Hausa Novel Zafafa

Hausa Novel Zafafa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hausa Novel Zafafa, Book shop, Unknown, Sokoto.

TARKON MUTUWA 1Complete bookTyping Suleiman Zidane kd. Whatsapp BOOK ONEA wani zamani can baya mai tsawo da ya shude a l...
25/07/2022

TARKON MUTUWA 1
Complete book
Typing Suleiman Zidane kd.
Whatsapp
BOOK ONE

A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude a lokacin da ake yin kashin dankali wato Babba a sama, Kanana a kasa. Ma'ana mai karfi, basarake da attajirai suke cin karan su ba babbaka.
A wannan lokaci zalunci ya yawaita, sam babu adalci, doka bata aiki sai akan talaka, mara karfi da makaskanci.
A daidai wannan zamani ne akayi wata nahiya wacce ta shahara a duniya a harkokin kasuwanci, Karfin mulki da yawan al'umma. Kasar da tafi dukkannin kasashen dake nahiyar daukaka itace Bindal.
Duk wani dan kasuwa dake mu'amala acikin birnin Bindal indai yana son ya tsira da mutincinsa da kuma dukiyarsa to dole yakasan ce dole ribar da ya samu a kullum ya rabata gida uku.
Kaso daya shine naka kaso biyu kuma sai ya kaiwa sarki Shamssal.
Sarki Shamsal ya kasance gawurtaccen jarumi mashahurin mayaki wanda babu kamarsa a nahiyar gaba daya domin a tarihin jarumtakarsa ba'a taba kai shi kasa ba a filin daga kuma ba'a taba yi masa rauni ba a yaki ko a gasar jarumtaka.
Yana iya shafe sa'a goma sha biyu yana yaki ba tare da gaji ba kuma yana iya yin tafiyar kwana bakwai a kasa cikin yin gudu ba tare da ya tsaya ko don ya huta ba sai dai kawai ya daga battar ruwa yasha yana cikin gudun.
Kai idon Sarki Shamsal yayi wani abun jarumtaka sai kaga kamar ba mutum bane ba shi, aljanine komai yawan rundunar mayaka yana iya tarwatsa su ya kashe na kashewa, MASU GUDU SU GUDU don tsira da rayuwar su.
A bangaren zalin ci kuwa masu hasashe sun tabbatar da cewa babu wani Sarki a nahiyar kaf wanda yafi Sarki Shamsal domin shi 'yan uwan sama sarakai cin zalinsu yake yi bare talaka.
Idan ya kyallara ido yaga wani Sarki da kyakykyawar mata sai dai kawai ya aika masa sakon ya kawota da kansa, Idan Sarkin yaki kawo ta zai iya rasa ransa ko mulkinsa don haka yana rawar jiki zai kai ta .
Batun haraji a kan talakwa babu inda aka tsanantashi sama da birnin Bidal ko yaya talaka ya yi laifi yanzunnan sai a zaneshi ko kuma a kai shi kurkuku a yanke masa shekara biyu ko fi,
A ta kaice dai in ban da Sarki Shamsal da fadawansa da kuma ya yan baran darsa da masu yi masa biyayya babu mai kwanciyar hankali a cikin birnin BINDAL.
A can karshen birnin Bindal a bangaren kudu a kwai wani makeri wanda ake kira da suna Satyan
Makeri satyan tsoho ne tukuf domin shekarun sa sunkai dari da biyar kuma tun baifi shekara tara ba a duniya ya kware a harkar kira kuma ya shahara domin gadon sana'ar yayi yana shekara taran mahaifinsa ya rasu kuma yaci gaba da aiwatar da aikin mahaifin nasa Hatta makaman yakin gidan Sarki Shamsal a makerar Satyan ake kerasu ba a taba samun wani sabani ba tsakaninsa da gidan Sarki Shamsal bai taba ganin tsoho satyan ba haka shima tsoho satyan bai taba ganin saba
A karkashin tsoho satyan akwai yara ma'aikata kimanin su saba'in da daya kuma duk suna samun abin da suke rayuwarsu a karkashinsaAlbarkacin kayan yakin da yake kerawa masarautar ne yasa ba' tsananta masa haraji ba,
kuma tun a zamanin mahaifin Sarki Shamsal hakaabin yake wakekana.
Tshoho satyan yana matar aure guda daya wacce itama girma ya kamata domin shekarunta sun kai
saba'in.
Allah ya albarkacesu da 'ya 'ya biyu kacal a duniy,
mace da namiji macen itace babba kuma shekarun ta sun kai ashirin da biyar,
Ana kiranta da suna Sadirat.
Sadirat kyakykyawa dai dai gwargwado mai kyan siffa ta taso da farin jini sosai a wajen samari
amma saboda itace kadai ke taimakon mahaifiyarta a ayyukan gida bata son ta yi aure har sai kaninta Hatyan yayi saboda
Matarshi za ta zauna a gidan ta rinka tai makon mahaifiyarsu,
ita kuwa dauketa za ai akaita wani gida.
Tsakanin sadirat da hatyan bambancin shekaru Hudu ne wato a yanzu Hatyan yana da shekaru Ashirin da daya kacal a duniya.
Allah daya gari bambam , ko kadan Hatyan bai gaji harkar kira ba.
Tunda ya taso da kuruciyarsa babu abinda yake so sama da harkar farauta don haka kusan kullum da koyaushe yana cikin daji,
Tun safe idan ya fita farauta baya dawowa sai rana ta fadi.
Wani ikon Allah kuma sai ya zamana cewa yana da nasibi matuka a harkar domin bai taba fita farauta ya dawo ba wani abu ba sai anganshi ya kamo babbar dabba ko wani babban tsuntsu,
Tun Hatyan na da shekara tara a duniya aka gane cewa sadauki ne domin tun a sannan yake iya gumurzu da manyan dabbobin daji kuma ya kashesu da hannunsa,
Wannan baiwa da Allah ya bashine tasa shi kansa Sarkin farauta na Birnin ya jashi a jikinsa
ya kaunace shi ainun hakannema ya rinka taimaka masa da yansim kan daji dana tsafi domin samun tsari.
A kullum abin da Sarkin mafarautar ke nunawa Hatyan shine lallai ya boye jarumtakarsa kada mutanen gari su sani saboda al'adar Sarki Shamsal itace dayaji ance wani sadauki ya taso a birnin sa saiya tura a sirrance a kasheshi .
Bakomai ne ya janyo hakan ba face bokayaensa sun gaya mashi cewa duk ranar da aka sami gagarumin sadauki mai irin baiwarsa ta jarumtaka da juriyar yaki da gudu a birnin to shine zai
karbi mulkinsa.

