20/10/2022
Copied By Ummee Yusuf. =Kashi; 001
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348030964043
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
[10/22, 4:09 PM] Ummee Yusuf: π¦πΉπ¦πΉπ¦πΉπ¦πΉ
π¦πΉπ¦πΉπ¦πΉ
π¦πΉπ¦πΉ
π¦πΉπ¦
π¦
*UMMU SALMA*
π¦
π¦πΉπ¦
π¦πΉπ¦πΉπ¦
π¦πΉπ¦πΉπ¦πΉ
A true love story.
Written by *UMMEE YUSUF*
( maman Yusuf)
Assalmu alaikum my fans gani Allah ya kara dawowa dani da sabon novel na mai dauke da zallar soyayya INA rokon Allah k**an yanda na fara lafiya mu gama ta lafiya.ina yinku sosai irin sosai dinnan faππ
Special greeting for my forum members luv u all.
*~βπ½βπ½GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONβπ½βπ½~
*~βWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np painβπ½~*
π
ΏAGE 1β£
Bissimillahi rahmanir rahim
Tsuke d'an mitsisin bakinta tayi tana jan tsaki yafi cikin trailer tare bankawa mallamin da ya dage yana koya musu physics harara a kusan karo na ba adadi,saboda sosai take jin haushin shi ji take k**an ta rufe shi da duka.
Kwata-kwata bata fahimtan abinda yake karantar dasu, burinta kawai a tashi daga makarantan taje taga nurul qalbinta.
Tana cikin tunaninta taji yayi musu sallama ya fice daga class d'in nasu.
Wata nauyayyan ajiyar zuciya ta sauk'e cike da jin dad'i ta fara tattara books d'inta na kan desk tana maida su cikin school bag tare da ciro wani k'aramin Handkerchief fari kal a ajihun wandonta ta fara goge beauty face d'inta dashi.
" besty wannan duka shirin wai na menene"?cewar Zee da take kallonta tund'azu .
Murmushi k'wance akan beauty face d'inta ta bata amsa da cewa..." Why asking me bayan kinsani,"
Mik'ewa tayi tare da rataya school bag d'inta a kafad'a kuma hakan yayi daidai da buga bell na after school.
Har ta juya zata fita daga class kuma ta dawo da baya tare da sunkuyowa dai-dai kunnen s**ayi tace with a smiling face..."u will not understand Zee,see u tomorrow " tana fad'an haka ta fice cikin Sauri.
Da ido Zee ta raka ta har ta fice sannan tayi murmushi tare da girgiza kai tace..." UMMU SALMA kenan.
Fita tayi direct daga school d'in ba tare da ta tsaya jiran twins brothers d'inta.
Ko yunwan irin na after school bata ji sai zuba sauri take Dan taje inda s**a saba had'uwa da nurul qalbinta wato SHETTIMA.
Tazo tsangayar su SHETTIMA tana ta raba ido cikin d'alibai da ta gani suna rubutun allo ko zata ganshi amma bata ga ko alamar shi ba a cikin su.
Jiki a tsab'ule take tafiya saboda kullum ta tashi daga school anan makarantan nasu take fara ganin shi.
Tana yin faba kad'an zai mik'e yabi bayanta zuwa inda s**a saba had'uwa su sha hirar su ta β€ duk da tasan abinda zata tarar a gida ba zai hana ta tsyawa ba.
Tana shan corner ta hango shi can yana jiranta a inda s**a saba had'uwa.
Wani sanyi taji yana ratsa tun daga tafin karfarta har zuwa tsakiyan kanta.
A hankali ta fara takowa kanta a k'asa ganin ya tsare ta da kyawawan idanun shi tare da jifanta da murmushin sa mai kara narkar mata da zuciya.
Jawo hijabinta tayi ya rufe mata rabin fuska tana murmushi ta karaso tare da jingina da jikin bangon da yake tsaye amma d'an nesa dashi kad'an.
Motsowa yayi kusa da ita yana lek'a fuskarta tare da cewa.." Gimbiya da alamu yau sarautan ya motsa tunda ake min rowan ganin fuskar da tafi komai a rayuwata".ya k'arasa yana dariya.
Dariya ta kyalkyale dashi itama tare da d'an janye hijabin zuwa baya kad'an.
" haba ko kefa,kinsan lokacin da na b'ata ina jiran isowarki anan ?"
" ni harna shiga wani hali da ban ganka ba acan makarantar ku, zuciya ta ta cika da kuncin rashin ganin ka ga wasi-wasi da ya cika raina ina tunanin ko lafiya? Saboda hakan bata tab'a faruwa ba".ta karasa maganan da dqmuwa k'wance akan beauty face d'inta.
Shima cike da damuwar ya fara bata amsa .." Eh hakane,nayi hakan ne saboda a makarantar mu an fara sa min ido shiyasa kika ga na riga ki zuwa yau"
"UMMU SALMA ba zan gaji da fad'a miki ba ina son muyi aure in killace ki a cikin gidana in nuna miki irin tsantsar soyayyar da nake miki" .
