Hamisha novels

Hamisha novels Welcome to hamisha novels

30/07/2020

SIRRIN ZUCI​........​

💞

Na Feedohm💞

1 to 2

البسم الله الرحمن الر حپم

Lumshe Ido yayi sannan ya budesu tar bisa kan wata karamar yarinya dake zanen yar galala ....

Fito yayi da bakinsa a hankali ....da sauri yarinyar ta kallo sama tana murmushi tare tsalle tana daga mashi hannu ...

Iska ya huro mata ...sannan ya daga mata hannu ....itama hannun ta daga mashi ....

Wata tsohuwa ta fito daga wani karamin gida wanda duk unguwar babu talaka sama dasu ....

Meenalle ...Meenalle. ..ta fara kwada kira ....

Yar karamar yarinyar ta juyo da sauri tana bata fuska ...cikin shagwaba tace .....Kai kaka ke kullun sae ki batawa mutun suna ...nasha fada maki Meenal fa ake cewa? ...

tsohuwar tace ...to naji sarkin hakuri zo muje ki sayo mana kwaki ko bakijin yunwa?

Saman benen ta kalla. ..har yanzu yana tsaye ita yake kallo ...daga mashi hannu tayi tare da langwashe kai ...sannan taja hannu tsohuwar s**a koma gida ....

Kudin ta karbo sannan ta sako hijab ta fito ...tana zuwa bakin kofa taja birki tare da dafe kirji ....hal ka ban tsoro ...ta fada hakoranta waje ...

Hararanta yayi...ke kuma sarkin tsoro ko ...ya fada yana gyara mata hijab dinta ...

Kai ...aikena fa akayi ...ta fada tana neman cire agogon dake makale a hannunsa ...

Hannunsa ya janye don karta bata mashi...sannan yace ...Me zaki sawo?

Baki ta tabe tana kokarin wucewa sannan tace ...kaini Kaka tace kabar sawo man komae ..wae ku yan yankar kaine ...kuma tace wae kaina zayayi tsada ...

Dariya ya sake a hankali kafin yace mata. ..ni kuma kakata tace man indae mace na yawo to kasa ake rufeta ...ya fada idonsa na kallonta ...

Ido ta waro cike da tsoro ...da gaske Mai kamshi?

Ganin ta tsorota ya saka yace ..eh mana ai bana so a rufeki shiyasa ma nace ki fada man in sawo maki ...

Kamar jira take ya rufe baki tayi saurin mika mashi naira hamsin din da ta gama nannadewa ...

Amsa yayi ..yace me zaa sawo. ..

Kwaki na talatin sae s**ari na ashirin ...ta fada a hankali ..

kai ya girgiza kana ya tafi. ..har yayi nisa ta kwala mashi kira...ya juyo. .tace ...Dan Allah kace a maka arha ..kuma kayi sauri kar kaka tace na dade ...

Kai ya daga mata sannan ya tafi ..

Baifi minti goma ba ya dawo rike da manyan ledoji. ..tana hangoshi ta tareshi tana dariya ...

Duka ledojin ya mika mata ya juya ...tayi saurin janyo hannunsa ..to ka tsaya mana na duba inda canji ba sae ka bani ba ...ta fada tana bata rai ..

Dariya ta bashi sossae ..ya dawo s**a shiga zauren gidan ...

Zama tayi kasa ta zazzage kayan tsaf ...ido ta waro lokacin da ta daga katon gwangwanin madara ..tace ...Nawa ka sayo wannan ...ta fada tana kallonsa ..

Naira biyar ...ya ce idonsa yana kallon karamin bakinta ...

Uhmm saura arba'in da biyar kenan ta fada ...biscuit ta cigaba da fitowa da chocolate sae ledar cos cos da sugar sae lemuka kala kala ...duk wanda ta daga sae ta tambayeshu kudinsa ...daga wanda zayace biyu biyar sae na biyar ....har ta fito da tiyar garin kwaki ...

Wannan nawa yake? ...

Kura mata ido yayi ..sannan yace ...wannan a shagon wani abokina ya bani su ...

