15/01/2026
Ban San Haka Mijina Yake Ba Sai Bayan Daya Mutu
Malam Tonga wannan labarin da zan baka ina so ne ya zama wa'azi kuma izzina ga iyaye, masu bada aure, da kuma matan kansu da ake aura. Shekaru 8 nayi da mijin da ban san asalinsa ba, ban san Addininsa da Akidarsa ba, ban kuma san danginsa ko 'yan uwansa na gaske ba, haka zalika ban san gaskiyar sana'ar sa da wasu halayen nasa ba har sai bayan daya mutu.
A Jami'ar da nayi muka hadu dashi, shine babban Dankwangilar Jami'ar. Cikin kankanin lokaci, kasa da watanni 6 aka daura mini aure dashi.
Tabbas mutane suna yiwa Mijina ganin mai kudi, sai dai kuma basu san dukiyar daya tara ya wuce tunanin su ko sanin su. Duk inda Mai kudi yake a kasar nan za a iya kira sa shima hakan, sai dai ba kowa zai fahimci hakan ba, sai wadanda s**a sanshi da kuma makusantansa kadai.
Mutum ne daya san ya kamata, yanada tausayi da kuma son taimako, shi yasa gidan mu da Ofis din sa, mutane ne a kullum suke cike, musamman mabukata, bayarwa yake bai gajiya kuma bai yin korafi.
Kamin muyi aure tabbas ina masa ganin mai kudi, amma ba yadda nazo na tarar ba da na zama matarsa. Kayan aurena ni da kaina da 'yan rakiya mutum biyar ya hanadi muka je Sin daga nan muka dawo Dubai, daidai da cokali babu wanda na saya anan Nijeriya duk daga waje muka sayo, kuma a jirgin sama s**a zo ba a ruwa ba. Ban san abunda ake kira rashi ko babu ba tunda na aureshi, ganin daman ni ba 'yar masu kudi bace, sai dai gidan namu akwai rufin asiri ganin mahaifina tsohon ma'akacin gwamnatin tarayya ne. Don haka 'yan uwana da abokaina kowa yana cin albarkacin wannan auren da nayi ganin Mijina mutum ne wanda baida kin mutane, kannena zaka zaci shine ma 'yan uwansa saboda yadda ya jasu a jiki ya daurasu akan dukiyoyinsa.
Shekarun mu 8 da aure, mun haifi yara biyu da shi, Namiji da kuma mace, ba sai na tsaya baku labarin irin gatan da yaran suke ciki ba ganin sune kawai yaransa. Sai dai kuma, duk wannan tsawon lokacin dana dauka ina zaune da miji na kwatakwata bansan wanda na aura ba, kawai zahirinsa na sani amma ba hakikaninsa ba. Na soma tabbatar da hakan ne a ranar daya mutu.
dagabakinmasuita
Ya dawo gida bayan magriba ba kaman yadda ya saba dawowa ba sai kusa 12 dare ba, yace mini kansa ne yake ciwo yana son ya sha magani ya kwanta zuwa 8 na dare zai tashi yana da inda za shi. Kwanciyar da bai sake tashi ba kenan har yau.
Babban abokinsa na soma kira bayan naga alamun kamar baya numfashi, bai dauki dogon lokaci ba, sai gashi ya zo. Yana zuwa na ganshi tare da wani da alamun dai likita ne, yazo ya yi aune aunensa ya tabbatar da cewa bai da rai. Daga nan ne fa hankalina ya tashi na soma kuka da kururuwa har kannena da suke bangaren su da sauran hadiman gidan s**a ji s**a shigo suga abunda yake faruwa, samun labarin mutuwar Maigidan sai wajen ya barke da kuka, masu Hailala da salati suna yi, masu kuka suna yi, anan ne abokin Mijina yace zasu dauke shi su kashe can wani dakin da lokaci lokaci Mijina yake shiga yana wurudi a cikinsa. Ganin cewa dakin nacan karshen gidan ne, kuma duk da ya mini kashedi kada na bari kowa ya je wajen harni, na taba zuwa sau daya, wannan ma shine yasa na kawo masa ruwa a cikin kasko, don haka ban ce komai ba su biyu daga shi sai wannan likitan ne s**a dauke shi s**a saka a mota har bakin wannan dakin s**a shiga dashi ciki. Kuma daga wannan lokacin har yanzu rabona da sake ganin gawar kenan.