Domin cigaba shiga nanπŸ‘‡πŸ‘‡

Tarkon Mutuwa Hausa novel

*DIJA QAYA*πŸ‡³πŸ‡¬                       *page* 3⃣4⃣                Cikin zafin nama Kabir yabi bayanta, tana daf dakaiwa jik...
16/07/2022

*DIJA QAYA*πŸ‡³πŸ‡¬



*page* 3⃣4⃣


Cikin zafin nama Kabir yabi bayanta, tana daf dakaiwa jikin gate, Daga inda yake tsaye yayi Umurni Ma Mai Gadi Da ya rufe Gate d'in kar yabarta tafita.

Agagauce Mai Gadi yacika Umurnin Ogan nasa, tana kaiwa Jikin Gate d'in Ta kifa kanta ajiki tana Bubbugawa Da Hannayenta Duka Biyu tana Kuka kamar kanta ya fashe.

Ahaka ya iskota, yatsaya abayanta Zuciyansa Kaman yafita, sam baya son tashin Hankali, Murya araunane yace "Nafisa! Cool dawn pls Kidaina irin wannan kuka, "Kabud'emin k'ofa intafi kabir".

"inazakije awannan yanayin ki nitsu Kar kiyanke Hukunci cikin Fushi manzon Allah (S. A. W) yayi hani dahaka.

"No Kabir banison jin komi kabarni inatafi gidanmu, bawani abunda zaka gayamin anriga anmin Illah" tayi maganan cikin k'araji.

