19/09/2025
Sunan Littafi: Tafiya Mabuɗin Ilimi
Marubuci: Abubakar Imam
Adadin Shafuka: 73
Shekarar Bugawa: 1944
Mawallafa: Northern Nigerian Publishing Company Limited
Tafiya Mabuɗin Ilimi littafi ne dake bada labarin tafiyar da editar jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo Abubakar Imam da sauran editoci daga yankin ƙasashen Afrika ta Yamma, sunyi wannan tafiyar ne a dalilin taron Majalisar Ingila (British Council) a shekarar 1943 lokacin ana tsaka da yaƙin duniya na biyu wato yaƙin Hitila. Mallam Imam ya samu damar shiga jerin editocin da s**a je Ingila tare da Nnamdi Azikwe ɗan kabilar Ibo a lokacin yana editan jaridar Pilot tare da Isaac .B. Thomas bayarbe wanda shima editan jarida ne me suna Akede Edo, su uku kenan daga Nijeriya. Akwai wasu daga Gollkwas da Saliyo.
Tafiya cikin yanayin yaƙi akwai wahala duk da su tazo musu da sauƙi, amma a tafiyar sun samu tseko musamman hare-haren Jamusawa abokan hamayyar Ingila, amma a hanyar su ta dawowa basu samu wannnan tashin tashinar ba. Sun isa Ingila bayan shafe kwana ki da dama suna tafiya akan ruwa, a dalilin babu jirgin sama, sabo da yana yi na yaƙi a lokacin, tafiya akan ruwa ita ce mafita shima akan haɗu da mayaƙan nan na Jamus ma'ana yaran Hitila.
Mallam Imam ya bankaɗo mana abubuwa da dama na ban mamaki da darussan daya koya daga Turawa a dalilin wannan tafiyar, kuma ya cika littafin da salo na ban dariya, ya kuma bayyana kansa a matsayin baƙauye duk da mutane dama a hakan s**a ɗauke shi. Se dai daya haɗu da Turawa irin su Luggard da Hans Vicher (Ɗan Hausa) da sauran masu jin harshen Hausa da magana da harshen sun ɗaga kimarsa a matsayin babban marubuci, fasihin matashi, ɗalibi mai kaifin tunani da basira. A yadda Imam yayi riƙon da shigar da ta Mallam bahaushe daga gida har yaje Ingila ya dawo abun burgewa ne matuƙa, sannan wasu da basu taɓa ganin bahaushe ba sun ta kafa misali dashi a matsayin ɗaya. Imam dai ba iya wakiltar jaridar Arewa ya wakilta ba, ya wakilci Hausawan Nijeriya da na duniya baƙi ɗaya a lokacin.
Cikin littaffin na koyi darussa kamar yadda Turawa suke da hangen nesa akan lamuran rayuwa, inda s**an saka abubuwa a muhallinsu, sannan basa wasa da dama a rayuwa. Haka kuma yadda suke bada tarbiyya tsakanin ya'yansu yayu da ƙanne, wanda hakan ma ya burgeni Imam, su basa horon yara da duka sedai magana cikin hikima, kuma s**an sa yara ƙanana su gane kuskuren su cikin hikima da jawo su a jiki.
Haka ɓangaren ƙere-ƙere Imam ya ruwaito cewa Ingila da sauran ƙasashen duniya sunyi fice, yayin da mu aka barmu da ƙananun tunanunnuka, wanda har wa yau muna nan kamar yadda muke.
Imam da abokan tafiyarsa sun dawo gida da ransu cikin ƙoshin lafiya, sannan ya ƙara samun kwarewa a aiki, sunyi yawon buɗe ido, tabbas "Tafiya itace Mabuɗin Ilimi". Marubucin ya samu ƙarin girmamawa da sheda ta gari, sannan ya fito da jama'arsa kunya.
©Aliyu Idris
₦2,000 @ Laylah Bookstore Gombe