Bayan nayi koke koke na ne, sai kuma hankalina ya dawo kan halin da gawar take ciki. Ganin yadda abokin Mijina yake ta kiran mutane suna shigowa gidan suna taruwa anan harabar dakin da gawar take, duk kuma wanda zai shigo, da fararen kaya jallabiya ne a jikinsa, mutum guda na iya shedawa wato Babban Wan shi Mijina, domin dashi da wannan Aminin nasa kusan koma tare suke yi, hakan yasa duk da yana a matsayin yayansa, ya dawo tamkar abokinsa ganin shima dai babu laifi yana da kudi. Ya kaaraso har inda nake ya mini ta'aziya, bayan zai juya ya koma inda suke taruwa ne, nake ce masa tunda dare ya riga yayi nasan sai gobe za a kai shi, ina son na tura a kirawo Malamai domin su sauke Alkur'ani kamin gari ya waye lokacin da za a masa sallah a kaishi makabarta.
"Hajiya ai mijinki ba musulmi bane" ya kira sunan abokinsa yace, "bai miki bayani bane, ai kuwa ya dace yanzu yazo ya miki bayani tunda lokacin hakan yayi". Yana fadin hakan ya juya zai koma a lokacin ne na fahimci da akwai wata jar kelle a hannunsa.
Maganar ce na jita wani iri wai "mijinki ba musulmi bane" ko dai nice ban ji da kyau ba, ta yaya za a ce ba musulmi bane duba da yadda masallatan daya gida, da wanda ya bada gudunmawar ginawa bazasu lissafu ba, kodai nice banji abunda Yayansa yace bane. To ai ina ganinsa yana sallah. Ni kadai nake ta yin wannan sake saken har sai da naji sallamar abokin Mijina. "mu shiga daga ciki, muyi magana ko". Yake fadamini bayan yayi gaba zuwa wata 'yar karamar daki na ganin baki. Tuni a wannan lokacin na kosa naji abunda zai fadamini saboda yadda maganar da Yayansa yayi ta gigita ni.
Ya samu waje ya zauna, yace nima na zauna saboda magana ce zamu yi mai tsawo. "Dole ne yau mu fito mu fadamiki gaskiyar wanene mijinki, ganin yau dai babu shi, don haka babu wani sauran boye boye. Daman idan har ya riga ki mutuwa, hakkin fadamiki yana kan mu ne, musamman kuma ni babban amininsa. Tabbas mijinki ba musulmi bane, cikenken Bamaguje ne, duk wadannan abubuwan da kika ga yanayi har zuwa Umrah da aiyukan Hajji da yake zuwa duk badda bami ne su. Amma dodo yake bautawa, wancan dakin da kika gani, dakin bautar sa ce shi yasa ya hana ku zuwa wajen. Duk gidansu babu musulmi, amma dai suna da illimin addinin musulunci tunda har Hadda suna dashi, kuma Dabi'unsu da sunayensu duk na Musulmai ne, amma ba musulmai bane.
"Ba wannan bane matsalar ba, babban tashin hankalin shine dukkannin mu da kika gani muna taruwa a dakin bautan nan, gaba dayan mu 'Yan kungiyar asiri ne (secret cult)... Yana zuwa daidai nan ban san lokacin da na soma sakin salati ba, na rasa abunda ke mini dadi, kuka zan fashe dashi ko ihu zan barka. Jikina ya soma rawa, zuciya ta sai bugawa take yi da karfi, a nan ne na tuna yarana na yunkura zan tafi wajensu ina kiran sunansu sai ya riko hannuna ya jawoni da karfi ya zaunar dani inda nake zaune...
Zamu ci gaba
Shi dai wannan labarin ba kagenge bane, labari ne daya faru a rayuwar wata baiwar Allah wacce kuma ta bukaci a wallafa shi domin ankaran da mutane. Don haka zamu ci gaba daga inda muka tsaya..
(ba ita bace a wannan hoton ba)