"Look Nafisa zo muje Part d'ina Muyi magana inyaso sai inmaidake Gidan, ya rik'o Hanunta, sannan yayi umurni ma Driver ya maida k'awarta.

Rarrashin Duniya Mami tayima Dijah Amma fir tak'i tayi shiru, tahad'a kai da gwiwa sai k'iran sunnan Baffa takeyi.

Iya wacce tayi jugum ad'aki tana jin irin badak'alan da yau akeyi agidanne ta fito, jin abun yak'i ci yak'i cinyewa.

Kamo Hanun Dijah tayi cike da Matsanancin tausayi, don duk abinka inkaji irin kukan datakeyi sai zuciyanka ya karye.

Abakin Gado ta ajiyeta ta d'ago kanta tana kallon Fuskanta, "Kiyi Hak'uri Khadijah ki kwantar da Hankalinki da yardan Allah kece da Nasara.

"lya Baffah na, lya zanje wajan Baffahna, kitamakamin lnason Ganin Baffah da lnna ta, na hak'ura da Karatun dan Allah lya kisa amidani Gidanmu kinji? Ta fad'a cikin raunanniyan muryanta da ya Dishe.

"To kiyi shiru za'a maidake amma kidaina kukan haka kar kija ma kanki ciwo.

Dak'yar ta lallab'ata tayi shiru.

Gidan Mami dayake cikin walwala kowani dare yau sai gashi yazama kaman ba kowa aciki,

Dan tunda Dijah tayi Sallan Magriba da Isha'i ta haye Gadon lya ta k'udundune, Zazzab'i Mai Zafi ne yarufeta, ko Abinci takasa ci, Ahaka Mami tashigo ta sameta, Bak'aramin Damuwa tayi ba Lokacin data tab'a jikinta taji zafi rau, data mata Magana cikin Kuka da dashshiyan Murya take cewa "Mami Baffahna!

Iya tace "Fatima ki k'ira Kabir man yadubata". Ko zai bata Magani zazzab'in ya sauk'a.

"Rabu dashi Kawai lya yaje yayi ta Faushinsa zan k'ira adubata da Safe lnsha Allah.

"Fushi kuma?
"Eh Fushi yakeyi da ni bakiga tunda yafita bai dawoba?
A'a karkice Haka, kinsan tunda s**a fara maganan bukinnan dama bai cika dawowa da wuriba,

Kabir bazaiyi Fushi dakeba dukda anmasa abunda yaran yanzu bazasu lamuntaba.

"mhmm kawai Mami tace tafita.

A falo tasamu Kabir yana zaune akan kujera ya Dafe kansa yana Kallon T. V kallo d'aya zaka masa kagane Hankalinsa baya jikin Kallon, Jin motsin dayayine yasashi kallon Wurin, Mami yahanga tana hauwa Sama.

Jim kad'an yatashi yabi bayanta, Waya yasamu tanayi da Dr Asma'u dan haka yazauna gefe sai da ta gama, Shiru ya ziyarci d'akin.

Kabir yayi gyaran Murya yana kallonta "Mami na naga Kaman Fushi kikeyi dani.

"Nikuma Kabir?
Taya za'ayi inma laifi Sannan inyi Fushi da kai? ...

"Laifi Mami? Wlh bakimin Laifiba, kiyi Hak'uri kimin Uzuri.

"Namaka Aure Kabir Shine laifin danamaka.

"Subahanallahi.

"Mami mungama wannan maganan ai, yafad'a yana zaro ido.

"daa kenana kafin kasan wacce aka auramaka, Yanzu kam kagano cewa Hatsabibiya mara kunyace, tafad'a tana k'are masa Kallo.

"Bahakabane Mami ninafi kowa Sanin yarinyannan wlh bata da dad'i Mami, amma ban isa jayayyiaya da Umurnin kiba.

Saidai Mami ya maganan Nafisa? Bazai tab'a yiwuwa inhad'a Nafisa da wannan yarinyanba Muddin inason zaman lfy.

Kuma ba hali ace za'a fasa Auren Nafisa.

