Shaikh Hamza Musa wagini

Shaikh Hamza Musa wagini Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Shaikh Hamza Musa wagini, Shopping & retail, Wagini, batsari, Katsina.

Yadda aka gudanar da makon hadin Kai a da'irar Wagini.A cikin bukukuwan maulud da da'irar Wagini take shiryawa a duk she...
13/09/2026

Yadda aka gudanar da makon hadin Kai a da'irar Wagini.

A cikin bukukuwan maulud da da'irar Wagini take shiryawa a duk shekara, da'irar ta fara da gabatar da makon hadin Kai a bana 1448,a unguwar Dan marke Wagini.

An samu halarta malamai daga bangarori daban- daban inda s**azo s**ayi musharaka wajan gudanar da wannan biki na Mauludin fiyayyen halitta ,an bayar da dama ga wásu malamai har sunyi magana a wajan Taron yayin da shaikh hamza musa Wagini wakilin Yan uwa almajiran sayyid Ibrahim zakzaky (H) yayi jawabin rufewa .

13/9/2026

hamza musa wagini #
maulud #

Photos 👇👇

AN DAURA AUREN MARYAM SIDI SHI'ITU MAI GUBA KATSINA.12/9/2026A jiya juma'a aka daura auren diyar sidi Shi'itu Mai Guba k...
12/09/2026

AN DAURA AUREN MARYAM SIDI SHI'ITU MAI GUBA KATSINA.

12/9/2026

A jiya juma'a aka daura auren diyar sidi Shi'itu Mai Guba katsina ,shaikh hamza musa Wagini ya samu halarta daurin auren .

Muna fatan Allah ya sa alkhairy ya bada zaman lapiya da zuria dayyiba

hamza musa wagini #
maulud Nabiy(S) #

TA'AZIYYA !Shaikh hamza musa Wagini yakai ziyarar Ta'aziyya A garin Batsari.Matar wakilin Yan uwa na garin Batsari malam...
29/08/2026

TA'AZIYYA !

Shaikh hamza musa Wagini yakai ziyarar Ta'aziyya A garin Batsari.

Matar wakilin Yan uwa na garin Batsari malam Abdullahi A.Umar Batsari ta rasu a ranar Alhamis daga gabata,sak**akon wannan rashi ne shaikh ta tawagarsa s**a Kai ziyarar Ta'aziyya ga malam Abdullahi A.Umar.

Muna fatan Allah yayi mata Rahma ya gafarta mata ,Allah ya kyautata makwancin mamatanmu Yan uwa musulmi.

Hamza musa Wagini #
16/3/1446
29/8/2026

طلب الحلال فريضة على كل مسلم والمسلماتYadda shaikh hamza musa Wagini ya ziyararci gonarsa  dake Wagini.Muna barar addu'a...
29/08/2026

طلب الحلال فريضة على كل مسلم والمسلمات
Yadda shaikh hamza musa Wagini ya ziyararci gonarsa dake Wagini.

Muna barar addu'arku Mai albarka

29/8/2026
16/3/1448

Photos 👇

*FREE KHUDBA DAGA MASALLACIN JUMA'A NA WAGINI.* Shaikh hamza musa Wagini ya gabatar da free hudba a babban masallacin ju...
28/08/2026

*FREE KHUDBA DAGA MASALLACIN JUMA'A NA WAGINI.*

Shaikh hamza musa Wagini ya gabatar da free hudba a babban masallacin juma'a na garin wagini,shaikh ya nuna yadda ake nuna soyayyar fiyayyen halitta ta hanyoyi daban daban k**ar:
a.Taruwar mutane suna zikiri don nuna farin ciki
b.Fitowa rali tare da Dinka sabbin kaya da rera yabon manzo (S) don nuna soyayya
c.Ciyar da abinci ko shayar da abinsha Dan murna da samuwar manzo (s) da sauran nuna nau'in farin ciki Wanda Bai sabawa ka'ida da shari'a ba.

