Nus-Hal Poultry And Agro-Tech Services

Nus-Hal Poultry And Agro-Tech Services INNOVATING AGRICULTURE

22/04/2026

Ibrahim Mohammad Ibrahim CEO Nus-Hal Poultry And Agro-Tech Services

16/04/2026

Ku zo muyi wani estimate.

Idan ka ware Naira 750k zai yi maka kiwon kajin layer (Kaza mai yin kwai).

Wannan 750k zai isa ka sayi abincin kajin na 6 Months, ka sayi vaccination din kajin na 12 Months, ka gina gidan kiwon kajin, ka sayi feeding equipment, ka sayi PPE da sauran abubuwan da ba a rasa ba duk a cikin 750k.

Expexted ROI (Return On Investment) dinka bayan kajin nan sun fara kwai zai iya zamowa 10k ne a kullum har na tsawon shekara daya da rabi Insha Allah.

Idan ka hada jimillar kudin duka zai k**a almost 5.4million zaka samu a matsayin riba a cikin shekara daya da rabi ta hanyar zuba jarin 750k kacal.

Duk da cewa akwai lissafin sayan abincin kajin still na tsawon shekara daya da rabi a cikin wannan 5.4million din, amma duk da haka dai zaka iya tsira da 4.075million, idan ka cire asalin jarin da ka fara sakawa kuma zaka tsira da almost 3.3250Million naira ne.

Ka duba ka gani, a cikin watanni 18 kacal ka samu ribar miliyan 3 da dubu dari 3 da wani abu.

TO AMMA KASAN WANI ABU?

750k din nan fa a matsayin jarin nan da ka zuba kudin sunyi yawa sosai, abinda ya jawo yawan kudin kuma saboda kana sayan abincin kajin ne, amma idan kai kake hada abincin kajin da kanka to jarin da zaka zuba naira 580k ne kacal.

Kaga tunda jarinka ya ragu kenan ribanka zai karu, a wannan lisaafin EROI dinka zai k**a almost 4.710 million ne, idan ka cire asalin capital dinka, zallan ribarka almost 4.0 million ne.

Kaga da jarin naira 750 kacal ka samu riba mai gwabin gaske a cikin watanni 18 kacal.

NOTE:
Wannan fa lissafin kiwon kazar layer ce kawai, ta hanyar sayar da kwai dinta kadai zaka samu wancan ribar, kuma ba wai sai bayan watanni 18 din zaka debi kudin ba, kusan kullum ne zaka rika samun 10k idan ka kiwata kajin kiwonka yai kyau.

Mu farka 'yan uwa!
.. ✍🏻
Ibrahim Mohammad Ibrahim

16/04/2026

SANA'AR KIWON KAJI.

1). ABU NA FARKO:
A kauye kake ko a gidan haya bazai hanaka sana'ar kiwon kaji ba, sai dai ya danganta ga wane irin kiwon kaji ya k**ata kayi.

Dole kiwon kaji yana bukatar la'akari da:

i). Environment: (Muhallin da kai mai kiwon kake ko kuma inda zaka yi kiwon).

ii). Temperature: Yanayin zafi ko sanyi na yankin da kake ko yankin da zaka yi kiwon.

iii). Financial Capital: Lissafin irin jari na kudi da kake da shi don sanin wane irin kiwon kaji zaka yi da kuma adadin abinda zaka iya kiwatawa.

iv). Knowledge : Ilimin kiwon kajin don ka zamo profitable trader da kuma risk management.

Wadannan su ne manyan abubuwa guda hudu da ya k**ata ka yi la'akari da su kafin ka fara kiwon kaji, sanin wadannan abubuwa da aiki dasu shi zai baka karsashi wajen kiwon da karin fahimtar cewa duk labaran da ake bayarwa akan kaji na yawan mutuwarsun nan ashe jita-jita da farfaganda ce kawai.

2). ABU NA BIYU:
Idan aka ce kiwon kaji, dunkulalliyar kalma ce wanda take kunshe da fannoni na kiwon kaji daban-daban. Idan aka buda ma'anar kalmar zamu gane cewa kiwon kaji ya kasu zuwa na'ukan kajin da muke da su musamman ma anan Najeriya.

Kenan kiwon kaji sana'ah ce da ta kunshi na'ukan kiwon kaji kusan kala biyar, kuma kowanne kala daga cikinsu tsarin kiwonsa ya bambanta da na dan uwansa.

i). Akwai kiwon kazar gida (Local chicken).
ii). Akwai kiwon kazar Broiler
iii). Akwai kiwon kazar Layer
iv). Akwai kiwon kazar Noiler
v). Akwai kiwon kazar Cockrell (Kudinka a bola) kenan.

