23/05/2024
A yanzu haka muna cikin zamanin Web3 (web three), wato Web3 Era. Menene Web3?
_____________________________
Za mu fara duba menene Web1 da kuma Web2 kafin muje kan Web3.
1. Web1 ko (web one) wani lokaci ne da aka yi a shekarun baya, alakar mutane da internet shine su shiga su karanta abunda aka rubuta kadai, a wancan lokacin babu wani abunda zaka iya yi a online sai dai ka karanta abinda aka rubuta akan Google ko website ko blog.
~ Ana kiran wannan zamanin da (Read Only), Masana tare da masu bincike suna cewa zamanin Web1 ya fara ne daga 1990 har zuwa 2002.
A wadancan shekarun mutane babu social media irin na yanzu, babu kafofin irin Facebook, Twitter, Telegram, Instagram da sauran su, sa'annan babu harkar Crypto ko Blockchain.
~ Alakar mutane da internet shine su karanta, su kwafa (copy) daga Internet, ana kiran zamanin da Read Only or (You can only Read from the Internet).
2. Menene Web Two (Web2):
Web2 wani lokaci ne da aka yi ko ake kanyi tun daga wajejen 2002 har zuwa yau, alakar mutane da Internet shine su karanta kuma tofa albarkacin bakin su, ana kiran lokacin da (Read and Write). Wato abinda zaka iya yi da internet shine zaka iya karanta abinda aka rubuta, kaima zaka iya rubutawa a karanta.
~ Shine zamanin social media, wato social media era. A zamanin Web2 an baka dama zaka iya karantawa kuma kaima ka tofa albarkacin bakin ka.
A Web1 baka da ikon rubuta komai, sai dai ka mallaki website kaima ka rubuta naka, while a Web2 period an baka dama zaka iya rubutawa wato zaka iya comment a karkashin abunda aka rubuta.
3. Web3 Era:
Zamanin Web3 shine zamanin da ake kira da (Read, Write and Earn).
Wato zaka karanta abinda aka rubuta akan Internet, zaka rubuta naka kaima, sannan zaka samu Kudi da Internet din.
~ Kowa da kowa a yanzu ya bar Web1, babu kowa a Web1, Web2 kuma a nan ne ake da yawa, wato majority na mutanen duniya suna cikin Web2 'yan kadan ne s**a wuce zuwa Web3, wato Blockchain and Crypto Currency Era.
Idan ka lura da Web1 zaka ga cigaba ne na Internet din da ada ake amfani dashi babu website babu blogs babu Google ko wasu search 🔍 engines. Sai aka samu cigaba aka kawo websites da Google a 1998 da sauran su, karatu kawai zaka iya yi a Online a wancan lokaci, ba zaka iya rubutawa, ba zaka iya yin comment ko ka bayyana ra'ayin ka ba.
Web2 kuma cigaban Web1 ne, a Web2 zaka iya rubuta ra'ayin ka a Facebook, zaka yi comment idan wani ya rubuta, zaka yi haka a Facebook, Twitter, Telegram, Instagram da sauran su.
~ Amma wadannan kamfanonin su Facebook ko Meta duk suna karkashin wasu mutane ne 'yan tsiraru, su suke kwasan makudan kudade ba tare da kowa yasan komai ba.
Sai aka fadada fasahar Web2 zuwa Blockchain and Crypto Era, wato ko baka mallaki Facebook ba zaka iya samun Kudi, ko baka mallaki Twitter ba zaka iya samun Kudi.
~ Misali, a duk social media bana samun Kudi da kowane social sai Telegram, kudaden da suke biya a kullum, a duk 24 suna biyana ta cikin TON a Telegram revenue.
Da ace zan fadin abinda nake samu a Telegram duk 24 hours da yawa zasu ce wallahi karya ne...🤣 Saboda ba kowa yasan karfin Web3 da yadda abubuwan suke gudana akai ba.
Ba mining nake yi suke biyana ba b***e kace kaza da kaza🤣, da ace yau zan shafe shekara guda ban bude Telegram ba zasu cigaba da biyana sai dai duk ranar dana bude in cire Kudi na idan ina so.
Fatan mu shine a cigaba da karatu da bincike akan wadannan abubuwan.
Akwai wadanda a TikTok suke samun Kudi, wasu Facebook Reals, wasu Instagram da sauran su.
Hawa social media da kake yi makudan Kudi suke samu da kai, toh ana biyan wadanda s**a cike ka'idar ne da Coins ta hanyar amfani da Blockchain, abun nan da ake ta ce muku Chacha ne ko Haram.
~ Wasu suna biya ta Dollar Accounts da sauran hanyoyi, amma Blockchain din yafi sauri ne kamar kyaftawar Ido.
So, a takaice idan ance maka what is Web1, Web2 and Web3 sai kace (Read, Write and Earn).
1. Web1 - Read.
2. Web2 - Write.
3. Web3 - Earn.
Mutane da yawa suna kwance akan Kudi suna bacci basu sani ba, sunki su tsaya su fahimci abun, tunda sun dauki Crypto Haramun ne, chacha ne su ba zasu saurari komai akai ba, you see, ana maganar Web3 da Blockchain ba ana maka maganar Crypto bane.
~ Yanzu kuma sai Web4 wato Metaverse da abubuwan da suke tafe dashi.
Zamu zo mu tattauna akan sa, domin wasu sun fara tsallakawa zuwa Web4 yayin da mutane da yawa suke cikin Web2 ko 3 din basu je ba.
Allah yasa mu dace.....