24/11/2023
Part 2:
Within 10 mins nagama donating dayake inada poor clotting factors (wato jinina a tsinke yake - kaman ace kunune dakuma surki...to nawan shine surki...lol).
Nakira matana dan tazo ta dan riqeni nasamu karfin kaiwa jinina dana bawa pt dina in case zanji jiri ko kasala, amma to my surprise nama riga isa kaiwa jinin while matana is following me. Alhamdulillah na isa Mrs. Ajidike Lovelyn Chichi tayi hanging wa Mrs. H jinin, while nikuma nadawo nayi few other documentations dakuma final rounds wa sauran patients dina kafun na tafi gida (Daman kullum nakanyi ward rounds sau biyu a Ni'ima dan naji complain dakuma improvement / new complaint) kafun hankalina ya kwanta natafi gida, haka mahaifina Dr. Bello shima yakeyi har yarasu).
So nida matana da Mrs. Lovelyn munata hira sena dan fara jin jiri jiri amma kadan kadan, cikin wasa nace musu kaaaiiii...kode zaku maidamun jini na ne...lol...sukace a'a nabar sauran aikin naje gida naci abinci nayi bacci. Ba wani bata lokaci nayi sallama da asibiti na wuce gida mukaci abinci da matana.
So, nayi last spoon dinane fa se jirin ya karu SOSAI, nazamo very restless, ni ban suma ba ni gani amma babu kanta. Habaaa akayi maza maza aka dauko wheel chair (dayake ina hospital quarters da zama) segani peeeee ana turani...lol...that was 9:45pm haka or so. Isana nasamu already Mrs. Lovelyn and her team suna jira su bani gado dayake already nasa matana takirasu awaya. Bawani bata lokaci akayi canulating dina akafara serving fluids very very fast da dan allurai.
My first question was ya jikin Mrs. H, sukace she is fine. Knowing cewa in shaa Allah nasan ko banyi surviving ba at least I have saved her (after all gangan cina da rashin kulana ne yasa tashiga halin da tashiga).
So alhamdulillah natashi abacci yaw Sun 19th Nov, nayi sallana, kuma banajin jiri ko wani kasala. Mrs. Lovelyn tacemun itama pt ta miqe da kafanta (from wheelchair) and we are both EXCELLENT.
Nagama drip dina na safe kuma in shaa Allah nanda few mins zanfara aiki