Kunga wadannan nau'uka na kiwon kajin, babu wanda idan ka nemi iliminsa ka fahimceshi ka kuma k**a yinsa bazai baka makudan kudade ba, amma dole sai kayi la'akari da wadancan abubuwa da muka ambata a sama.

A Enterprenuer akwai abinda ake cewa 4Ps.

a). Place: Dole kayi la'akari da wajen da zakayi kiwon kaji kafin kasan wace irin kaza ya k**ata ka kiwata.

b). Product: Dole kayi la'akari da mutanen da suke rayuwa a inda zaka yi sana'ar kiwon kajin domin kasan irin nau'in kaza da ya k**ata ka kiwata.

c). Promotion: Dole ka san yadda zaka rika tallata kajinka domin ka samu kwastomomi su rika saya, domin duk ingancin kayanka ko da ba kaji bane ai dole dai sai ka tallata shi kafin asan kana sayarwa, to haka kajin ma dole sai kana tallata sana'ar taka tukuna kafin ka samu masu saya har ka kwashi riba.

d). Price: Dole ka samu farashi moderate ka saka ta hanyar la'akari da yadda zaka saukakawa mutane kar ka tsawwala musu, tare da la'akari da kanka kuma ta yadda bazaka saka farashin da bazaka iya maida kudinka bama ballantana ayi maganar riba.

3). ABU NA UKU.
Yana da kyau mu tashi mu k**a harkar nan na kiwon kaji gadan-gadan domin dogaro da kai da kuma rufawa kai asiri.

Akwai ilimummuka jibge a cikin sana'ar kiwon kaji, wanda kake bukatar ka san su kafin ka tinkari sana'ar.
.. ✍🏻
Ibrahim Mohammad Ibrahim

15/04/2026

_*PLEASE MU KARANTA WANNAN BAYANIN HAR KARSHE*_

Bisa tambayar da nai dazu cewa: "Wace sana'a ce mutum zai k**a da 1million naira kuma kullum ya rika samun ribar 20k naira a jikinta?"

Da yawa sunyi kokarin kawo sana'o'i da s**a dace da wannan target din kuma Alhamdulillah na san sanadiyar haka wasu sun karu da rubutun domin sun samu haske akan sana'ar da za a fara da matsakacin jari kuma a rika samun riba mai gwabi kullum.

Babban Misalin sana'ar da aka bada amsa da ita ita ce:
Sana'ar sayar da Pure water.
Tabbas idan ka samu location mai kyau ka sakawa harkar Pure water 1million naira Insha Allahu kullum sai ka kidaya ribar 20k naira.

2). SANA'A TA BIYU.
Akwai sana'ar da ko kadan ba a kawota karkashin wancan comment section din ba, kuma sana'a ce ga duk wanda ya reneta bayan ya karanceta ya fahimceta yadda ya k**ata, to da 1million dinsa zai rika kwasar riba cikin taimakon Allah.

Sana'ar ba compitable bace, actually ma masu yinta sunyi kadan saboda yadda a kullum product demand dinta yakan fi product supply dinta yawa, yawan masu neman kayan da sana'ar ke fitawar yafi adadin kayan da sana'ar take fitarwa.

Ba seasonal sana'a bace ballantana ace akwai lokacin da kasuwar take yin sanyi.

Sana'ace very pure, da dan karamin jarinka sai ka rika dibar riba mai yawa Insha Allah.

Wannan ba kowace sana'a bace illa sana'ar HARKAR POULTRY AND VITAL FEED PRODUCTION.

Harkar kiwon kaji da yin abincin kaji gaskiyar magana sana'a ce da a yanzu take tashe kuma aka fara wayewa da ita, yankin Arewanmu an barmu a baya sosai akan sana'ar nan, yawanci supply dinmu daga Kudu yake fitowa almost 70%, 30% ne kawai yake fitowa daga Arewa nan ma kamfanonin da suke yi mana supply na product da suke Arewa din ma mafi yawa na 'yan Kudu ne s**a zo nan Arewa s**a giggina su.

Idan ka tsaya ka kalli wadannan abubuwa k**ar haka:

'Ya'yan kaji (Day-Old)
Layed Eggs
Processed meat
Vital feed
Hatching services

Yawanci source dinsu daga Kudu ne, mu nan Arewa sai dai a noma kawai a kawo mana musa kudi mu saya muyi amfani da shi.

Yau idan farashin kaji day-old ya tashi ko ya sauka control din hakan yana hanun Yarbawan nan 'yan Kudu ne, mu muke da high consumption and demand amma kuma su suke da high production and aupply.

Harkar poultry ba karamin zunzurutun kudi ake samu sanadiyarsa ba, me zai hana muma 'yan Arewa mu farka mu rungumi wannar sana'a hanu bibbiyu?

