Auwal Bin Umar

Auwal Bin Umar Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Auwal Bin Umar, Shopping & retail, Kwami LGA malam sidi checheniya, Gombe.

24/12/2025

CEWA KIRISTOCI "HAPPY CHRISTMAS" DAIDAI YAKE DA AMINCEWA DA AKIDAR ALLAH YA HAIHU, KUN GANE?

21/12/2025

MIJINA YANA SADUWA DA NI, RANAR GIRKIN KISHIYATA


Tambaya
Asslmu alaikum
Mun kasance mu biyu awajen mijinmu.
Sai ya kasance yar uwata bata iya gamsar dashi, to ko ranar girkinta yakan shigo ya tara dani da rana ko da daddare.

Tambaya anan shi ne malam shi hakan ya halasta?
Kuma idan na mishi magana yadaina zuwa baya ji ba gidan mu daya ba.
Dan Allah hukuncin hakan da mafita.

Amsa:
Wa'alaikum assalam, Ya wajaba ya nemi izininta, tun da hakkinta ne, in har ta sarayar ya halatta ya sadu da ke a ranar kwananki da kwananta.
Saboda lokacin da Nana Saudah ta tsufa ta ji tsoron kada Annabi S.A.W ya sake ta, ta dauki kwananta ta bawa Nana A'isha, kamar yadda Bukhari ya rawaito.

Bayan haka Annabi S.A.W yana yin kwana dai-dai a dakunan matansa guda bakwai, ita kuma Nana Aisha yana mata kwana biyu, Saudat kuwa ba ya kwana da ita, saboda ta sarayar da hakkınta.

Allah ne mafi sani.

04/7/1437
12/4/2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Daga A'isha (R) : An tambayi Manzon Allah (SAW): Wanne aiki ne ya fi soyuwa a wajen Allah? Sai ya ce: ((Aikin alkairin d...
16/12/2025

Daga A'isha (R) : An tambayi Manzon Allah (SAW): Wanne aiki ne ya fi soyuwa a wajen Allah? Sai ya ce: ((Aikin alkairin da aka dawwama ana yi, ko da kaɗan ne))

📚 Bukhári da Muslim

Abubuwa guda bakwai da ladansu zai cigaba da gudana bayan Mutuwar Mutum:Manzon Allah ﷺ yace: Lalle yana daga cikin abind...
15/12/2025

Abubuwa guda bakwai da ladansu zai cigaba da gudana bayan Mutuwar Mutum:

Manzon Allah ﷺ yace: Lalle yana daga cikin abinda zai riski Mumini na aikinsa da kyautatawansa bayan Mutuwar sa:

1•Ilimin daya koya kuma ya yaɗashi.

2•Da Qur'anin da ya gadar.

3•Da ɗa nagari da ya bari.

4•Ko Masallaci da ya gina.

5•Ko gida daya gina ga matafiya.

6•Ko qorama da ya gudanar.

7•Ko Sadaqa mai gudana daya aiwatar daga cikin Dukiyarka a halin lafiyarsa da rayuwarsa Wanda ladan zai cigaba da Isa gareshi bayan Mutuwar sa.
📚 Saheh ibnu Majah na Albany -200

Manzon Allah ﷺ yace: idan ɗan Adam ya Mutu dukkan ayyukansa sun yanke saita 6angare uku: Sadaqa mai gudana da ya bari, ko Ilimin daya koyar ake amfana dashi, ko ɗa nagari da yabari yake masa addu'a".
📚 Saheh Muslim -1631

•Waɗannan Hadisai suna nuna mana cewa dazaran Mutum ya bar Duniya to dukkan ayyukansa sun tsaya saidai ta waɗannan hanyoyi da aka ambata.

•Wannan kuma yana nuna mana cewa lalle Mutum yayiwa kansa tanadin aiki na kwarai da ladansa zaina kaiwa gareshi bayan Mutuwar sa.

•Tahanyar ya koyi ilimin addini kuma ya Karantar dashi dan Allah kuma yabawa Yaransa tarbiyya ta gari, ko ya Gina Islamiyya ko Masallaci ko Rijiya ko famfo ko gida ga Mabuqata dan Allah, ko yadasa bishiya ko yabada Sadakan Qur'anai da littatafan addini ga ɗaliban ilimi, ko Taimaki Wani wajen Karatun addini ko yadau nayinsa, da sauran ayyukan alkhairi da zasu wanzu bayan rayuwarsa.

•In aka samu akasi Mutum bayyi ɗaya daga cikin waɗannan dabarunba har ya Mutu to lalle yayi hasara duk Dukiyarsa kuma zayyi Dana sani da Nadama, amma duk bazasuyi amfaniba.

Allah yabamu ikon aikata ayyukan alkhairi waɗanda zamuci gajiyarsu bayan Mutuwar mu Ameen.

Sheikh Usman Haruna Abu Rumaisa Assidawiy...✍️

Daga Hafs Ɗan Ásim (R) Manzon Allah (SAW) ya ce: ((Ya ishi mutum zunubi ya ke bayar da labarin duk abin da ya ji)) 📚 Mus...
14/12/2025

Daga Hafs Ɗan Ásim (R) Manzon Allah (SAW) ya ce: ((Ya ishi mutum zunubi ya ke bayar da labarin duk abin da ya ji))

📚 Muslim

Address

Kwami LGA Malam Sidi Checheniya
Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Auwal Bin Umar posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share