Shaikh ya nuna cewa nuna farin ciki da samuwar fiyayyen halitta (S) umurni ne na Allah ,hujja daga ayar al'qur'ani

بسم الله الر حمن الر حيم
Suratu Yunus, Aya ta 58:
قُلْ بِفَضْلِ اللَّهِ وَبِرَحْمَتِهِ فَبِذَٰلِكَ فَلْيَفْرَحُوا هُوَ خَيْرٌ مِّمَّا يَجْمَعُونَ
Shaikh yacigaba da jawabinsa akan cewa lazim ne Wanda ya nuna yanason manzo (S) dole ya kwaikwayi dabi'u da halayensa k**ar Amana, gaskiya da tausayi dss.

Shaikh yayi Allah wadai da wadanda suke danganta Iyayen Annabi(s) da shiga wuta tare da Jan kunne al'umma akan taba mutuncin ma'aiki (S).

Daga karshe shaikh ya nuna cewa a wannan lokaci ya dace a samu hadinkai musamman tsakanin masoya Annabi(s) dake cikin ko wace kabila musamman Hausa Fulani,Tare dayin addu'a ga duk wadanda suke dasa hannu wajan Hana zaman lapiya a tsakanin al'umma .

16/3/1448H
28/8/2026M
hamza musa wagini #

Photos👇👇👇👇

Ta'alim a da'irar Wagini.Ayau laraba ake gudanar da ta'alim a da'irar Wagini,malam Ahmad Muhammad S/gari ne ya jagoranci...
19/08/2026

Ta'alim a da'irar Wagini.

Ayau laraba ake gudanar da ta'alim a da'irar Wagini,malam Ahmad Muhammad S/gari ne ya jagoranci ta'alim din a wannan Rana!.

19/08/2026
ya RASULALLAH #

LABBAIKA YA RASULALLAH (SAWW).An sauya tutar ashura izuwa ta maulud a dairar Wagini,inda wakilan Yan uwa almajiran sayyi...
17/08/2026

LABBAIKA YA RASULALLAH (SAWW).

An sauya tutar ashura izuwa ta maulud a dairar Wagini,inda wakilan Yan uwa almajiran sayyid Ibrahim zakzaky (H) na dairar Wagini dake karamar hukumar Batsari ta jahar katsina ,shaikh hamza musa Wagini ya jagoranci Saka tutar a farfajiyar fudiyya Islamiyya Wagini .

Ayau litinin dai wannan taro ya kasance muna fatan Allah ya karba ya maimaita mana na Badi cikin aminci da yalwar Arziki.

Photos 👇👇

16/08/2026
Yadda post-hudhba ta gudana a babban masallacin juma'a na garin wagini .Shaikh Ya fara da godia ga Allah madaukakin sark...
14/08/2026

Yadda post-hudhba ta gudana a babban masallacin juma'a na garin wagini .

Shaikh Ya fara da godia ga Allah madaukakin sarki daya sake nuna mana wannan juma'a lapiya da fatan Allah ya maimaita mana .

Shaikh ya tafi Kai tsaye wajan yadda ake nuna San manzo(Saww) da iyalansa a aikace da Kuma a Baki,ganin yadda watan Rabi'ul auwal ya k**a ,shaikh din yake cewa a cikin wannan wata na Maulud zakaga yadda al'umma suke nuna San fiyayyen halitta a aikace ,ta hanyar ciyarwa da fitowa rali suna nuna soyayyarsu da wannan Manzo namu(Saww).

