01/03/2026
G.M Usman Rabi'u Mahuta Ya Kaddamar Da Rabon Kayan Azumin Watan Ramadan Ga Marasa Karfi, Wanda Ya Hada Da Shinkafa, Gero, Masara Kimani Buhu 5000.
Shugaban gidauniyar (U.R.M Foundation) kuma babban manaja na kamafanin (Blue Camel Nigeria Limited) reshen jihar Katsina, G.M Usman Rabi'u Mahuta (Talban Dandume), ya kaddamar da rabon tallafin kayan azumin watan ramadan ga marassa karfi da masu bukata ta musamman, da shugabannin Jam'iyyar APC, wanda ya hada da Shinkafa buhu 1500 mai nauyi 45kg, Masara buhu 1500 mai nauyi 10kg Gero buhu 2000 mai nauyin 10kg.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a harabar makarantar firamaren garin Mahuta karamar hukumar Dandume jihar katsina a ranar Asabar 28 ga watan fabrairu, 2026.
A jawabin Mai garin mahuta Malam Sani Hamza ya yabawa mai girma gwamna Malam Dikko Umar Radda Phd, CON akan irin ayyukan da yake yi na raya kasa da kuma gina al'umma tun daga matakin akwatin zabe har zuwa matakin jiha babu inda aikin shi bai kaiba, ya kuma yi godiya da G.M Usman Mahuta akan irin yadda yake taimakon al'umma babu dare babu rana daga karshe ya rufe jawabin shi da zayyano kadan daga cikin ayyukan da gidauniyar tayi a fadin karamar hukumar Dandume irin su ayyukan raya kasa da kuma gina al'umma, taimakon marayu tare da marassa karfi.
Shi kuwa Kansilan Dantankari Hon. Salisu K.K fatan alkhairi yayi ga G.M, ya kuma yi kira ga sauran al'umma da suyi koyi da halin G.M.
A na shi jawabin shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Dandume Hon. Shafi'u Lawal Dantankari, Ya bayyana irin yadda G.M yake nuna kishin shi akan al'ummar karamar hukumar Dandume dama jiha baki daya, ya kuma yabawa Malam Dikko Umar Radda akan irin yadda ya ba sashen kiwon lafiya muhimmanci tun daga matakin kanannan asibitoci har zuwa manya da kuma yadda yake kokari wajen ganin an samu zaman lafiya a jihar katsina, ya kuma roki maigirma gwamna da ya kara rike masu G.M da kyau sakamakon mutum ne mai kishin al'ummar shi.
A nashi bangaren Wakilin matasan karamar hukumar Dandume, ya yabawa Talban akan irin kokarin da yake yi na tallafawa marasa karfi da marayu, ya kuma yi kira ga shugabanni da suyi adalci a tsakanin al'umma domin shugabanci abune mai wahala, ya taya sabon shugaban jam'iyyar karamar hukumar, ya kuma yabawa gwamna akan irin yadda yake kishin al'ummar katsina ta kudu dama jiha baki daya.
A jawabin Uban Taro G.M Usman Rabi'u, ya bayyana irin farin cikin shi da allah ya nuna mashi wannan rana da zai kaddamar da kayan azumi ga marassar karfi, ya kuma bayyana irin yadda ya ke yin ayyukan alkhairi akaramar hukumar ddm dukkananin abinda yake bayar wa na tallafi baya nuna banbanci a tsakanin al'umma.
Ya kuma bayyana irin yadda kan 'yan siyasar karamar hukumar Dandume ya ke a hade, bayan haka ya yi kira ga matasa da suyi koyi da ayyukan alkhairi kuma su rika yi ma kansu hisabi, ya kuma kara kira ga sauran al'umma akan ko yaya mutum ya samu dama ko ya take to yayi kokari ya tallafawa wanda baida shi.
Bayan haka ya kuma sake wani kiran ga matasa da su cire tsoro su shigo cikin siyasa adama da su, ya kuma fadi cewa "ko dan gidan mu ne kai idan baka son malam Dikko Radda to muma bamuson ka koda kuwa dan gidanmu ne kai", daga karshe ya rufe bayanin shi da kira ga matasa da su daina bangar siyasa.
Taron yasamu halartar Shugaban karamar hukumar Dandume, Shugabannin jam'iyyar Apc na karamar hukumar hukumar Dandume Alhaji Shafi'u Dantankari, wakilin katukan Katsina hakimin Dandume Shamsu Ibrahim Sambo, tsofaffafin shugabannin jama'iyyar Apc, sauran al'ummar gari maza da mata, jami'an tsaro, yan jarida.
Hotuna: Karaduwa Post