30/12/2022
BAKIN DA ALLAH YA TSAGA
"Tsananin Talauci d kuma wahalar rayuwa ta sanya wata tsohuwa shiga gidan Talabijin domin neman taimako.
Wani Mulhidi (Shugaban wani babban kamfani) ya ji wannan sanarwar, sai ya ce a ransa, bari na yiwa wannan dattijuwar izgili tun da musulma ce.
Ya kira sakatariyarsa y bata kuɗi masu yawa, ya ce duk ababan da tsohuwar nan take buƙata ki saya kuma ki ƙara mata har da wasu abubuwan da bata nema ba na buƙatun yau da kullum ki kaimata. Na san in ta gani zata yi mamaki sosai, zata tambaye ki waye ya aiko mata d wannan saƙon haka, ke kuma sai ki ce "SHEƊAN NE YA AIKO MATA DA SU"....!
Bayan Sakatariya ta kai saƙo, tsohuwa ta yi farin ciki sosai kuma ta yi murna...Sakatariya ta yunƙura don ta tafi, sai ta kalli dattijuwa ta ce, ba zaki tambayi waye ya aiko miki da waɗannan kayan haka ba...?
Ta ce bana buƙata, in Allah ya yi nufin cikawa bawa burinsa; hatta Sheɗanu biyayya suke yi masa, basu da zabi face zartar da al'amarin Ubangiji.....!"
Daga Shafin Sukairaj.