuwa na gargajiya na iya taimakawa a matsayin riga-kafi:

Zuma ta gaskiya – na iya rage yawaitar ƙwayoyin cuta

Tafarnuwa – tana da sinadarai masu yaƙar ƙwayoyin cuta

Citta (ginger) – na taimakawa wajen rage kumburi da tashin zuciya

Muhimmin Lura: Ana bukatar ayi amfani da su ne tare da shawarar likita, musamman ga masu ulcer mai tsanani.

🛡️ Hanyoyin Kariya

Wanke hannu kafin cin abinci da kuma wanke hannu da sabulu ko omo bayan gama bayan gida

Shan ruwa mai tsafta

Guje wa raba kayan baki,yazama kayan tsaftar baki nakane kai kaɗai

Cin abinci mai tsafta da tsaftataccen muhalli

📝 Takaitawa

H. pylori cuta ce da ke shafar ciki

Wasu mutane ba sa nuna alamomi

Ana iya ganowa da gwaje-gwaje

Maganin likita na iya warkar da cutar gaba ɗaya idan an bi umarni

Idan kana bukatar ƙarin shawara ko maganin mai inganci zaka iya tuntubar a08152753609/08029665783 kira ko Whatsapp

👳‍♂️ LABARIN WANI SAHABIN ANNABI ﷺ DA BARAWO.An kuma ruwaito wata kissa cewa:Wani mutum daga cikin Sahabban Annabi ﷺ yan...
14/01/2026

👳‍♂️ LABARIN WANI SAHABIN ANNABI ﷺ DA BARAWO.

An kuma ruwaito wata kissa cewa:
Wani mutum daga cikin Sahabban Annabi ﷺ yana da shago da aka rufe, yana kasuwanci da dukiyarsa.

Wata rana ya fita k**ar yadda ya saba, sai barawo ya tare shi.

Barawon ya ce masa:
“Ka ajiye abin da ke tare da kai, in ba haka ba zan kashe ka.”

🤲 Bukatar Sahabin Kafin Mutuwa

Sai Sahabin ya ce masa:
“Ba na so komai sai abu ɗaya kacal:

*Barawon yace masa wanne abune kake bukatar?*

Sai wannan sahabin yace masa:
👉 ka bar ni in yi sallah raka’a biyu.”

Daganan wannan Barawon ya amince.

🕊️ Addu’ar da Ta Sauko masa Daga Sama🏰🤚🖐️

Bayan ya yi sallah, a sujada ta ƙarshe, sai Sahabin ya yi wannan addu’a:

“Ya Wadūd, Ya Wadūd, Ya Maɗaukakin Al’arshi,
Ya Mai aikata abin da Ya so,
Ina roƙonKa da girman mulkinka da ba ya gushewa,
da hasken fuskarka da ya cika sammai da ƙasa,
Ka kare ni daga sharrin wannan barawon.”

⚔️ Allah madaukakin ya Amsa Addu’a nan a Take🤲

Da barawon ya ɗago kansa, sai ya ga wani jarumi a kan doki, da takobi a hannunsa.
Sai jarumin ya bugi barawon, ya kashe shi.

Sai Sahabin ya tambaye shi:
“Wane ne kai?”

Sai ya ce:
🕊️ “Ni mala’ika ne daga sama ta huɗu.
Da ka yi addu’ar ka, sai Allah yaji kiranKa, Daga nan Allah madaukakin sarki Ya aiko ni.”

📜 Maganar Anas bn Malik (رضي الله عنه)
Anas bn Malik (Allah Ya yarda da shi) ya ce:

“Duk wanda ya yi wannan addu’a bayan alwala,
ya yi sallah raka’a huɗu,
to Allah zai amsa masa addu’arsa,
ko da ta shafi abin da aka riga aka ƙaddara shine.
Allah ne mafi sani.”

🕊️ Kammalawa

✨ Wannan labari yana nuna:

Girman addu’a

Karfin komawa ga Allah alokacin da aka shiga acikin tsanani,da kuma ƙunci.

Cewa Allah Yana amsa addu’ar mai tsananin buƙata

Kuma Yana turo taimako daga inda ba a zata ba

🤲 Allah Ya sa mu kasance daga cikin masu yawan addu’a da samun amsa warta da karɓar ta nan take. Ameen.

    MAI JAKI DA KUMA WANNAN ƊAN FASHIN DAJI MAYAUDARI 🤕🔪🕌 Mutumin da Ya Ruɗe a SallahAn ruwaito cewa: Wannan mai jakin s...
14/01/2026

MAI JAKI DA KUMA WANNAN ƊAN FASHIN DAJI MAYAUDARI 🤕🔪

🕌 Mutumin da Ya Ruɗe a Sallah

An ruwaito cewa: Wannan mai jakin sai yarude bayan yafara sallar nafila 🕌
Bayan ya karanta Suratul Fātiha, sai ya kasa samun wata aya da zai karanta bayan ta.

Ya tsaya shiru, ya ruɗe, ya rasa abin da zai karanta.

Sai ya ce wa kansa:
😔 “Ina gaggawa, me zan yi a cikin sallah?”

📖 Komawa ga Alƙur’ani a Lokacin Tsanani

Sai tunanin yazo masa acikin Alƙur’ani a cikin zuciyarsa,cewa ya karanta maganar Allah Maɗaukakin Sarki:

> ﴿أَمَّنْ يُجِيبُ الْمُضْطَرَّ إِذَا دَعَاهُ﴾
“Wane ne yake amsa wa wanda yake cikin tsananin hali idan ya kira Shi?”
(Suratun An-Naml: 62)

Sai ya ɗaga muryarsa yana karanta wannan aya da karfi 🎙️

"AMMAN YUJEEBUL MURƊARRA IZA DAAHU WAYAKSHIFU SUUA WAYAKALAKUM KULAFAAL ADAR"

🏃‍♂️ Barawo Ya Ji Kiran wannan Aya

A bayan mutumin akwai wannan barawo.yana jira yagama sallar yaka she shi.