Shiru Mami tayi tana nazarinsa can ta nisa tace "Karkadamu Ka Auri Nafisanka da zaran Khadijah tagama makarantanta zan maidata ga iyayenta kaman yadda ka buuk'ata inkuma tasamu miji anan shikenan sai na aurar da ita.

Dumm!! Yaji maganan ya daki zuciyansa.

Shiru yayi cikin Mutuwan Jiki, Kalaman suna masa yawo a Kansa can ya nisa Mami badai Fushi kikayi bako?

"Ko d'aya banyi fushiba Kabir saidai kafinnan lnason Kasani duk yanda ka kai da k'inta Tana da Hak'k'i kafin wa'adinmu yacika.

Kallon Mamin yakeyi da wannan dunk'ulallen maganan nata.

"Kaci Abinci ne?
"Wlh Mami nakasa cin komi ne.

"yanzu zaka iya ci ai tunda nabarka da zab'inka, baki bud'e yad'ago zaiyi magana, tadakatar dashi da Hanu tashi kaje kaci Abincin ka ni Kwanciya zanyi.

Mik'ewa yayi cikin Mutuwan jiki, Har yakai Bakin k'ofa tace "ln kagama cin Abincin ka kawomin Maganin Zazzab'i,

Yad'an Rausayar da Kai "Zazzab'i kikeji Mami?

Kaman bazata Amsaba tace "Bani bace, Khadijah ce, inka kawo ka kaima lya zand'an watsa Ruwane.

Juyawa yayi yafita kaman Mara laka, kodaya Haye daining ba yanda baiyiba yaci Abinci Amma yakasa.

Tashi yayi kaman wanda aka tsakaleshi, ya nufi pert d'insa, Baiijimaba yadawo da magani yashiga d'akin lya,

Akan gado ya hango Dijah kalle kalle yashiga yi baiga lyaba saidai yaji Motsi abayan gida.

Ahankali yatako Har gaban gadon jin irin Numfashin datakeyi.

Ya bud'e Bargon da ta rufe Fuskansa dashi, yak'ura Ma Fuskan ldo Bacci takeyi amma fuskan yayi fayau dashi alamun akwai damuwa akansa sai sheshshek'a takeyi da Alama taci kuka har ta gode Allah, Yasa yatsunsa Biyu ak'asan Wuyanta, saikuma ya janye da sauri yasake Bargon yajuyamata baya.

Dai2 Lokacin lya tafito kallonsa takeyi har tazauna akan Sofa, "Kabir! Yanzu kadawone? Kazo dubatane?.

Yatako ya k'araso gabanta yana yamutsa Fuska "Mami ce tace inkawo kibata, yafad'a yana Mik'a mata, karb'a tayi tana bud'ewa yana mata bayani yanda zata bata.

Ya juya zai fita Har yakai Baki k'ofa yajuyo ya kalleta, "Wannan Numfashin yanzu tafara ko tuntuni? Ina nufin kafin tayi bacci tanayi ko sai datayi Baccin?

"a'a Gaskiya sai da tayi Bacci naji tanayi, inaga Ko Kukan datayine yasa haka Don tayi kuka sosai.

Ya yamutsa Fuska "ai dama ita ba abunda ta iya sai koke2, kuma tasan cewa itan ba kaman Normal Mutane bane, daga haka yafice.

Iya ta tab'e Baki tabi hanyan da yafice da Kallo tace "kaji dashi dai Gulmammen Yaro.

Washi gari da safe Dr Asma'u tazo duba Dijah kaman yanda s**ayi da Mami, Bayan binciken datamatane s**afito a falo s**a zauna ta kalli Mami inaga kaman yarinyannan matsalan zuciyane da ita,

Sai daima Abunma yazo da sauk'i ga ku da Likitan Zuciya agida Dr Kb sai yadubata,

Mami tajinjina kai "da nayi zaton ko matsalanta ya shafi Fanninkine.
Dahaka s**ayi sallama ta tafi.

