31/08/2026
KARANTA SAKON ATIKU ABUBAKAR AKAN BATUN HUTUN SHUGABA TINUBU A TURAI👇
Ku duba irin halin da Bola Tinubu yake barin Najeriya a ciki. Farashin man fetur ya wuce ƙarfin talaka. Iyalai na rage yawan abincin da suke saya saboda tsadar rayuwa. Kuɗin sufuri ya yi tsada har tafiya zuwa ƙauyen mutum ya zama kamar abin wahala. Rashin tsaro na ci gaba da jefa ‘yan Najeriya cikin makoki mako bayan mako.
A cikin irin wannan yanayi, Shugaba Tinubu ya shirya tafiya Turai na tsawon makonni uku.
Mataimakin Shugaban Ƙasa ma yana ƙasar waje bisa wata tafiyar aiki. Wannan ya sa matakin Shugaban Ƙasar ya ƙara zama abin tambaya. Jagoranci ba wai kawai haƙƙin zama a kan kujera ba ne, jagoranci yana nufin sanin lokacin da ƙasa ke buƙatar shugabanta ya kasance a gida.
Uba na iya yin tafiya idan komai yana tafiya lafiya. Amma idan gidansa yana ci da wuta, kuma iyalinsa suna cikin gidan, ba zai É—auki akwatinsa ya nufi filin jirgin sama ba.
Shi ne batun da muke magana a kai. Ba wai Shugaban Ƙasa bai kamata ya huta ko yin tafiya ba ne. Abin da ake magana a kai shi ne, Najeriya tana cikin matsala, amma Shugaban Ƙasar ya zaɓi tikitin jirgi maimakon kashe wutar.
Miliyoyin ‘yan Najeriya suna fama da tsananin ƙuncin rayuwa, yayin da Shugabansu yake shawagi a sararin samaniya. Jama’a ba sa iya samun kuɗin tafiya, amma Shugaban Ƙasar yana ci gaba da tafiye-tafiye.
Gwamnatin da ba ta jin raɗaɗin wahalar da take jefa al’ummarta ciki, amma ta kasa samun ƙarfin gwiwar kawo ƙarshen wannan wahala.
Tinubu ya mayar da Najeriya ƙasa mai tsadar rayuwa. Ni kuma zan sake mayar da Najeriya ƙasa mai sauƙin rayuwa. Insha Allahu. -AA