Dariya tayi kana ta maida kayan tana kallonsa ...to bani canjina ...ta fada lokacin da ta gama maida kayan ...

Ido ya waro ...wane irin canji kuma?

Harara ta balla mashi ...sha biyar mana. .ba yanzu mukayi lissafi ba naira Talatin da biyar ka kashe ...

Murmushi yayi ..ya lalubi ajihunsa ...babu ko naira 500 bare kananan canji. ..

dubu daya ya mika mata ...ta make kafada ...ni canjina zaka bani ....ta fada a shagwabe

Dukawa yayi dae dae tsawonta ....kiyi hakuri Meenatou ...banda canji...kinji. ki bari anjima zanyi canji sae na baki ....

aa Ni dae ban yarda ba ....muje a canzo su ...ta fada. .

To naji shiga da kayan sae ki fito muje. ...ya fada idonshi a lumshe ...

Ka gudar man da canji ...tace

Hannunta ya kamo ...baran gudu ba ....ya fada har lokacib idonshi a rufe ...

Shiga gidan tayi tana waigenshi ...aje kayan tayi ta fito da gudu ...kaka nata kiranta. ..amma ce mata tayi ....Kaka Kawata ta mutu ake kiranmu muyi mata addua ....

​Feedohm💞

01/12/2019

Ibrahim Hamisu



5 minutes ago

WALLETWITHDRAWProfilePostsSettings

wallet

Your Referral Link:

24/08/2019

Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠

Page 3-4
By
Gentle lady💃🏽

Sai bayan fitar" labila sannan hajiya lubabatu tasamu tashiga wanka ganin duk jikin kawayen nata yayi sanyi da maganganun da labilar tafadamasu yarinya tamkar banice nahaifeta ba sam bataganin mutuncina
Tayi kwabaa

Batajima dashiga wankaba tafito tasheka kwalliya tamkar wacce zataje gasar sarauniyar kyau" ta chanchade cikin wani tsadadden bugaggen less dan ubansu akalla kudinsa zas**ai dubu dari da hamsin""
Tasaka sarkar diamond hannunta yasha awarwaraye na gwal"" nantake tasoma shekii tashi s**ayi dukansu s**a fara zaga gidan duk indas**a wurga sai anjinjinawa kwalliyarta nikuwa araina nace wato yangulma kikewa kwalliya illai kuwa kwalliya tabiya kudin sabulu dankuwa tayankesu kowacce takoma gidansu tana Allahummar zukuni""

Wani abun saigidan manya bakuga yanda akasoma fitowa dakayan ciye ciyeba bikin gidan masu kudi ko ba agayyacekaba kaje kodakuwa ba asakarmaka fuskaba kakwaso gara""
Dankuwa yanda akacika gidan kaima dagani kasan wadansu abincin kawaine yakaisu "" babujimawa akafara fitoda dakwalen kajiii dakuma babba kakkun raguna masu maiko"" anyimasu gashi Na musamman sunsha shafen barkono saizubarda mai sukeyi saikuma lemuna namanyan mutane wanidinma bantaba ganin irinshiba

Kowa kaganshi rabonsa yake yaga"" masu DJ ne s**afara sakin kidaa bayan suncika tunbinsu""" hajiya lubabatu ce tafara takarawa cikin murna kaikace ba itah za ayiwa kishiyaba babuwanda bata burgeba wasuma sunata rokon Allah yabasu uwargida maihalinta Sam batadauki kishi abakin komaiba

Kai ranarfa tasha rawa nikam nace jikinki zaiyi ciwo kuwa""duk wannan bidirinda akeyi banga ma mallakin gidanba""

Yinin ranarfa sunchashe son ransu DJ yakwashi kudii wadanda akaita masu likidasu kasan biki na kusoshin yan duniya wadanda s**arika

Shigar hajiya lubabu goma kowacce shigarkuma saiwanda yaganie komai kuma kalar kayan" anzuba hotona"" magrib tana kawojiki kowa yafara haramar barin gidan"" daki s**a sake kowama"" suna nan kowadai saifadin albarkacin bakinsa yakeyi

