20/09/2025
Duk yadda muka kai da son Wallahi baza mu iya cusa Soyayyar Malam ga kowa ba, akwai masu fahimtar gaskiya akwai marasa fahimta, akwai masu mutunci da girmama nagaba koda sunga kuskure sukanyi tsokaci cikin hikima da ilimi, akwai kuma masu jiran kuskure su yada, amma basu yada alkhairi.
Imamu Shafi'i a littafin sa ديوان الشافعي yace: idan sakarai yayi magana(ta rashin girmamawa) Toh kada ka amsa masa, abunda yafi alkhairi shine kayi Shiru saboda idan kayi magana zaiji dadi (Kuma tabbas zai kara yin maganar da tafi ta farko muni da zafi)
إِذا نَطَقَ السَفيهُ فَلا تَجِبهُ فَخَيرٌ مِن إِجابَتِهِ السُكوتُ فَإِن كَلَّمتَهُ
فَرَّجتَ عَنهُ....
Ba kowace magana ake mayar da martani ba, garin gyara sai ata bude wasu kofofin baraka.
masu raunin imani dama abun da suke so kenan
Allah yasa mudace. Malam Allah yakara doraka akan daidai. Amin.
✍️
# RayuwarMalamai
14th Sep 2025CE