28/04/2026
SHIN 'YAN SANDA ZA SU IYA K**A SOJA?
KU ZO MU YAMUTSA HAZO
Amsa a takaice: Eh, za su iya.
Amsa mai tsawo: Har yanzu eh… amma cikin hankali da bin ka’ida.
Mutane da yawa suna tunanin idan mutum ya sanya kayan sojoji, to ya fi karfin doka.
Wannan kuskure ne.
Najeriya kasa ce da ake tafiyar da ita bisa doka, kuma babu wanda ya fi karfin doka.
Idan soja ya aikata laifi a cikin al’umma, ’yan sanda za su iya k**a shi.
Uniform ba kariya ba ce daga doka.
Amma ga inda abin yake da muhimmanci:
Ana sa ran ’yan sanda su yi aiki cikin kwarewa da mutunci. Da zarar an k**a soja, ya k**ata a sanar da hukumomin sojoji da s**a dace.
Me ya sa? Saboda sojoji ma suna da tsarin hukunci da ladabtarwa a cikinsu.
Don haka ba batun waye ya fi girma tsakanin soja da ’yan sanda ba ne. Batun hadin kai ne, girmama juna, da bin doka.
Kasancewa soja ba lasisin yin barna ba ne. Idan soja ya aikata laifi, doka za ta bi kansa.
’Yan sanda ba marasa iko ba ne a gaban soja.
Doka ce tafi karfi a kansu gaba daya.
Idan muka ci gaba da bautar uniform maimakon girmama doka, za mu ci gaba da kare zalunci.
Idan wani soja ya aikata laifi nan gaba kar kace, “Babu abin da zai same shi, ai soja ne,” ka yi murmushi kawai…sannan ka tuna:
Doka ba ta sa uniform, amma ita ce ke umartar masu uniform.
Babu wanda ya fi karfin doka domin doka ba ta da tausayi ko son rai.
DANSANDA ABOKIN KOWA
DANSANDA DAN ALJANNAH