Karfe takwas mukafarajin dirar motocin amaryaa"" sunata rangada gudaa"" akashigo da itah"" zuwa bangaren uwargida s**ashiga da sallama ta amsa dasakin fuska marabanku lale marhabin kuzazzauna mana""
Daga kawayenta harmasu kawo Amarya bakisake suke kallonta sambatada bakinciki taja hannun amaryar tace zo Kanwata kizauna nan"" cikin jinkunya"" tazauna kanta yanakasa ayanda akebata labarin matarsa babu ruwanta ashema tafiyanda akabata labari""
Take tamike tafara jidomasu kayan makulashe dakuma kayan sha"" da gasassun naman kajie"" bayan sungaisa s**ace ga amanar kanwarkinan munkawo maki
Duk dakowa yana shaidunki bakida wata illah Dan Allah kiyi hakuri dahalin kuruciyarta dan kingirmeta nesa bakusaba idan tayi badaidaiba kiyimata fada""
Tayi murmushi aibakomai abokin zama dadine dashi tadafa kafadarta"" Kanwata nandin kidauka gidane komai yashigemaki duhu karkiji shakkar komai kisanardani nikuma zanwayarmaki dakai

Allah yasa nandin gidan zamankine Allah kuma yasa ace karada akayi Allah yabamu zaman lafiya"" gabadaya aka amsa da amin""
Mikewa s**ayi tace yabazaku taba koda ruwabane ai anzama daya nibazanji dadi idankuka kicin komaiba nima idan nazowajenku tareda Kanwata aibazakuji dadiba idan nakishan koda ruwane

S**ace tayi hakuri akoshe suke ganin tamatsa yasaka s**adan kurba lemun"" tareda itah akafita zuwa bangaren Amarya """ harkuryar dakin tazaunarda itah yanganin daki Duk suncika dakin"" sunfara tabe tabe"" hajiya lubu tasoma miyarmata"" dakayanda akasoma turewa tadade taredasu sannan tayimasu sallama takoma wajen kawayenta indasuma sunsoma haramar komawa gidan mazajensu"""

Tahadamasu shatara Na arziki tarakasu kowacce tak**a hanyar gidanta"" bangarenta takoma"" hawa na uku shine Nata nabiyu na Amarya maigidan shine hawana karshe""

Idanzakije bangarensa Mahayar Na ura zakishiga kidanna zuwa sama bàsàikin wahalda kanki wajen taka matakalaba

Tanashiga bangarenta tarage kayan jikinta tahaye saman makeken gadonta tasoma sharar barciii hardà minsharii hankalinta kwancee saijuyi takeyi sànyin Ac yanashigarta tako ina"""

Gabadaya gidan anwatse kowayatafi yana yabon lubabatu da kyawawan halayenta"" karfe shadaya motarsa tashigo gidan"" bayan driver yayi fkng yayi saurin fitowa yabudemàsaa kofaa

Yafito"" yacewa driver n ina" habu driver dubamun kagani nayita kiran"" wayarsa batashiga labila kuma bata dauki wayarba

Yadan gurfana dasaurii yayi hanyar dakinsu yanakwala masa kirah haryasoma barcii yaji anakiransa firgigit yamike yafito dasaurii tares**a koma wajen alhajin""

24/08/2019

Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
+2347039625239

☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠

Page 1-2
By
Gentle Lady💃🏽

Dasunan Allah mai rahma maijinkai"" dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki maikowa mai komai ina kara godiya ga Allah subhanahu wata ala "" Wanda yabani ikon fara wannan labarin Allah yasa jama a zasu amfana da fadakar wardake cikinsa

Hakika komai kaga yasamu bawa mukaddarine daga Allah Amman kuma akwai sanadi wannan labarin kirkirarren labarine nayishi domin tsokaci dawadansu abubuwa dasuke faruwa acikin al umma""

Wacce wannan labarin yaxo daidai darayuwarta saita tuba tadaina domin ganin makomar Wanda yake kwatankwacin irin halintaa Allah yasa mudace Ameen

