Achi dariya

Achi dariya Hahaha you have made me Laugh

26/12/2025

لا اله الاالله .. محمد رسو ل الله ..
الهم صل عل سيدين محمد، والي سيدين محمد ..

26/12/2025

Allah ka haɗa mu da babban rabo 🙏

26/12/2025

Assalamu alaik*m!
Ƴan uwa barkan mu da juma'a

22/11/2025

Assalamu alaik*m!!
Ya ƴan uwa musulmi a yanzu fa mun fara shiga halin da sai mun tashi tsaye da addu'a, domin wallahi ƙasar mu na fuskantar mummunan bara zana, allah ka cigaba da kare musulmi da musulunci amin 🙏😓

03/05/2020

Assalamu alai k*m, barkan mu da shan ruwa, a madadin daukacin members din wannan page mai al-barka ina mai roqon allah s.w.a da ya qar6i ibadun mu, ya k*ma yafe mana zunuban mu. Ameen

20/02/2017

TRUE LIFE STORY
LABARI NA PART (3)
Dajin muryar nazir batayi mamakin abinda yake faruwa ba, domin tasan zasu aikata abinda yafi hak**a, sai tace don allah ku kyale shi bai ci abinci ba na tabbata yanxu yunwa yake ji, alokacin da tazo nan a zancen ta sai s**a kwashe da daria, anan nazir ya gaya mata cewa ta kwantar da hankalin ta yanzun nan zamu tafi kuci gaba da soyewar ku ya kara da cewa ta kular musu da abokin su domin basa son abinda zai ta6a mishi rai, nan take nazir ya kashe wayar tareda cewa kutashi mu tafi dare ya soma yi, sai anan na samu nai magana bayan sunce saida safe nace allah ya kaimu, daga nan na kira ta muka ci abinci ba yan mun gama firar mu irin ta masoya sai tace bacchi take ji, anan mukai addu'ar kwanciya bacchi nace mata sai da safe tare da cewa ta kular min da kanta, washe gari misalin karfe 5:00am sai ga kiran ta a waya tace natashi nayi sallah, yau kan tare muka tafi makaranta kasancewar kowa yasan halin da muke ciki soyayyar mu ta baza gari kowa sha'awar mu yake kullum muna tare sai kwatancen mu ake tamkar wata da zara, haka rayuwa tai ta tafiya gwanin ban sha'awa, wata rana misalin karfe 6:00pm saiga kiran ta, mun dade muna fira sosai don har sai da akai kiran sallar magriba tukunna nace mata lokacin sallah yayi muje muyi sallah in anjima madora daga inda muka tsaya, bayan munyi sallar magriba bata kira ni ba nima k*ma ban kira taba har lokacin sallar isha yayi bayan mun idar da sallar ne tun daga masallaci ban tsaya ko ina ba sai a kofar gidan su, anan nayi mata waya nace gani a kofar gida, ba tare da 6ata lokaci ba ta fito mun dade muna fira misalin karfe 9:45pm nace mata dare yasoma ma yi haka muka tashi uwa baza mu rabuba, bayan na dawo gida sai ta kira ni a waya har misalin karfe 12:00am muna waya a nan tace tana jin bacchi mukai addu'ar kwanciya bacchi, mukai sallama sai da safe, washe gari da safe yau kan na makara a lokacin dana farka rana tayi sosai babu abinda na fara nema sai waya ta domin a tunanina takira ni taji shiru saboda bacchi yamin kamun kazar kuku, abin mamaki yau bata kirani ba a tunanina itama ta makara ne domin jiya bamuyi bacchi da wuri ba sai na kira wayar ta ikon allah wayar a rufe take, yau ya tabar wayar ta a rufe ko babu charji ne? na fada cikin raina domin ban ta6a kiran wayar ta naji a rufe ba bayan na tashi nayi sallah yau kan babu makaranta wannan shine dalilin da yasa na shirya na tafi wajen aiki, abin mamaki har yanxu wayar ta a rufe hankalina ya kasa kwanciya zuciyata ta kasa samun sukuni, bayan na isa wajen aiki sai na sake kiran ta still a rufe,