Atake Mami tayi waya ma Habib tana nimansa,

Kabir yana zaune ad'kinsa duk yanda yaso da yacire duk wata damuwa da matsala aransa abun ya fasakara

Ba abunda yafi tsayamasa aransa irin furucin Mami nacewa In Khadijah tagama Makaranta zata maidata Garinsu ko ta aurar da ita shin hakan yana nufin tayi fushi dashine?

Kuma to meye matsayin Aurensa akanta?

Abunda yake tayi kenan yasak'a wancan ya kunci.

Ahaka Yaji ana niman ordern shigowa, nan yaba da ordern Habib ne yashigo yazauna Kujeran gefensa yana kallonsa "Man yadai? Tun jiya banganemakaba any problem?

Tab'e baki Kabir yayi gami da ajiyan Numfashi mai k'arfi yad'an kishingid'a acikin kujera, Habib ya d'anyi Murmushi.

"Yauwa Mami ce ta k'irani ashe Khadijah bata da lfy ne? Kabir ka bata Midicine mana.

Hararanshi Kabir yayi "a wani dalilin?

"Dalilin fanninkane kafini k'warewa a fagen.

"Eh amma ai wainda s**a nimokan sunfika sanin hakan ko sokake inyi shishigi?

"Mamice fa tagayamin,

"Eh Mamin, watak'ila tafi yarda dakaine akaina.

"Amma Kb ai kaine....

"Sh*ttt! Malam kaje kayi aikin ka kawai kar kasani aciki.

Habib yayi dariya sannan ya yagi takarda yazaro Biro a Aljihun Kb yana Rubutu d'an karkato kai Kabir yayi yana lek'awa ta wutsiyan ldo Habib d'in yake kallonsa yanagama Rubatawa ya mik'e Kabir ya ja tsaki "Amma dai bakasan mekakeyiba Midicine d'in da Mai hert Disease yakamata yasha kenan?

"Eh asanina shi yakamata Malam banson shishshigi.

"mtsss kb yakuma jan tsaki ya finciki takardan yayaga nan yashiga gayamasa Abunda zai Rubuta shikuma yana Rubutawa.

sai da Habib yanimo Maganin yakai ma Mami Sannan yadawo wajen Kb.

Alokacin har yawatsa Ruwa ya canza kaya, a k'ofan falo s**a Had'u, sannan s**a koma tare s**a shiga Mota, Har sun fara tafiya Habib yajinjina kai "Gaskiiya yarinyannan tana jin jiki, Kb yayi kaman baijiba.

Can anjima ya nisa yana kalon Habib "kasan wai yarinyannane Mami ta had'amu da ita?

Habib ya gimtse Dariyansa yace "Wata yarinyafa?

"Wannan mai rawan kan tsiyannanman.

"Wai Nafisa kake fad'a?

Azafafe yace "Khadijah dai Nafisa kuma tana da rawan kai ne?

Habib ya shek'e da dariya yace "Af zancen yazo kunnenka kenan, yaushe kasamu labari? Ya ciro wayansa ya d'auko masa vidion Auren yace "gashi kaima ka shaida wlh Kb aurenku yayi Albarka kaga jama'a karkaso ka ganni Ranan wlh kaina sai huruwa yakeyi munzama manya, Kabir da ya k'ura ma waya ldo ko k'iftawa bayayi yanajin yanda sunasa yake tayawo a bakin mai shela abun daya k'ara bashi mamaki shine yanda yaga abokansa kaca2 a wajen amma arasa murum d'aya da zai gaya masa.

Dogon tsaki yaja ya wurgo masa wayan acinyansa, Gaskiya kai ba k'aramin Munafukibane shine ko a fuska baka tab'a nunaminba, Gaskiya angama dani yandama naji anata k'iran sunana ana had'awa da nata.

Hahh shiyasa a Ranan kak'irani kakw ta min dariyan iskanci kana hausa.

*Kuyi hak'uri da wannan wlh abubuwane s**a sha kaina basonabane bana typing akan kari, sanna kuyi hak'uri da typing Errow masu k'irana awaya da masu min masdage a inbox nagode* 🀝🏻

Address

Unknown
Sokoto
80213

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Novel Zafafa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category