Kafin ka kushe sana'ar yana da kyau ka fahimci cewa duk yadda propaganda yake yawo akan risk na sana'ar wallahi ba haka abin yake ba, though babu sana'ar da babu risk a cikinta, amma yadda ake zuzuta asarar da ke cikin harkar poultry abun bai kai haka ba ko kadan, kuma daman ai duk sana'ar da zaka yi ta bakada iliminta ai dole ka rika tafka asara, amma idan ka karanceta fa?

Daga cikin harkar poultry idan ka dauki fanni daya kawai ka kware akai wallahi ka sha kwana an gama Insha Allahu.

Misali:
Idan ka dauki fannin "Eggs production" ta hanyar karantar yadda ake kiwata kazar layer to nan ba karamin kudi ake kwashewa ba.

Idan ka dauki fannin Vital Feed production ka karance shi ka kware akai musamman ma yadda ake hada abincin kazar layer, shikenan kai kam. Ace ya zamana kana kiwon layer kuma kana samar da abincinta da kanka ba saya kake yi ba, ai kar ka qi kaga irin ribar da zaka kwashe da 'yar 1 million dinka ko kasa da haka Insha Allah.

A karkashin kiwon kazar layer kawai akwai Business Opportunities kusan guda biyar da duk wanda ka k**a zaka samu kudi masu kyau da su.

Sannu a hankali zan rika kawo mana bayani akan harkar nan domin mu fahimci irin alfanun dake ciki Insha Allahi ta'ala.
...✍🏻
Nus-Hal Poultry And Agro-Tech Services

15/04/2026

BUSINESS OPPORTUNITY

002

A sana'o'in da Arewa ta dogara dasu a yanzu mun gama fahimtar cewa an nakasa harkar noma, dubban matasa da dottawan da a baya s**a dogara da harkar noma a yanzu sun zamo basu da madogara tunda harkar ta lalace saboda rashin tsaro, rashin ingantaccen tsaro na gomnati da tsadar kayayyakin noma na zamani.

2). Sana'a ta biyu ita ce kasuwanci.
Kasuanci a yau shima yana neman karyewa a Arewa, dalili kuwa shi ne rashin tsaro.

Karamin misali da zamu dauka wajen gamsuwa da tabarbarewar kasuwanci sanadiyar rashin tsaro shi ne:
A yau kidnapping ya zamo ruwan dare a Arewarmu, idan aka dauki wani dan talaka aka kaishi daji aka ce ba za a sake shi ba sai an biya naira miliyan 10, dangi da 'yan uwa fa su ne masu hada wadannan kudaden.

Daga cikin 'yan uwa da dangin nan idan akwai 'yan kasuwa uku masu jarin Naira miliyan bibbiyu, sai kowannensu ya dauki nauyin bada gudunmowar miliyan daya domin a hada kudi a kaiwa 'yan ta'adda a daji su sako wancan bawan Allah da s**a k**a, to su fa daga nan karfin kasuwancinsun nan yaja baya, kayan da zasu sayo a baya a yanzu kaso hamsin ne kawai na kayan zasu iya saya, kaso hamsin na jarinsu sunyi asararsa.

Idan kuma dan kasuwa aka dauka aka bukaci naira miliyan 30, dole kayayyakin kasuwancin nasa za a gwanjar a kadar dasu tass! domin a samu kudin zuwa a biya fansar sa.

Misalan haka da yawa yasha faruwa a Arewa, kunga ko ta nan ma kadai kasuwanci ya samu mummunan tasgaro a yankinmu na Arewa.

Wadancan misalan fa masu dan dama-dama ne wai a hakan ma idan ka kwatanta da rashin shigowar foreing investors da insecurity ya hana su shigowa su zuba hanun jarinsu a yankin Arewan, rashin wutar lantarki da ya kashe kamfanoni da masana'antu da yawa a Arewa, da dai wasu misalai mak**anta wadannan.

Bisa wadannan bayanan zamu fahimci cewa harkar kasuwanci yana kan hanyar tabarbarewa a yankinmu na Arewa muddin ba matakan gyara aka dauka na gaggawa ba.

Kuma wadancan sana'o'i guda biyu "Noma da kasuwanci" tabarbarewarsu ba karamin rashin aikin yi da rashin kudin shiga yake jawowa ga matasa masu kokari da mafarkin gina gobensu ba.

Sanadiyar haka ake kara samun ta'azzarar 'yan shaye-shaye, yawan ta'addanci da sauran miyagun laifuka.