Sai barawo yace kakira duk wanda zaka kira yau kashe ka kawai zanyi 🔪

Da ya ji ayar, sai ta shiga zuciyarsa, har ya fice daga cikin kwari da takobi a hannunsa, k**ar wutar da aka kunna.

🐎Ana cikin hakan sai ga wani mutum ya fito daga cikin wannan kwarin akan doki datakobi a hannun sa🔪

Ya kai wa mutumin hari, ya soke shi da wuƙa, sai mutumin ya fāɗi ƙasa k**ar matacce.

🗣️ Tattaunawa Tsakanin Mutumin da Barawo

Sai barawon ya ce masa:
“Ka karanta aya, kana cewa Allah Yana amsa addu’ar mai tsanani, ni ma ina cikin tsanani.”

Sai mutumin ya ce masa:
“Allah Ya ji ƙorafi na, kuma yakarɓa addu'a ta, kuma Ya nuna mini hanyar tsira.”

Ya ce masa:
“Ka tafi hanyar kabi asalin hanyar daka sani, kada ka ji tsoro.

Da haka Allah madaukakin sarki ya kuɓutar da wannan mai jakin daga hannun wannan ɗan fashin dajin daya yau dare shi 🐎🔪🤕

To k**ar hakane idan kazama mai imani da yakini,da komawa ga Allah da kuma tawakkali izuwa gare shi kake samun taimakon sa,nan take kuma ya amsa addu'ar ka nan take a lokacin daka roke shi.🏰

Allah taala ka amsa mana bukatun na alkhairi,Kabamu kariya daga dukkan sharrin mutane da kuma Aljanu baki daya.

WANNE NE KE AMSA ADDU'AR BUƘATAR WANDA YA SHIGA TSANANI IDAN YA YI ADDU'A A GARE SHI YARO KE SHI?)Kamar wanda ya nutse  ...
13/01/2026

WANNE NE KE AMSA ADDU'AR BUƘATAR WANDA YA SHIGA TSANANI IDAN YA YI ADDU'A A GARE SHI YARO KE SHI?)

Kamar wanda ya nutse aruwa,ko aka yar dashi a cikin jeji 🏜️, kuma ya kusa halaka.

Duk wanda ya dogara ga Allah da gaskiya, kuma ya nemi taimakonsa, addu'arsa za a amsa nan take. 🙏

Allah Maɗaukaki Ya ce: ﴿أَمَّن يُجِيبُ الْمُضْطَرَّ إِذَا دَعَاهُ ﴾ [Surah An-Naml: Aya ta 62]. 🕋
(Ma'ana: Wanene ke amsa buƙatar mai tsanani idan ya yi masa addu'a?)

Daga cikin gaskiyar mai buƙata akwai labarin da Abdul Wahid bn Zaid Al-Basri ya ruwaito. Ya ce:

"A wajenmu akwai wani mutum mai jaki 🐎, wanda yake haya da shi zuwa wasu garuruwa.

Wata rana ya fito daga Basra yana so ya tafi Kufa.

Sai wani mutum ya tare shi, ya gaishe shi, sannan ya tambaye shi: 'Ina za ka?' Sai ya ce: 'Ina so in tafi Kufa,

Sai mutumin yace masa:da ba don ina da rauniba kuma ba zan iya tafiya ba, da na tafi tare da kai.

Idan kana so, zan ba ka dinari 💰 kuma ka ɗauke ni a kan dabbarka, domin na ga tana da sauƙin tafiya, kuma kai kyakkyawan abokin tafiya ne.' Sai mutumin ya karbi dinarin, ya ɗauke shi, s**a yi tafiya a rana ɗaya..." 🤝
"...sai s**a ci karo da hanyoyi biyu 🛣️.

Sai mahayin ya tambayi mai jakin: 'Wace hanya za mu bi?' Sai ya ce masa: 'Babu wata hanya da na sani sai babbar hanya.'

Sai mahayin ya ce masa: 'Wannan tafi kusa kuma tafi sauƙi.' Sai s**a bi wannan hanyar, har s**a iso wani kwari mai ban tsoro 🏞️

inda hanyar ta ɓace musu. Sai mai jakin ya ce: 'Ina hanya?' Sai mahayin ya miƙe tsaye, ya fito da wata babbar wuƙa 🔪 daga cikin rigarsa, ya ce:

'Wannan ita ce hanya.' Sai [mai jakin] ya ce masa: 'Ya ɗan'uwana, ka karɓi jakin da duk abin da ke kansa, ka bar ni in tsira da kaina.' Sai [mahayin] ya ce masa: '

Dole ne in kashe ka.' Sai [mai jakin] ya ce masa: 'Idan ka yi niyyar kashe ni, ka bar ni in rufe aikina da raka'a biyu.' Sai [mahayin] ya ce masa: 'To.' Sai mutumin ya yi alwala da ruwan da yake tare da shi, ya tsaya..." 🤲

(1) A asali yana nufin niyya...........zan kawo karshen sa, a rubutu nagaba idan kunji dad'i kuyi mana share, Mun gode Allah yasaka da alkhairi

Address

Jani House Funtua Jihar Katsina
Funtua
2030

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Formula 9 formula 8 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share