D'an dakatawa yayi yana kallon yanda duk ta shiga tashin hankali k**an yanda take shiga a kowqni lokaci indai zai zo mata da maganar auren su sannan ya cigaba...
"Darajar 'ya mace gidan mijinta SALMA baki san yanda nake jin zafi a raina ba inna hango ki cikin wannan ranan ,Dan haka nake son ki bani dama in fito ayi auren nan kiga yanda zan nuna miki zallar soyayya tare da kulawa".
Hawayen da ya gangaro mata tasa handkerchief ta goge sannan ta d'ago ido ta kalle shi kad'an ta maida kanta k'asa dan bazata iya jure kallon shi ba saboda a duk lokacin da ta kalle shi sai taji wutar kaunar shi na k'ara ruruwa a zuciyar ta.
"SHETTEE kaima kasan ba laifi na bane,kuma bansan yanda zan tukari ABBAN mu da wannan maganan ba saboda ya d'aura buri akan mu sosai kan cewa ko wacce sai tayi degree kamin yayi mana aure. Ga AUNTY KALTUM da take level 2 ma bata maganar aure bare ni da nake s.s 2? Nasan ranan da nayi maganan kashe ni kawai zaiyi".ta k'arasa hawaye yana gangaro mata.
" haba ki daina hawayen nan k'ona min zuciya suke, ni na tabbata ABBA naku bakomai yasa yace sai kun gama ba,nasan yana tsoron kar ayi auren Ku kasa cigaba da karatun Ku.amma abinda nake so ki gane ni ba zan hanki karatunki ba burina kawai inga na mallake ki nasan sauran mai sauki me".
Rasa abin cewa tayi saboda ita kanta ta matsu suyi auren ya nuna mata soyayyar da kullum sai ya gaya mata but tayaya zata tunkari ABBA shida tsayawan da take suyi hiran ma kullum sai ta sha suburbd'ab b***e ace taje da maganan aure tasan wannan rana yanka ta kawai zaiyi.
Shi kuwa ganin tayi shiru ta kasa magana yasa ya k'ara matsowa yace.." Da kinsan dad'in da yake cikin zamanta kewar aure da dakanki zaki ce na fito ayi auren amma sai gashi kullum ina miki maganan kina watsarwa koda yake nasan ba sona k**e ba shiyasa kika barni ina ta haukana kullum amma bakomai daga yau na daina miki zancen sai anjima"yace tare da juyawa zai bar wajan.
Da sauri ta sha gaban shi tana hawaye tace...Dan ALLAH ka tsaya ba haka nake nufi ba wallahi tsoro nake ji".
" kin tab'a ganin an had'a soyayya da tsoro? Haba karki bani kunya mana saboda masoyan asali basa saka tsoro a cikin soyayyar su kuma sune suke iya sadaukar da komai nasu saboda so".
Ganin ta daina kukan da take tana sauraron shi kuma da dukkan alamu maganar da yake tana shigarta yasa ya cigaba da karfafa mata guiwa.
"Bari in baki misali akaina ,ki dubi yanda malamin mu yake da zafi baya d'aukan raini,amma kina wucewa nake tashi nabi bayanki duk da taron d'alibai da suke jirana dan d'aukan karatu.kinga kuwa nima da in had'a tsoro da soyayyarki ban isa in tashi a wajan ba bare har in oya binki".
Saida ya numfasa sannan ya cigaba " misali na 2 ina son ki dubi banbancin da yake tsakani na dake, dubi arzikin gidan ku ki dube ni banida komai amma saboda ina matuk'ar sonki haka na tunkare ki da soyayya ta.har Allah yasa nayi nasara".
Haka yacigaba da kawo mata misalai shi bai barta ba har said a yaga ta samu confidence na tunkarar Abban nata sannan ya kyale ta.
Sallama s**ayi kan sai gobe kuma ta tabbatar tazo mishi da labari mai dad'i.
Hanyar gida ta k**a tana tafe ta imaging irin rayuwar da zasuyi it a da Shettee ta in har Abba ya yarda ya musu aure.kai dole ma ya yarda Dan bazata sake ya kara mata fushi ba.
Tana zuwa bakin tamfatsetsen gate d'in gidansu fuskar ta ya canza lokaci d'aya ganin mutane sai turuwan Shiga masallacin k'ofar gidan su suke saboda anyi Kiran sallar la'asar kuma hakan ya tabbatar mata da Abba ya dawo daga office kenan.
Tana tuna kalaman Nurul Qalbinta na cewa ba'a had'a tsoro da soyayya.
A take taji duk wani tsoro na cikin zuciyar ta ya kau saima wani k'warin guiwa da yazo mata lokaci daya kuma tana ganin in akan Shettee ne zata iya yin komai.
Bud'e k'aramin k'ofan tayi tare da shigewae ta cikin gida abinta.
[10/22, 4:09 PM] Ummee Yusuf
ππππ 1 π©ππ π 2 ππ¨π¦π’π§π ππ¨π¨π§