Ku biyo ni sannu a hankali domin fahimtar mafita akan wadannan matsaloli.
.. ✍🏻
Nus-Hal Poultry And Agro-Tech Services

15/04/2026

BUSINESS OPPORTUNITY.

Ku karanta wannan a tsanake.

A nan yankinmu na Arewa manyan sana'o'in da muka taso muka ga iyaye da kakanninmu suke yi basu wuce guda uku ba: Noma, "Kiwo, fatauci (Kasuwanci)", idan akwai wadanda zasu biyo baya ba su wuce irin su: Kira da Sassaka ba.

Yanzu dukka wadannan sana'o'i a Arewa sun zamo tarihi, idan muka kalle su daya bayan daya zamu ga cewa:

1). Noma:
Rashin tsaro da tsadan kayan noma na zamani su s**a kashe harkar noma murus a Arewacin Najeriya, kuma gomnati ke da alhakin hakan, tunda ita ta karya farashin abinci sannan kuma taki karya farashin kayayyakin noma na zamani k**ar taki, magungunan feshi da sauransu domin talaka yai noma cikin sauki.

Sannn ita gomnatin dai hallau ta kasa maida hankali wajen dakile rashin tsaron da ya addabi yankin na arewa, wanda hakan ya kara mayar da harkar noman baya sosai.

Sannan gomnati ta ki samar da tsari wajen daura matasa akan harkar noma, wanda hakan shi ma ya kara jawo tabarbarewar lamarin noman.

Sannn gomnati ta rusa harkar industrialization da ko da ace manoman sun samu damar yin noman zasu samu wajen sayar da amfanin gonar tasu da daraja.

Kuma shi noma shi ne ginshikin rayuwar kowa ba ma talaka kadai ba, talaka da ya dauke shi a matsayin sana'a shi ne ya shiga halin kaka-ni-kayi a yau, amma masu hanu da shuni kam zasu fita waje su nemo abincinsu su kawo gida su ci ba lallai sai wanda Malam talaka ya noma a Arewacin Najeriya ba.

To ina mafita?

Ku biyo ni sannu a hankali domin jin inda wannan maqalar tawa ta sa gaba.
...✍🏻
Nus-Hal Poultry and Agro-Tech Services

15/10/2022

Maraba da zuwa shafin mu mai albarka na "Daga Alƙur'ani mai girma"

Fatan zaku kasance damu a wannan shafin domin ƙaruwa da abinda shafin zai zo muku dashi da kuma samun gudunmowar ku domin tafiyar da shafin gaba.

Muna maraba da gudunmowar ku ta alkhairi akan abinda ya shafi manufar ƙirƙirar wannan shafi mai albarka tare da farin cikin kasantuwar ku mabiya wannan shafin.

Fatan Allah ya taimake mu ya ƙarawa rayuwar ku albarka.

Wasalamu alaikum!

29/08/2022

Indeed, the patients will be given their reward without account.

30/07/2022

Akwai baiti da na rubuta mai taken "Yankin mu Arewa" zsn sake shi a rubuce a timeline ɗina insha Allahu nan ba da jimawa ba.

Ina neman wanda zai shiga studio ya rera mana ita don Allah.

Idan akwai wanda zai iya yai min magana ta private domin mu tattauna!

28/04/2020

RAMADHAN MUBARAK!

21/07/2016

HADIN KAI A MUSULUNCI
Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barkatuhu!
'Yan uwa masu albarka,yau kuma MIMBARIN SUNNAH zata yi mana bayani ne dangane da hadin kai a musulunci.
MENENE HADIN KAI?Hadin kai wata aba ce wadda ake buqatar al'umma su kasance akai domin cimma dukkan wata muradun su ba tare da wata tangarda ba.
To kuwa tunda haka ne,yafi kyautuwa ace wannar ma'ana ta sifar hadin kai tafi dacewa da rayuwar musulmi a cikin musulunci.
Idan yau akace babu hadin kai a cikin al'umma,to wannar al'ummar zata rasa muhimman abubuwa k**ar haka:-
(1)zata rasa qarfi ta kowane bangare
(2)Bazata taba cimma muradun ta ba.
(3)Zata rasa ci gaba a dukkan lamuran ta.
(4)Za kuma ta rasa rahamar ubangijin ta.
(5)Kima,kwarjini da kuma mutuncin wannar al'ummar zai yi matuqar rabuwa a idanun abokan gaba.
Saboda haka,yaku 'yan uwa masu albarka,ina qira a garemu damu zo mu hada kan mu,kar mu zamo masu farraqa,domin kaucewa abubuwan da aka lissafo a sama.
Allah ta'ala ya taimake mu,ya kuma hada kan mu.

Address

Gombe

Telephone

+2349061567188

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nus-Hal Poultry And Agro-Tech Services posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category