30/09/2025
Burin Rayuwa da Manufar Zamani
Idan ba ka da buri, bai kamata ka kasance a raye ba.
Domin rayuwa tana da ma’ana ne idan mutum yana da buri da kuma manufa da yake nema ya cimma.
ALLAH (SWT) ya halicci mutum da aljanu domin su bauta masa. Wannan shi ne babban dalilin samar da su, kuma ba zaɓi bane gare su – dole ne su bauta masa domin Shi kaɗai ya cancanci bauta, koda kuwa bai tanadi Aljanna ko Wuta ba.
Sai dai, bayan wannan babban dalili, ALLAH ya kuma ba ɗan Adam damar rayuwa a duniya da mu’amala da juna; ta hanyar kyautata zumunci, bayar da sadaka, da aikata alheri domin samun lada da ƙarin sakamako.
Bautar farilla dole ce ga kowa, amma ayyukan ƙari (nafila) ba dole bane. Duk da haka, wanda yake da burin samun daraja mafi girma a lahira, dole ya dage da ƙoƙari wajen ayyuka domin cimma burinsa.
A tsarin lahira:
Idan burinka samun sakamako mafi girma, sai ka dage da ibada da ayyukan alheri.
Idan burinka mutuwa da kalmar Shahada, dole ka kasance ma’abocin faɗin Lā ilāha illallāh tare da kyautata ayyuka.
A tsarin duniya:
Idan burinka kafi ƙarfin buƙatunka, dole ka nemi kuɗi domin cikar burinka.
Idan burinka yaƙi da jahilci, dole ka nemi ilimi.
Idan burinka jarumtaka, sai ka koyi salon iya yaƙi.
Idan burinka samar da aikin yi, sai ka gina kamfani.
Idan burinka samun mace tagari, sai ka nemi mace mai addini.
Daga haka za mu gane cewa duk ɗan Adam mai hankali yana rayuwa ne da wani buri ko manufa: kodai na kuɗi, ko na ilimi, ko na mulki, ko kasuwanci, ko jarumta. Kuma duk wanda baya da wannan dabi’a ta neman buri mai amfani, rayuwarsa bata da ma’ana – ya rayu a banza ne.
Saboda haka, buri shi ne ginshiƙin rayuwa. Shi ke sa mutum ya dage, ya yi haƙuri, ya yi ƙoƙari, ya nemi ilimi, ya yi kasuwanci, ya yi ibada, ya yi alheri, kuma ya bar tarihi mai kyau bayan ya bar duniya.
ALLAH ya cika mana burikanmu na alheri, ya kuma kyautata ƙarshenmu da alkhairi.