18/03/2021
Gwamnan Najeriya ya bayyana dalilin da zai sa ya sauka daga kujerar mulki
Daga Yahya Abdullahi Birnin Gwari
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi alkawarin yin biyayya ga bukatun mutanen da yake mulka
- Makinde ya nesanta kansa da iyayen gida a siyasa
- Gwamnan na Oyo ya bayyana dalilin da ya sa bai k**ata a dauki zaben shugaban kasa na 2023 a matsayin mai mahimmanci ba yanzu
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce zai sauka daga mukaminsa idan mutanen jihar s**a nemi ya yi hakan.
Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba, 17 ga Maris, a taron kungiyar datawan Yarbawa da aka yi a Mapo Hall, Ibadan, PM News ta ruwaito.
Makinde ya ce shi bai damu da matsayin ba, inda ya kara da cewa shi ya sa ya lashi takobin yanke hukunci don amfanin jihar da kasar Yarbawa.
Ya ce:
"Idan mutanen jihar Oyo s**a nemi na bar ofis a matsayin gwamna a yau, ba zan yi jinkirin barin ofishin ba saboda a kullun da jakata nake zuwa ofis."
“Na tsaya takara a 2007, 2011 da 2015 amma na fadi kuma da lokaci ya yi da Allah Ya sa zan zama gwamna, shi ya sanya ni.
Idan mutanen jihar s**a yanke hukuncin cewa ba sa sona kuma, zan dauki jakata ne kawai in tafi saboda ba ni da ko allura a ofis.”
Makinde ya kuma bayyana cewa bashi da ubangidan siyasa sai Allah uba.
Da yake magana kan zaben shugaban kasa na 2023, gwamnan ya shawarci yankin kudu maso yamma da kada su mayar da hankali kan zaben da za a yi nan gaba yanzu.
Ya ce ya k**ata yankin ya fi mayar
da hankali wajen ganin an yi adalci ga wadanda aka cuta.
Makinde wanda shine gwamna daya tilo a karkashin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a kudu maso yamma ya yi kira ga hadin kai don magance matsalar rashin tsaro a yankin.