Wannan labarin narubutashine ra ayin kaina danhaka Wanda yaji zai iyah karantawa banhanashiba saidai kuma akiyaye karwani ya sarrafamun sh*tawata hanyaa idan kunne yaji gangar jiki tatsirah

*BISMILLAH*

***********************
Gabadaya unguwar cinkushe take da manyan motoci sai kaikawo sukeyi alamu sun nuna wani mihimnin buki akeyi na wani kasurgumin maikudii Dan la akari da yawan motocin dasuketa karakaina hakazalika masu tsadar gaske kaima kasan ba bikin"" fukara"u bane

Bakin kofar gidan tacika makill da maroka dakuma masu kidaa"" ahakan nasamu tattakawa zuwa kofar gidan duk da dakyar nasamu nakai wajen asheni banga jama a ba dankuwa cikin gidan tamkar anabikin nadin sarautane""

Sai rarraba ido nakeyi domin samun hanyar shiga wannan katafaren gidan ginane namusamman maihawa hudu anyimasa fentiii da farin fentiii maishegen kyau da shekiii wannan gidan kusan yafi kowanne gida kyau dakuma tsari gabadaya ya haskaka unguwar anayiwa gidan nan lakabida farin gidaa!! Tofa Allah yasa abunda yakecikinsafarine🠽򢠊
Kutsa kaina nayi Cikin gidan kofar shigama abar adubace""nagama zagayena nikam banga alamar matar gidan ba"" dankuwa irin wannan gidan yak**ata ace matar gidan ta banbantaa dayanbukiii ajikinta kadai za agane""

Nayi zugum inabinsu dakallo nace tomezaihana insaurari firarsu watakil nagane matar gidan aciki🤔 wannna shawarar nayarda da itah nafarabi lungu dasako ina saurare abun takaici abun bakinciki duk inda nawulga zancensu kusan dayane kishiyaaa!!!!

Waimenene illar kishiyane??? Kumata kunada abun mamaki idan mijinku ya aureku yace zaikara aure kuyita fitinaa toyakenan idankuma keza a aura??? Itakuma matarsa taceme??? Yak**ata zuwa yanxu mata sugane Susan kalar kishinda zasuyi kuyi koyi da matan Manzon Allah (S A W) suma sunada kishi saidai nasu sunayinsane abisa tsari kowacce tanarigengen wajen kyautata masa domin tasamu matsayi fiye Dana dayar

Amman wasufa saboda tsabar bala.i da masifa daga ranarda yasoma maganar kara aure tofa ya ballowa kansa likii zatadaina wanka tabar dafamasa abincii wata hatta gadonta baxata barshi yakwantaba dazaran yace yimun kaza tace bazanyiba kajecen wajen amaryarka taimaka tabar yayanta acikin wahala waifa a irintata wautar waita naso tazubawa mijin haushine shikuwa dayafita iyawa saiyabuge iskanta yayima dadai duniya k**arma baisan da zamantaba sai idan tayi masifar tagababuci kuma biki yanata karatowa sai afara yangyare gyare waidaga bayakenan sadaka da bajawara bayan kinzubarda girmanki kimarki darajarki

Bari nabaku wani sirri wlh idan mijinki zaiyi aure kika kwantarda hankalinki zakici arziki komai kikeso zaiyimaki domin yataushi zuciyarki kuma zai rika tambayarki menene kikeso haka zalika komai zaiyiwa amaryar zairika neman sha wararki"" sabanin idan kikasoma fitina zaiyibanza dake duk wuyartadai kece akasa bazaki hanashi auren ba

Saikiyi ba1 ba 2. Darajarki dayake gani kinbata bazaisake yarda dakeba kuma koda amaryar tashigo gidan akatada fitina kodakuwa kece mai gaskiya bazai yardaba zaice aiyaga take takenki tunkamin yayi aure kiketa fitina tosaidai kiyi abunda zakiyi matadai matar sace matsayinku daya awajesa uwargida kinga mutuncinki yaragu

Idan kikacigaba da fitina karshenta yasakeki yazauna da amaryarsa wagari yawaya???? Hakan yana faruwa sosai acikin al.umma

Iyayena mata iyayen gobe mukula mukiyaye kishii ba haukabane!!!