20/01/2017

TRUE LIFE STORY
LABARI NA PART 2
idan zamu tafi makaranta da safe kuwa sai mun kirawo juna munyiwa kanmu fatan dawowa lafiya tare da yiwa kanmu alkawarin cewa bazan kula wata ba itama k*ma bazata kula wani ba, haka rayuwar mu taita tafiya cikin farin ciki, babu yaudara babu ha'inci sannan babu ganin kyashi, a kwana a tashi duk abinda ka tona ka binne to wataran sai yafito, abinda nake nufi anan shine sirrin da muka boye aranmu ya fito fili, watarana wani abokina ya sameni da zimmar na ara mishi littafina na geograpy zaiyi assigment sai na fada mishi cewa yaje cikin jakar makaranta ta ya dauka, bayan ya dauka ne da yan wasu awanni alokacin da naje duba hotunan muradin raina sai na nemesu na rasa, bayan na birkice ko ina bangan suba sai na tsaya na zurfafa tunanina ana na gano cewa hotunan suna cikin littafin geograpy'n dana arawa abokinnan nawa, a take na ciro waya na kirawo muradin raina na gaya mata abinda yake faruwa, anan naji taja wani dogon ninfashi domin tasan abinda muka dade muna boyewa yau ya fito fili, dan tasan abokinnan nawa ciki da bai mutum ne mai shegen surutu, dan yana daya daga cikin wa'yanda suke bibiyata akan dole sai na gaya musu wacece budurwata, anan na gaya mata cewa kawai mufito mu nunawa duniya cewa soyayya muke, domin tunda abokin nan nawa ya sani tofa babu wanda bazai sani ba, anan mukai sallama na kashe wayar, bayan yan wasu lokuta sai naji hayaniyar mutane da alama dakina suke shirin shigowa, kafin na yunkura na fita don ganin abinda yake faruwa har sun shigo dakinnawa, abokanaina ne susu biyar ciki harda abokinnan nawa wanda ya zo ya'ari littafin geograpy na yana rike da hohunan a hannun sa, kafin nace wani abu sai umar yace haba abokina yanzu dan kana soyayya da wance sai ka boye mana? Abubakar kuwa cewa yayi ai dama biri yayi k**a da mutum domin a kwai lokacin da muna zaune a majalissa da tazo wucewa naga tana mishi wani irin kallo shik*ma yana murmushi to tun alokacin naso na fahimci wani abu, zaharaddin kuwa cewa yayi agaskiya abokina ka iya takunka domin halaiyar yan unguwannan nan sai da haka, toni abin mamakin ma shine tayaya suke haduwa har suke soyewa domin babu wanda ya taba ganin su inji nazir, aliyu yace kai inbanda abunka ai ta waya suke soyewa, muna cikin wannan haline sai wayata tai ringing ina duba screem din wayar sai naga muradin raina ce take kira, nan take nazir ya shamma ceni ya fisge wayar hahaha itace take kiran shi, ya daga tare da cewa ranki ya dade

20/01/2017

TRUE LIFE STORY
LABARI NA
Part 1
Dani da masoyiya ta munso junan mu uwa bazamu rabuba,
hakika inasonta har cikin zuchiya ta, haka zalika itama tana sona sosai da sosai, mun fara soyayyar mu babu wanda ya sani, kasancewar kusan layinmu daya, babu dare babu rana kullum muna tare, amma a waya domin soyayyar tamu ta basaja ce, dalili kuwa shine ra'ayinmu yazo daya,
ra'ayinmu shine matasan layinmu sunada wata dabi'a, idan har akasan dawadda kake soyayya ko akasan sunan ta, to sunan ta zai koma naka, nata k*ma zai koma nata, babu wanda bazai san wance budurwar wane bane, mu k*ma anamu tunanin sai muke ganin hakan ba daidai bane, shi yasa muka yanke shawarar boye sirrin mu, domin afili idan muka hadu babu wanda zai ce akwai wata alaka a tsakanina da ita, domin bama yiwa juna magana saboda tsaro, amma idan muka hadu daga ni sai ita uwa ma chinye junan mu, haka rayuwar soyayyar mu taita tafiya gwanin ban sha'awa, bamuda aiki sai na waya, domin bazai taba yuwuwa minti talatin tazo tawuce batareda daya yayiwa daya waya ba, a kullum zaka ganni ina waya amma baka isa kasan da wanda nake wayar ba, haka itama a cikin kawayen ta yake faruwa babu wanda ya san da wanda take waya, mutane suna min kallon wanda ya ke burga da waya, domin kowa yanamin kallon cewa aduk lokachin da nake waya tofa karya nakeyi, kawai dai na kara wayar ne akunnena don na burge mutane sudauka cewa waya nakeyi, domin aduk sanda zaka ganni hannuna yana kan kunnena alamar cewa waya nakeyi, haka mutane s**ai ta karyata ni, domin yin wayan nawa yawuce misali, wani lokachin ko abinci nakeci tofa waya nakan kunnena, saboda akoda yaushe tare muke cin abinci, nasan mai karatu zaiyi mamakin cewa tayaya za'ayi abinci yaciwu ta wayar selula? Hmmm to bari kaji yadda mukeyi, idan na dakko abinci na saka a gabana sai na cemata itama ta dakko idan nayi cokali daya sai nace mata itama tayi, to kaji ta yadda muke cin abinci a waya tare, a kullum idan zamu kwanta bacci sai mun kirawo juna a waya munyi sallama sannan muyi addu'ar kwanciya bacci, da safe kuwa idan na rigata tashi zan kirata na gayamata cewa gari ya waye, haka zalika itama idan ta rigani tashi zata kirawo ni, idan azumi ya zo wani lokachin ita take tashina natafi tuhajjid, ni k*ma idan nadawo sai na tasheta muyi sahur

05/06/2016

The family of alhaji dabino and hajiya banana,watermelo,hon.kosai,barister kunu,hajiya pertetoz,malam orange,mr.egg,senator maggi,engineer tea nd brd
Are saying RAMADAN KAREEMM
Daga

05/06/2016

GWAURO! GWAURO! GWAURO!
Mai sahurda qarago hahaha
Ina kira da duk admin da sauran members din wannan page da su tashi sutsaya domin naji hajiya rice na cewa tafi karfin dukkan wani karamin magidanci a fadi nigeria ballan ta na gwauro aban garen garin kwaki kuwa yace babu wani gwauro da ya isa ya cishi sau biyu wato idan aka sha ruwa ya shashi san nan k*ma yayi sahur da shi yace sam haka ba zai wuyu ba
Nikam
Nariga da na shiryawa yaqar shin kafa da chokali

Address

Unguwa Uku Quoters
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Achi dariya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share