28/04/2026
Kashi na 1
Yadda zaka gane idan ƴan kajinka suna jin zafi ko sanyi (Amfani da Dabi'unsu)
Kaji suna magana da mu ta hanyar dabi'unsu. Ba lallai sai ka duba thermometer ba, kallo ɗaya zaka yi ka gane halin da suke ciki. Ga yadda zaka gane:
- Idann sun bazu ko'ina: Wannan shine abin da muke so. Idan ƴan kajinka suna wasa ko'ina, suna cin abinci da shan ruwa cikin nutsuwa, to zafin brooder ɗinka ya yi daidai!
-Idan sun taru ƙarƙashin hasken : Wannan alama ce da ke nuna suna jin sanyi. Idan kuma kana jin suna kukan rashin jin daɗi, to lallai ne ka rage hasken ko ka ƙara masa ƙarfi.
Idan suna guje wa Dumin/hasken : Idan sun matsa nesa da hasken kuma kana ganin suna numfashi da sauri (panting) ko sun shimfiɗa fukafukansu, to suna jin zafi. Wannan na iya kawo rashin ruwa a jiki, don haka ka ɗaga hasken sama ko ka rage zafinsa nan take.
-Idan suna taruwa a kusurwa : Idan suna matsa wa ƙusurwowin brooder ɗin, to akwai iska da ke shigarsu. Ko zafin ya yi daidai, iskar na iya sa su matse juna har su maƙure.
Me kake gani a brooder ɗinka yau?
mu hadu a comment section