Nafara biyar lungu dasako cen saman hawa na uku nayi katari da matar gidan "" sosai nafirgita daganinta sam bazaka taba cewa matar gidan bace"" irin matan nan ne wadan da mazajensu suke dakudi amman idan kagansu bazaka siyesu kwandalaba duk kayanda suke siyamasu basa sakawa idan kagansu mai aikinsuma tafisu daraja amman fa idan zasuje gidan bukii kokuwa zasuje unguwa zakadauka basason taka kasa saboda tsabar tsafta""

Abokananta dasuke gefenta dayar tace wai lubabatu mezaihana kitashi kiyi wanka gidan nanfa yanbiki sunfara cikashi kosokike araina class nakii
Wacce take gefenta nadama tace hajiya larai kibarta hakan mana"" dame zataji dakishiyarda akai mata kokuma da kwachakwaimar kwalliya?? Kinsan Allah danice kotaron biki bazanyiba

Wata tace habadai hajiya larai aiyanzu andaina wannan yayin idan za akawomaka kishiya kahana kanka jindadin rayuwa yanxu kissa akeyi kikwantarda kai tamkar mumina ni wlh mijina yayi aure saina gasawa amaryar gyada ahannunta

S**a kwashe da dariya haryanzu uwargidan uwar iko batayi maganaba"""
Larai tace hajiya sadiya kenan ashe wacce tsautsayi yasaka tashigo gonarki zatafi gwammacewa kwana akabarintaa" s**a sake shekewa da dariya"" amman banda itah""

Haba kukuwa banda abinku ai kishiya abokiyar zamace menene abunkishin??? Abunda akasaba bakifa badainawa za ayiba nisam banajin kodar akan auren nan
Hajia lubabatu ce mai wannan maganar""

Hajia larai tarike haba lallai hajiya kodayake wannan bashine nafarkoba bakyada jinkomai nikam wlh bazan sakewa mijina fuskaba dahar zaiyi sha awar karawani auren"" tirkashi ranarkuwa dahakan tafaru wlh sai yayi zaton aturu aka kwantoni dan zankoma masa mahaukaciyar karfi dayajii

Wannan karon harda hajiya lubabatu wajen dariya wata matashiyar budurwace tabude kofarda sallama""" s**abita dakallo babu wanda ya amsa tafara kallon mutanen dasuke cikin dakin daga bisani tadauke kanta k**ar taga kashi
Hajiya lubabatu ce ta daka mata tsawa ke wacce irin shashashar yarinyace labila???? Zakishigo wamutane daki haka bakiganin bakine dani??? Baki tatabe nagansu mana mom kuma ainayi sallama "" takai karshen maganar tanasake wurgamasu mugun kallo ta murguda bakiii
Kinyi sallama gidanwa mu kuramene dabamujiba"" ta kwabe fuska to tayazakuji bayan kuna tazuba shegen surutu wanda bazai kareku dakomai ba""
Ido lubabatu tazaro s**am su hajia larai inda sabo yaci acesun saba dahalin labeela"" tace labila waiyaushe kikazama tsagera nifa mahaifiyarkice kinamun magana tarashin da a

Tasake mere baki"" tacee malamai niku gyara zanduba jakata "" tayi maganar tana rike kunkumi afusace hajia lubabatu tasauko daniyar dukanta su hajiya sadiya s**ariiketa haba hajia baidace kidaketaba ai labila karamar yarinyace kuruciya ce take damunta

Kotakansu batabiba tahauduba jakarta"" tadauko sannan takallesu daibayan daya tace naji kuruciya tana damuna amman karani saudubu daku sakarkarun mataa mstw tsaki taja tafita tabar dakin

Gabadaya dakin yayi tsit bakajin motsin komai saina saukewar ajiyar zuciyarasu" labila karamar yarinya amman kullum tasamesu agidan saita soka masu miyagun maganganu

Dasauri tasauko kasan tana rike dajakarta"" sai kutsawa takeyi cikin taron mutane ranta yayi matukar kuna bataso mahaifiyarta tana hulda da wadan nan matan saboda dukansu babu Allah azuciyarsu amman mahaifiyarta batada wasu shakikan abokai bayansu
Wayarta tajawo takamo wata nomber tadanna kirah babu jimawa akadauka"" tayi sallama ya amsa dad dan Allah katuro driver yamiyar dani bazan iyah zama anandinba!!

