23/04/2024
JAGORA NA GARI.
Jagoranci na nufin shugabantar al'umma ko mulki ko samun madafun iko na jagorancin kowace al'umma.
HON ABUBAKAR MUHAMMAD LUGGEREWO (speaker Gombe steta) Shugaba ne da yake son a tabbatar da cewa anbi doka da order kamar yanda aka tsara ga kowane irin al'amari.
HON LUGGEREWO yakan wucewa mabiyansa gaba, su Kuma suna biye dashi bisa cikakken tsari na gaskiya, ba tare da tsoron ko wane irin abin cutarwa bah.
Tabbas mun shahara wajen yarda da irin kokarin da yake, bugu da qari, mun yarda da halayensa da kuma daukan umurni da biyayya ga abinda ake so muyi a bisa tsarin doka.
HON ABUBAKAR MUHAMMAD LUGGEREWO ya yadda da kasancewarsa bawa wajen hidimtawa al'ummarsa, ta hanyar jagorantarsu cikin lamuran da s**a shafi cigaban su, da kuma abubuwa buqatun su.
Tabbas jagoranci muhimmin aiki ne na gudanarwa wanda ke taimakawa wajen ha6aka aiki, da kuma cimma buri da muradun al'umma.
Babu shakka, HON LUGGEREWO dattijo ne dake kokarin tabbatar da gaskiyar komai kafin daukar mataki akansa, domin baya aikata abu idanuwa rufe a ma rayuwarsa.
HON ABUBAKAR MUHAMMAD LUGGEREWO (speaker Gombe steta), ya kasance mutum mai alkawari da kokarin sakawa duk wanda ya taimaka masa, mussaman a lokacin da yake neman wani matsayi, saboda shi baya bukatar mabiyansa su tura mota kuma ta tashi ta barsu da hayaki.
HON LUGGEREWO Yana matuqar kokari wajen cusawa mabiyansa akidar tsoron Allah da dogaro dashi da kuma nuna yadda da cewa duk yanda mutum yake Allah Yana tare dashi, yana jinsa, yana ganinsa, yana sane da duk abinda yake aiwatarwa.
Kuma tabbas wannan shi ake qira da bam-bancin jagoranmu da sauran jagorori a siyasa.
Naku Mohammed Bafeto