Shaikh hamza musa Wagini yaja hankali sosai wajan kwatanta dabi'u da aiki irin na manzon Rahma (Saww),inda yake cewa"in kace kana San manzo to Yana da kyau aka dabi'u da halayya irin da manzo (Saww)

shaikh shaikh yake cewa ,al'umma su kwatanta gaskiya,amana,Kar'a samu mutun da Karya ,ko giba alhali Yana cewa shi masoyin Annabi ne(Saww).

hamza musa wagini #
Mauludin nabi(Saww)

14/8/2026

Lokacin Matasa Ne Ya Kamata A Gina Lahira Da Kyawawan Ayyuka Kafin Tsufa -Sheikh Abdulhameed Bello ZariaDaga Abubakar Sa...
10/05/2026

Lokacin Matasa Ne Ya Kamata A Gina Lahira Da Kyawawan Ayyuka Kafin Tsufa -Sheikh Abdulhameed Bello Zaria

Daga Abubakar Sani Batsari

A safiyar ranar Asabar, 9 ga Mayu, 2026, Dandalin Matasan Harkar Musulunci na Imam Husain (AS) Zone Katsina ya ci gaba da gudanar da taron ƙara wa juna sani karo na biyu, wanda ke gudana a garin Batsari da ke Jihar Katsina.

Yayin gabatar da maudu’i na farko mai taken “Hadafin Harka Islamiyya da Kuma Hadafin Halittar Ɗan Adam”, Sheikh Abdulhameed Bello Zaria ya bayyana cewa manufar gwagwarmayar addinin Musulunci ita ce ceto ɗan Adam daga azabar wuta zuwa aljanna.

Ya ce matasa su ne ƙashin bayan al’umma, don haka lokaci ne da ya dace su yi amfani da ƙarfinsu wajen gina lahirarsu da kyawawan ayyuka kafin tsufa.

“Lokacin matasantaka lokaci ne da ya k**ata matashi ya fahimci ni’imar da Allah SWT Ya yi masa, tare da amfani da ita wajen bautar Allah da kyautata ayyuka,” in ji Sheikh Abdulhameed.

A maudu’i na biyu mai taken “Wajibcin Neman Ilimi da Hanyoyin Samunsa”, Dr. Shu’aibu Muhammad Gashua ya jaddada muhimmancin neman ilimi a rayuwar Musulmi.

Ya ambato maganar Imam Ali (AS) da ke cewa: “Neman ilimi ya fi zama wajibi a kanku fiye da neman dukiya.”

Dr. Gashua ya ƙara da cewa idan mutum ya haɗa ilimi da aiki da shi, hakan kan kai shi ga babban matsayi har mala’iku su riƙa ambaton sunansa a sama.

Haka kuma, a maudu’i na uku mai taken “Neman Aure da Zamantakewar Iyali a Manhajin Ɗan Gwagwarmaya”, Malama Khadija Katsina ta yi bayani kan yadda tsarin aure a Musulunci ya k**ata ya kasance.

Ta ce Musulunci bai yarda a yi aure ba tare da fahimta da tattaunawa tsakanin ma’aurata ba, tare da ƙarfafa zaɓen abokin zama mai addini, k**ala da ilimi.

A maudu’i na huɗu kuwa, Sheikh Hamza Musa Wagini ya gabatar da jawabi mai taken “Kyawawan Ɗabi’u Makamin Ɗan Gwagwarmaya Zuwa Ga Nasara”.

Ya bayyana cewa akwai buƙatar matashi ya suffanta kansa da kyawawan ɗabi’u har su zama jiki da jini a rayuwarsa.

“Ya zama wajibi mutum ya gyara mu’amalarsa da Allah SWT da kuma hulɗarsa da mutane, ba tare da jin cewa ya fi wani ba,” in ji shi.

Sheikh Wagini ya kuma jaddada muhimmancin kyautatawa iyaye, yana mai cewa duk wanda ya kyautata wa iyayensa, shi ma wata rana za a kyautata masa.

Tun da farko dai, bayan buɗe taron da addu’a, mawaƙan Matasan Harkar Musulunci sun gabatar da majalisi, sannan aka gudanar da salloli da liyafar cin abinci.

An bayyana cewa ana shirya taron ne domin gina shaksiyyar matasa ‘yan gwagwarmaya tare da ƙara kusanta su da harkar Musulunci.

Address

Wagini, Batsari
Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Shaikh Hamza Musa wagini posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share