Ajiyar zuciya yasaukar yace saboda menene labila bazakijirah akawo antyn takiba cikin sauri tagirgiza kai no dady"" dagabaya zandawo inganta yanzu akwai muhimmancin tafiyar tawa gobe munada harda a islamiyya"" amman inshaa Allah idan komai ya daidaita zandawo naga mom din kafin lokacin tazama yargida da murmushi afuskarta tafurta hakan shima murmushi yayi badamuwa labelaa yanzun bari nakirashi yazo amman nayi kewarki yata gashi zaki tafii amman bamudan zantaba"'

Tashafo gefen fuskarta bakomai dady zansake zuwa saimuyi firanko?? Yace yauwa yata kikasance cikin amincin Allah

Tasaki sassanyan murmushi tace kaima haka"" inasonka babana yace nima inasonkii tace bye yace ok bye taciro wayar akunnenta takuramata ido Allah sarki babana"" Allah. Yasa kayi dacen mata Allah yasa daka wannan auren kasamu kwanciyar hankali wasu sirarun hawayene s**a sauko mata tasa gefen mayafinta tashare sake matsawa tayi saboda cinkoson mutane ga shi ankusa la asar"" batawani jimaba driver yazo bayan sungaisa tashige motar s**a k**a hanyar kano

22/08/2019

Like my page pls

09/08/2019

*MIJIN 'KWAILA* ����‍♀

sabon salo daga labarin *zahra adam ishaq*

"-chapter one-"

