10/08/2026
WAKILAN GOMBE TA KUDU SUN AMINCE DA FARFESA PANTAMI, SUN YI ALKAWARIN MARA MASA BAYA A TAKARAR GWAMNAN PDP
Ɗan takarar jam’iyyar PDP na Gwamnan Jihar Gombe, Professor Isa Ali Ibrahim Pantami, ya karɓi wata babbar tawaga daga ƙananan hukumomi huɗu na Gombe ta Kudu, wato Balanga, Billiri, Kaltungo da Shongom, a ranar Lahadi da ta gabata.
Tawagar ta ƙunshi ma’aikatan gwamnati, malamai, ’yan kasuwa da sauran manyan masu ruwa da tsaki daga yankin. Barr. Benjamin Sati ne ya shiya ganawar, yayin da Farfesa Obida Gobra W. ya jagoranci tawagar.
Tawagar ta bayyana amincewarta a hukumance da takarar Farfesa Pantami a zaɓen Gwamnan Jihar Gombe na shekarar 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
Da suke magana a madadin tawagar, shugabanninta sun ce abin da ya ja hankalinsu ga Farfesa Pantami shi ne tarihin ƙwarewarsa, amincinsa da kuma tsarin shugabancinsa mai tafiya da kowa da kowa.
Sun bayyana cewa Gombe ta Kudu a shirye take ta mara wa jagoran da ya himmatu wajen gudanar da mulki ba tare da nuna wariya ba, haɗa kan al’umma daga dukkan sassan jihar, tare da tabbatar da adalci wajen rabon damanmaki da ayyukan cigaba.
Tawagar ta kuma jaddada ƙwarewar Farfesa Pantami a hidimar jama’a da gudummawar da ya bayar a fannin tattalin arziki na zamani, ilimi, cigaban matasa da ƙarfafa mata, inda ta bayyana shi a matsayin wanda ya dace da jagorantar Jihar Gombe zuwa sabon mataki na cigaba.
A nasa jawabin, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya nuna godiya matuƙa bisa goyon baya da amincewar da aka yi da shi, tare da tabbatar wa tawagar cewa zai gudanar da mulki cikin adalci, gaskiya da kuma haɗa kan kowa idan Allah Ya bashi dama.
Ya ce gwamnatinsa za ta yi tafiya da kowa, tare da tabbatar da cewa dukkan sassan jihar sun samu wakilci da ci gaba cikin adalci.
Ya ce: “Ba za a samu Gombe ta Arewa, Gombe ta Tsakiya ko Gombe ta Kudu kawai ba. Gombe ɗaya ce kawai za ta kasance babu wani bambanci. Gombe ta Kudu za ta samu nata kaso na adalci wajen samun wakilci, ayyuka da naɗe-naɗe a ƙarƙashin gwamnatinmu.”
Farfesa Pantami ya kuma tabbatar wa tawagar cewa za a yi la’akari da mambobinta wajen shigar da su cikin kwamitin yaƙin neman zaɓe, yayin da mata za su samu fifiko wajen naɗe-naɗe, shirye-shiryen ƙarfafa su da kuma harkokin yanke shawara.
An kammala taron da addu’o’in neman zaman lafiya da haɗin kai, sannan aka ɗauki hoton bayan taro.
Sa hannu:
Professor Suleiman Muhammad
A madadin:
Ƙungiyar Pantamiyya
Daga Shafin:
Abba Sani Pantami