Ahankali yake tafiya da motar sak**akon yanda ya iske saitin bakin makarantar yaran yacika yakuma batse da dandazon yaran da'aka riga aka taso daga makaranta,ya d'anja gajeren tsoki lokaci guda yana kallon tsadadden agogon dake hannunshi ya taka burki k**ar yanda sauran masu ababen hawa y'an uwanshi s**aja nasu burkin sak**akon dakatar dasu da yellow piper yayi.
Ranshi 'kwarai yana a dagulene koda yake ba abin mamaki bane ganin fuskar tashi babu walwala kusan dukkan na tare dashi sunsan dahakan duk da yake mutum mayen barkwanci lokaci kankane yakoma k**ar wani horror abin tsoro ga kowa saboda yanda yakecin magani kullum idanunshi suna manne da farin gilashi saboda yanda ya matsama idanun nashi da kuka wanda har yazuwa yau d'innan yakasa dena kukan,
Baya zato ko tunanin zaidena kukan rasa jigon rayuwarshi dayayi a cikin watanni shidda das**a gabata.
Yazuwa wannan lokacin yazama abin tausayi ga kowa to ai dolene dukkan mai imani ya tausayama d'an sangirin saurayin maicike fal da 'kuruciya akan fuskarshi da dukkan sassa na jikinshi,
Rashi yayi babba rashin dayake ganin bazai ta'ba samun tamka ko madadin taba.ZAHRA ADAM ISHAQ cikakkiyar budurwar das**a sha'ku tun yarinta shine yaci kashinta da fitsarinta ya goyata a gadon bayanshi yamata soyayya dabai ta'ba yima wani mahalu'ki a duniya irintaba rana guda ciwon mara yayi fatali da rayuwar zahara yazuwa barzahu,
Adai dai lokacin da yarage saura kwana uku rak!
Daurin aurensu,
Yashiga rud'u mara misaltuwa dayawa yawa anzata ya haukace,amma dayake allah gafurune kuma rahimu saiya tashi kafad'unshi yakuma saka mashi dangana duk da ikirarinshi na dena kallon kowacce y'a mace da gashi tunda yarasa zahra.
Y'amma dayawa sunsha kawo kansu gareshi wasu iyayensu zasu kawo talla wasu text zasumai amma haryau baiga mai maye gurbin zahra ba,
Yashafi gefen fuskarshi daya tuna aneesa wacce tanace mashi k**ar chewing gum saboda so,
D'iyar 'kawar mummy ce,
Ya girgiza kai batare daya ankare ba.
Kamar ance dashi ya kalli gefen damarshi ya hangota cikin dandazon yara sa'anninta k**ar sauran yara akwai uniform bulu da farin hijabi jikinta sai y'ar jakar makaranta saqale a hammatarta,
Wata mummunar fad'uwar gaba ta riskeshi lokaci guda ya cire gilashin fuskarshi yasake murza idanu gabanshi na bugun goma goma,
Dai dai lokacin data tsallako gefen dayake yara sun ragu sosai,
Tana tafe tana tsokanr yaran dake gefe da ita.
Caraf idanunta s**a sar'ke cikin na ishaq wanda tuni anbasu hannu amma tsabar kallonta baimasan anbasu hannunba.
Tarin ababen hawa dasuke bayanshi s**a addabeshi da horn hakan yasakashi waigawa da sauri, lokacin wani har yayi mashi overtaken yana fad'in "amma kai wawane,idan kallon mata kazoyi toka bamu hanya mu wucewa zamuyi "
Ishaq bai tankaba yagyara parking mota zuciyarshi k**ar zata tsage saboda tashin hankali.
Ganin ita yaketa kallo yasata cewa da 'kawayenta"ummilolo kukalli d'an 'kauye yanata kallona kutsaya kuga yanda zanmashi gobe bazai sake kallonaba,ummana tace mai kallon mutane mayene."
Saita lalla'ba k**ar zata wuceshi sai dai tana zuwa saitinshi inda ya sauke glassa d'in motar ta tofa yawu, cikin sa'a kuwa ya sauka akan fuskarshi.
Sauran students y'an uwanta s**a saki baki suna kallonta duk sun kasa tafiya,
Yayinda su ummilolo s**a hau tsalke suna kyalkyala dariya.
Itama dariyar take don asukwane tabar wajen da gudu,
Tana zuwa tami'k**a su ummilolo hannu s**a tafa, kafin tacigaba dayima ishaq gwalo tanasaka hannayenta saitin kunnuwanta almar eho...ya numshe idanu yana tunano zahranshi a irin wannan lokacin tayi mak**ancin hakan gareshi, lallai batada maraba da zahra, hannu yasaka ya lakace miyon,ya sumbata zahra daban take, komai nata so yakeyi.
Bai ankareba ya hango zahra can kusa dawani matashi irin masu tallar agwaluma d'innan,
Ta mararaice fuska tace dame agwaluma "kai don Allah bani d'aya?
Me agwaluma cikin mamaki ya kalleta yace"kibada kud'i sai abaki agwaluma yammata."
Sudai su ummilolo sun 'kunshe baki sunason dariya suna tsoron bala'in zahra don sunsan akwai daru.
Ta murgud'a wa mai agwaluma baki,"nace kabani d'aya kawai."
Me agwaluma ya fusata yace"tunda ubanki yabani jari meze hana inbaki d'aya."
Tazaro idanu"la la la..kazagi ubana?
Me agwaluma yayi tsaki,
Aikafin ya ankare tuni ta duma wawa uku ta sura ta fece aguje da fad'in "pdp!!!"
Sauran yara dasuke tsaye s**ace "wawaaaa!!!"
Tuni sun duma hannaye suna dumbuzar agwaluma,
Ganin yara sun kwashe agwaluma yasaka me agwaluma binta aguje bayan ya jefar da tiren dayazama empty.
Shegen gudu gareta ko barewa ta shafa mata lafiya,
Sauran yara s**ad'au ihu "sai zahra !!sai zahra!!!!
Gaban ishaq dake kallon duk abinda yafaru yabuga da karfi.
Ya maimaita sunan ZAHRA???

��������

Address

Katsina
Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hamisha novels posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category